← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 134

Sashe 60

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Raihan ya ce "Gidanmu dai ni ne autan maza, kuka zan tayi miki, kuma ke da Alhajinmu kin saka babban mutum kuka"

Ummi ta ce "Ai bulala zan samu, na zaneka ka yi kukan da dalili, Alhaji ba zai ce komai ba"

"Wallahi ummi ina iya ƙoƙarina, Alhaji ashe aiki yake tuƙuru ba kaɗan ba, dare nake bi in yi, bana son zaman office ɗin ne saboda kowa sai ya kawo mini abun da suke buƙata, na son zuciya, na rasa yadda zan yi musu, ni ba Alhaji bane cewa nake ba zan yi ba, kuma sai su zagaye su kai ƙarata.
Sai wahalar da ni ake yi, wallaahi ji nake kamar na lallaɓa na gudu bauchi, amma kawai mun riga mun wani saba, ba zan iya tafiya na bar ki ba, ba zan din ga cin irin abincinki ba"

Ƙuri ummi ta yi da ido tana kallonsa, wai yau ita ce a rayuwa wani zai ce yayi sabo da ita, da ba zai iya nesa saboda ita ba, babu dangin iya babu na baba, Allah sarki.

"Ki ke kallona ki bani shawara mana"

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Kamar yadda na gaya maka a baya, kar ka nuna wa Alhaji gazawarka, ka yi haƙuri ka daure, da haka zaka san zafin nema, kuma kar ka kuskura ka yi zalunci dan ka farantawa wani rai, ka yi abun da ka ke ganin ya dace, amma dan Allah ka janye maganar guduwa bauchin nan"

"Saboda me?"

Ta ce "Kawai, Alhaji ba zai ji daÉ—i ba"

"Shikenan, ranar da ki ka tashi da wuri, zaki rakani zagaya ƙananan branches ɗin mu, daga nan sai mu je sayayyar, kamar jibi in Allah ya kaimu ko gobe yayi?"

Ta ce "Eh, Allah ya kaimu, amma dan Allah a cikin kuÉ—in ka bani ko dubu É—aya ce idan ban takura maka ba, na sai kayan miya da kaina in yi wa kawu girki, yau zai dawo na saya wa mama noor chocolate, idan ya so ranar da muka je sayayyar sai in siya wa kawu wani abun, da Æ´an gidanmu ko?"

"Eh har da gori zaki yi mini, saboda kina da 15k, dan kuÉ—inki yana wurina, bari a samu POS na baki kuÉ—inki kan ki tara mini jama'a".

"Ni ba haka nake nufi ba fa, to yi haƙuri, sonake kawai na farantawa kawu"

"Albashin naki har nawa ne da zaki yi ta rabo? Daga kawu sai noor da ni zaki sayawa abu, idan aka kuma biya sai ki sayawa sauran, kuma ni duk wata sai kin saya mini abu".

Ba musu ta ce "To"

"Me zaki dafa wa Kawun ne?".

"Haryanzu ban gama tsarawa ba, amma ina ga alkubus zan yi masa, da miyar ganye yana so sosai".

"To nima zan ci".

"To shikenan, idan na gama zan kiraka a waya, amma kar ka ƙaraso gida ka kira ni a waya, sai na kawo maka".

"Meyasa ba zan ƙaraso gidan ba?"

"Amm, saboda kar a ganka ace wani abun"

Raihan ya ce "Saboda ni ciwo ne?"

Ummi ta ce "A'a ba haka bane ba"

"Salma" ya kira sunanta kai tsaye abun da bai taɓa yi ba" wani yarrr ta ji a jikinta yadda ya faɗi sunan.

Ta waro ido ta ce "Salma kuma?"

"Ba sunanki ba ne?"

"Kuma sai ka faÉ—a gatsal, ina yayan ni ka daina kirana haka, yaya ummi zaka ce"

Yayi dariya ya ce "Eh to sannu uwar son girma, ba za a faÉ—a É—in ba".

"To ba zan yi alkubus É—in da kai ba".

"KuÉ—inki kuma suna wurina ba, in sai data da kuÉ—inki"

"To ai ba damuwa zan yi ba idan ka yi hakan".

"A'a kar ki zo kina yi mini kuka".

Sai kuma ya ce  "Amma ummi kamar akwai matsala yanayin zamanki a gidanku ko?" Bata amsa masa ba ta kalleshi.

"Ba sonake na ji sirrinki ba, mun wuce wannan zuwa yanzu, yadda wasu abubuwan suke gudana, duk da ni yaro ne ina fuskanta, dan Allah duk wani abu da zan yi idan zan janyo miki matsala ki gaya mini, kar a ɓata miki rai saboda ni ba zan ji daɗi ba"
Bai jira amsarta ba, ya canza hirar har ta ware.

Suna tafe suna hira suna dariya, suka tsaya wurin masu kayan miya, ta sayi abubuwan da take buƙata ya biya, a tunaninta a cikin kuɗinta ne.

Tana zuwa gida ta tarar da kawun a gida, ummi ta ce "Kawu, na É—auka sai yamma fa zaka dawo, na yi cefane zan yi maka abincin dare"

Yayi murmushi ya ce "Mamana ta kaina, dawowa ce ta kamani da wuri".

Ummi ta risuna ta ce "Kawu an biyani salary, shi ne na yi cefanen alkubus"

"Allah dai yayi miki albarka, amma cefane nawa ne ummi, ki riƙe kuɗinki ki yi buƙatunki kar ki ce zaki din ga kashewa a gidan nan".

"Kawu ka sanya albarka" tayi maganar tana murmushi tana jin ƙwarin gwiwar yin magana kamar tana tare da raihan.

Dr. Ya ce "Allah ya yi albarka"

"Amin na gode sosai " ta miƙe ta nufi kitchen, farida kuma sai kwaɓe fuska take yi tana hararar ummi babu dalili.

Bayan sallar magariba ta gama girkin da ta yi wa dr., Ta zubawa raihan na sa a flask, ta buɗe data ta yi masa message ya zo ya karɓa, za ta bawa maigadinsu, da ya zo ya ce masa shi ne raihan, zai bashi.

"Sai ka ce wani me ma zance ne? Idan ba ke zaki fito ki bani ba, na ƙoshi".

"Haba raihan, ba lallai a barni na fita, kuma zan iya samun matsala, wai kai idan ba ka yi rikici da gangan ba ba ka jin daÉ—i?"

Ya ce "Soryy don't cry Salamatu, zan zo in karɓa in sha Allah"

"Salamatu ko?" Ya katse wayar yana dariya

Shima bai samu zuwan ba, direba ya aika, ya karɓo masa, babu ƙarya raihan yana sarawa ummi wurin iya girki, dan sosai ya saba da abincinta ya rage yawon restaurant cin abinci, dan cewa yake ƴan aikin gidansu jagwalgwalo suke yi.
Yana cin alkubus É—in ya kirata yana ta zuba mata santi yana koÉ—ata.

Da safe ummi ta ji abun da ba ta taɓa tunani ba, dr. Ya kan yi faɗa wasu lokutan, duk da yana da kawaici amma yau ya ɗau zafi da yawa.

Farida yake zazzagawa bala'i, a kan lallai inteesar ta koma É—akinta.

"Wai dan Allah dr. