Sashe 64
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sagir yayi sallama, suka amsa banda mami da take sababi tana faÉ—in "Wallahi dole ka É—au mataki Alhaji, kar a kassara mini É—a a cuceni"
Cikin dakiya Hajiya ta miƙe ta ce "Sagir, uban meye ya kai ka wurin raihan, ka yi yinƙurin dukansa?" Yayi shiru yana kallon Hajiyan.
Alhaji ya ce "Yi masa a hankali, ni na tura shi wurinsa, ban san kuma haka zata faru ba, zo ka yi mini bayanin meyafaru?"
Cikin fusata hajiya ta riƙo rigar Sagir ta ce "Ba magana nake yi maka ba? Zuwa ka yi kayi rashin mutunci a gaban mutane ko sagir? Idan baku yi abun da za a ce baku kyauta ba ba kwa jin daɗi ko?"
Raihan ya cire hannun Hajiya daga jikin Sagir ya ce "Duk fa baku fuskanta ba, ya zaku ɗauki zafi a kan abun da ba a gabanku aka yi ba? Ni ne mai laifi abun da na yi wa yaya Sagir yana gaba da ni ban kyauta ba, kuma da niyyar ba shi haƙuri na dawo, bai kamata ba yadda na yi treating ɗin sa, dan Allah ka yi haƙuri yaya Sagir" wani irin mugun kallo Sagir yayi masa, tare da tunanin wata shiryayyiyar ce Raihan da babarsa suka shirya, kawai ya juya zai tafi, Hajiya ta bishi a zafafe, Raihan ya riƙeta ya girgiza mata kai, kawai ta fashe da kuka zuciyarta na yi mata zafi.
"Jarrabawa ce mai buƙatar juriya Hajiya, ki daina yi masa kuka" raihan ya faɗa da sigar rarrashi.
Mami kuma sai rashin mutunci take yi, tana yaɓawa Hajiya magana, Raihan ya dafa kafaɗarta ya ja ta suka bar falon yana rarrashinta.
"Gaskiya Alhaji ka saka baki, yaranta ba za su lalace kuma ta din ga nema ta ƙwace mini ɗa ba, alhalin yaranta na barazana ga rayuwar Raihan ba.
Ummi ta yi ta kiran raihan a waya, amma sai ta ji busy, bama ta shiga gaba ɗaya, haka ta haƙura ta ajiye ta tafi kitchen dan yin sanwar dare.
Farida ta daka mata tsawa, ta ce kar ta kuskura ta shigar mata kitchen, ba ta buƙata, domin kuwa barin gidan za ta yi.
A karo na farko da ummi ta ji ko a jikinta, yau ta samu hutu.
Alhaji Tahir ya kira meeting na gaggawa na iyalansa, da manyan manajojinsa da lawyoyinsa gidansa, bayan sallar isha'i.
Suka din ga mamakin hakan, dan kuwa ba su san dalilin hakan ba, dan bai taɓa yi ba.
Raihan yana maƙale da Hajiya, dan tun ɗazu da suka bar falon, sashinta ya koma ya tare yana rarrashinta.
"Bakomai ne ya sanya na taraku a halin yanzu ba, sai dan gabatar da wani hukunci da na yanke, wanda na daÉ—e ina nazarinsa kafin yanke shi.
Daga yanzu Raihan zai riƙe office ɗina, na tsawon shekara guda, ni kuma zan koma gefe ina monitoring ɗin ayyukan sa, duk hukuncin da ya zartar kamar ni na yi ne, duk mai buƙatar wani abu, zai yi a rubuce ya kai masa, yana da damar sallama ko ɗaukar ma'aikata, kar wanda ya zo ya sameni ya sani in yi masa wani abu, wurinsa za aje. Aikinka tuƙuru shi zai tabattar da kai a kan wannan kujera mai nauyi, Allah ya tayaka riƙo Muhammad Raihan sabon MD na Tahir and Son's Limited.
Wata irin razana raihan yayi yana kallon mahaifinsu, yayin da Mami ta rangaɗa guɗa tana faɗin "Ƙaraminsu babbansu, ka ga ɗan ƙaramin sauro mai hana giwa bacci"
Hajiya da yake zaune kusa da ita ta yi murmushi ta shafa sumar Raihan ta ce "Allah ya tayaka riƙo babana, Allah ya tsare mana kai"
Raihan kuwa miƙewa yayi ya bar falon, zuciyarsa babu daɗi ko kaɗan Allah ya gani baya so, kuma ya ƙudirci a watse ya samu Alhaji.
Ayshercool
0808012143
What's app only please ðŸ™
           *CUTARWA!*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
P27
FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
Masu neman free books É—ina, da free pages duk akwai a kan watpad account É—ina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya
Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.
And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ayshercool.
PAID ADVERT!.
Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku
Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921
*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUÆE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUÆŠI GIDA*
BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARÆAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.
