← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 134

Sashe 33

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai lokaci É—aya kawun nata ya rage bata wannan kulawar da yake bata da farko, hakan sam bai damu ummin ba, dan gani take duk wahalar da zata sha, ba zata kai ta gidan Iya da idris ba.

Ranar lahadi suka koma ganin likita, sai dai ummi ta ji daɗin amfani da magungunan nan, dan kuwa sosai yayi mata sauƙi ba kamar da ba.

Likita ya dubata, ya rubuta mata magunguna, Allah ya sa kawu yahaya bai yi ƙwauron baki ba, ya sanar masa magungunan da take sha, likitan ya ce ta ajiye su ta gama shan na asibiti, idan suka ƙare ta cigaba da waccan.

Yayi masa godiya suka tafi gida, suna tafe yana rarrashin ummi, yana yi mata nasiha.

Sai da ummi ta yi sati biyu cif a gidan, baban su Abdul ya cewa farida zai kai ummi makarantar su Abdul, amma ta ce ba ta yadda ba, sai dai ya nemi wata mai arha ya kai ummi, dan ba zai dai-daita ta da yaranta ba.

Staff school ya saka ummi, ta nan makarantar da yake lecturing, makarantar islamiyya ma, wata daban ya saka ummi, sai dai makaranta ce mai kyau sosai ana karatu, dan akwai Æ´aÆ´an manya a makarantar.

Duk wanda ya shigo gidan nan ya ga ummi, sai farida ta ce musu ummi sabuwar ƴar aiki ta yi, su yi ta yaba ƙoƙarin ummi, yarinya ƙarama amma ba ta jin jikinta.

Ko da ummi ta fara zuwa makaranta, a nan É—in ma bata sauya zani ba, saboda ba ta tsira daga cin zarafi daga É—alibai ba, saboda launin fatarta da ta idonta.
Wahala ta ƙara ƙaruwar mata a ka, ga zuwa makaranta, ga kuma aikin gida tamkar jakarsu.

Hatta rahama idan ta dawo daga makaranta, har wankin phant da brezia haka take watsowa ummi, ƙarewar wulaƙanci har da wando mai jini, sai ta cire ta bawa ummi ta wanke mata.

Iya shege da rashin kunya kuwa a wurin su intee, ba a magana, sai ta gyara wuri su ɓata, idan suka ci abinci sai ta bi ta ɗauke musu kwanuka, sai dai kawu yahaya baya iya magana, yana ji yana gani farida da ƙanwarta suka mayar da ummi baiwa, ban da cin mutunci da wulaƙanci da muzanta halittarta. Dan har haramta mata zaman kan kujerar falo aka yi, wai kar ta shafa baƙi a jikin kujerar.

Abdul ne ma ruwansa da ita, dama shi ba wani magana ya cika yi ba sosai.

Yau ma farida ta tafi gida wai suna biki, ga tsohon ciki, amma kamar akuya saboda gantali, gashi tana cikin watanta na haihuwa.

Daga ummi sai Abdul, sai kuma kawu yahaya da yake gida.

Tana ta aikace-aikace, cikin tausayawa kawu yahaya ya ce "Sannu da aiki ummina, ki samu ki je ki kwanta ki huta".

Tayi murmushi ta ce "Kawu na kusa gamawa ai"

"Ummi kin daina kirana da Abba dai sai kawu ko?" Tayi shiru tana murmushin yaƙe.

Bayan ta koma kitchen, ya numfasa ya ce "Yaya" Abdul ya É—ago ya ce "Na'am Abba".

"Yanzu muna tare muna rayuwarmu, gwanin sha'awa kuna rayuwa tsakaninmu cikin jin daÉ—i, hakan yana yi muku daÉ—i ko?"

Yayi murmushi ya ce "Sosai makuwa Abba".