27
Mami har ta yinƙura za ta bi bayansa, amma Alhaji ya hanata, mami tamkar ta taka rawa, tana kallon fuskar Hajiya, ko zata ga damuwa ko ɓacin rai a fuskarta.
Amma sam bata ga hakan ba, sai ma fatan alkhairi da take ta yi wa raihan ɗin, su kansu su Salim ko a jikinsu, sai dai Salim ya ɓata fuska ya kalli Alhaji ya ce "Yanzu idan muna buƙatar wani abun sai mun je wannan yaron ƙanin bayanmu ya yarje mana, ni bani da matsala da koma me ka bashi, amma wallahi ba zan je wurinsa neman abu ba, a nemi wani abun kawai"
Sagir ya ce "Balle kuma ni, da yayi niyyar dukana, sai dai ace na daina morar komai a gidan nan, da dai ace in je in sake neman wani abu a wurinsa wallahi"
"Sagir....
"Shhhh" ita ma Alhaji ya hanata yi masa magana, duk ya ce su rabu da su.
Raihan wuri ya samu yayi zamansa, gaba É—aya ransa babu daÉ—i, saboda sam bai yi farinciki da wannan al'amarin ba.
Har kusan sha É—ayan dare, babu wanda ya san in da raihan ya yi, Alhaji kuma yana falo yana jiransa, dan ya san a daren dole zai dawo ya neme shi.
Aikuwa sai ga shi yayi sallama ya dawo, da ya tabattar kowa ya watse.
Alhaji bai É—ago ya kalli raihan ba, har ya zo gabansa ya zauna, a hankali ya ce "Alhaji"
"Ka dawo ka ce mini ba zaka yi aikin bane ko? Ba ka so na nemi wani, kaima da nake jin daÉ—inka zaka fara bujure mini"
Jiki a sanyaye raihan ya girgiza kai ya ce "Ba haka bane ba Alhaji, yayi mini nauyi da yawa, ba zan iya ba wallaahi kaima ka san na yi ƙanƙanta da wannan al'amarin, kuma nine ƙarami kar yayyena su ji babu daɗi a kan hakan"
"Raihan"
"Na'am".
"Ba lokaci ɗaya kuma kai tsaye na yi assigning ɗin ka a kan wannan matsayin ba, na yi addu'a, kuma na jarrabaka ta kowane ɓangare, kai ɗin ne dai zaka iya, yara nawa Allah yake ɗaukakawa wanda suka kai ka, da wanda basu kai ka ba ma? Wani a waje bare ka ke so na ɗaukko na danƙa masa ragamar dukiyata da kula mini da ku? Ko kuma wannan yayyen naka da ba su san ciwon kansu ba? Ka sani ko takaicin abun da na yi musun, ya sanya su shiryu? Hajiya ce ta bani wannan shawarar, kuma na ga hakan ne ya dace"
Raihan ya kalleshi da sauri, ya ce "Hajiya ce ta ce ka bani ragamar kula da harkokinka?"
Alhaji ya jinjina masa kai, raihan ya yi shiru yana tunani, ya san da mami ce sai dai ayi mutuwar kasko kowa ya rasa, da dai ta yarda ko ta bayar da irin wannan shawarar.
Maganar Alhaji ce ta dawo da shi daga tunanin da ya tafi "Babban mutum, kar ina yabonka salla ka kasa alwala mana, kar ka watsa mini ƙasa a ido, i will always be by your side, duk abun da ba ka gane ba, ko abun da ka ke buƙata i will assist you like a ghost" yayi maganar yana dariya, wanda raihan ma yayi murmushi.
"Alhaji ka É—aureni da jijiyoyin jikina, kana faÉ—ar maganar nan na ji kamar ka sakani a kurkuku".
Yayi dariya ya ce "Ba wata kurkuku, ka san babban abun da ya burgeni? Da ka yi offending ɗan uwanka, ka dawo ka bashi haƙuri, ka hana abun da ya faru yin tasiri a cikin gidan nan, da kuma tsakanin iyayenku mata".
Raihan ya jinjina kai ya ce "Ummi ce ta bani shawarar yin hakan ai, ba idea ta ba ce".
Alhaji ya sake dubansa ya ce "Wace ummi kuma?"
"Baka santa ba, ƙawata ce bari ne je na kwanta Alhaji, idan na yi bacci wataƙila kaina ya daina ciwon".
"To Allah ya bamu alkhairi, zan saka ranar yi maka walima tare da abokan hulÉ—armu da ma'aikata, da gabatar da kai a matsayin sabon MD".
"Alhaji riƙon ƙwarya fa ka ce, ko dai wayo ka yi mini?"
"Tashi ka tafi sai da safe" kamar soko raihan ya tashi ya bar É—akin ya nufi É—akinsa.
Wayarsa ce ta fara ringing, ya tsaya ya É—aga.
"Ƙaraso sashina ina son ganinka" ya sauke hannunsa shi ko son yin wata maganar baya yi.
Ya koma ya nufi sashin mami, tana falo tana jiransa, "Mami, baki yi bacci ba?"