"Allah sarki, kamar haka idan Allah ya so, a kowane lokaci zai iya raba mu, muna raye ba tare da wani ya mutu ba, amma zai iya rabamu, kamar yadda ya ɗauke mahaifin ummi, ya rabata da mahaifiyarta, ya kawota zama a cikinmu. Ina kallon duk abun da mamanku take yi wa yarinyar nan, da ita da ƙannenka, ko ban ce komai ba, Allah yana kallon komai, dan Allah ko daga ɓangaren ka ne ta samu sassauci, ba dan Allah baya son ta ya ɗauki mahaifinta ba, ya kawota cikinmu ba, zaka so ayi treating ɗin ƙannenka kamar yadda ake treating ɗin ummi?".

Jiki a sanyaye Abdul ya girgiza kai.

"To dan Allah ka din ga nunawa Æ´an uwanka, ummi mutum ce, kuma Æ´a ce kamar ku, muzanta ta da bautar da ita, ba shi da wata fa'ida" ya din ga yi wa Abdul nasiha, sai duk jikinsa yayi sanyi.

Sai dare sannan suka dawo, suna dawo gidan kamar sun dawo da dauÉ—a, suka cire kaya suka zubar, suka ci abinci suka baje kwanuka.

Abdul ya tarar da ita a kitchen, tana ta wanke kwanukan da suka ci abinci, ya kalli ummi ya ce "Ki je ki kwanta, yakamata ki huta".

Ummi ta ce "Kwanukan nan zan ƙarasa wankewa"

Ya ce "Bari na tayaki"

"Maza basa wanke-wanke"

Tun da ta zo gidan nan, maganar kirki bata taɓa haɗa su ba, ba ruwansa da ita, dan haka yau tayi mamakin cewa da yayi zai taya ta aiki.

Shi dai tun da Abba yayi masa wannan nasihar É—azu, gaba É—aya sai tausayin ummi ya kama shi.

Kallonsa take yi tana mamaki, yadda yake kikkife mata kwanukan, ummi sai cewa take yi ka bar shi fa yaya Abdul.

"Uban me ka ke yi a kitchen ɗin nan?" Rahama tayi maganar tana shigowa hannunta riƙe da indomie.

"Aiki nake taya ta".

Ta watsawa ummi indomie, ta ce idan ta gama, ta dafa mata guda biyu.

Ko da wasa ummi babu alamar gazawa a fuskarta, ta dafa mata indomie, Abdul yana biye da ita, ta gama yayi zaton kwanciya ummi za ta yi, amma ta kwaso uwar guga ta hau yi, kayan su na babarsu da na rahama.

Abdul ya zuba mata ido, tana ta sauri ta kammala gugar, dan tana da assignment, tana yi yana ƙoƙarin yi mata hira, amma kasancewar ba sabawa suka yi ba, ya kasa ya saukko ya ce bari ya taya ta.
Ba iya gugar yayi ba, ummi tana nuna masa yadda zai yi, sai dai bisa tsautsayi Abdul ya ƙona rigar babarsa, ta lace babban lace ba ƙarami ba.

Hakan yayi dai-dai da fitowar rahama, ta gansu a tare Abdul da dutsen guga. Ta buÉ—e murya ta ce "Anty farida, zo ki ga bariki, aikin da ake sakata take rabawa da Æ´aÆ´an gida".

Abdul ya ce "Ni ne na ce zan tayata fa"

Farida da ƙyar ta ƙaraso falon, saboda ciwon baya da mara da take yi.

"Uban me ka ke yi a nan a wannan daren?".

Ya ce "Bakomai".

"Tashi ka wuce ka je ka kwanta" ya tashi ya nufi hanyar É—akinsa.

Idonta ya sauka a kan rigar leshinta, da sawarta uku an ƙona rigar.

Ashar ta lailayo, ta ɗago rigar ta ce "Rigar ta wa ki ka ƙona mini? Dan ubanki dan baki da mutunci ba ki da hankali?"

"Anty dan Allah ki yi haƙuri, tsautsayi ne, ban san zata ƙone ba"

"Wallahi sai na ƙona ki da iron ɗin nan, ke wallahi sai na fanshe rigata, kut lallai baki da hankali"

Miƙews ummi tayi, ta fara kuka tana bata haƙuri, amma rahama ta danƙota, ta danne ta farida ta sake jona iron ɗin ya ɗau zafi, ta nufo ummi.

(*Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ina amfani da wannan dama wurin miƙa saƙon ta'aziyyata, ga ɗaukacin marubuta, na rashin ƴar uwa marubuciya, maryam nasir marsad, dan girman Allah duk wanda ya karanta page ɗin nan, muna barar ƙulhiwallahu ƙafa uku, Ubangiji Allah ya yi mata rahama, ya kai haske kabarinta ya sanya bakin wahalarta kenan, idan ta mu ta zo ya sanya mu cika da kyau da imani Amin*)

(MASU NEMA DAGA FARKO, KU DUBA A WATPAD PLEASE 🙏)

Ayshercool
What's app only please 🙏
08081012143.
                            *CUTARWA!*

   

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

BRIGHT PENS
FREE BATCH

P15

Ihu ummi take yi, tana yi musu magiya su yi haƙuri, amma cike da mugunta da zalunci, rahama ta danne ummi a ƙasa, ta cusa mata ɗan kwali a baki, ta yadda sautin ihunta ba zai fita sosai ba, ta ɗage wa ummi riga, farida ta din ga nana mata iron ɗin  nan a cikinta da zafinsa da komai.

Wata irin miƙa ummi take, saboda azabar da ta ratsata, take ta saki fitsari, saboda azabar zafi da ya ratsa ta.

Abdul har ya je ɗakinsa ya tuna ya ƙona rigar maama, kuma ƙila ummi zata hukunta, dan haka ya juyo da sauri, ya dawo falon.

A gigice ya ƙarasa wurin, ganin bala'i da izayar da ake yi wa ummi.

"Maama dan Allah ku bari, ba a yi wa mutum azaba da wuta".

Fitsarin da ummi ta saki, ya sanya rahama cikata, ta rufeta da duka, saboda ta ɓata mata jiki da fitsari, ta fizge hijjabi da hular kan ummi, a take dogon gashin ta mai matuƙar santsi ya zubo har fuskarta.

Rahama ta ce "Kut, wannan gashi ko attach" tayi maganar tana jan gashin ummi da ƙarfin gaske, ummi jikinta ya din ga rawa, ta kasa ihun saboda azaba, ta riƙe gashinta da rahama ta cika hannu da shi.

Abdul ya fara ƙoƙarin ture rahama daga kan ummi, farida ta kai ƙafa zata daki ummi, ta zame da ruwan fitsarin da ummi tayi, ta faɗi.

Wani irin ihu ta kurma, rahama ta ɗaga ummi, ta nufeta a gigice, ummi ta samu ta lallaɓa ta tashi da gudu, ta tafi ɗakinta.

BanÉ—aki ta shiga, ta cire rigarta ta din ga zuba ruwan famfo a cikinta, tana jin tamakar wurin ci yake yi da wuta, ga wani irin azaba da kanta yake yi, har wani jiri take ji.

Kan ka ce kwabo jini ya fara zuba daga jikin faruda, jikinta ya fara kakkafewa, rahama ta ce "Abdul yi sauri ka je ka taso abbanku" Abdul ya tafi da gudu É—akin da mahaifinsa yake ta bacci, saboda a gajiye yake sosai, duk wainar da ake toyawa bai sani ba.

"Abba, Abba ka tashi maama ta faɗi ƙasa"

Da ƙyar ya buɗe ido, ya kalli Abdul ya ce "Meyafaru?"

"Maama ce ta faɗi a falo" agogo ya kalla, ɗaya saura na dare, me ta je yi falo a yanzu?". Ya saukko daga kan gadon, suka fito falon tare, falon sai ƙauri yake yi saboda iron da aka bari a jone.

Jini take zubarwa sosai cikin gushewar hankali, da sauri kawu yahaya ya ɗaukko mukullin motarsa, da ƙyar suka ɗaga farida, saboda nauyin cikin ta suka bar Abdul a gida suka tafi asibiti.
Chapter 33 · 0% Book details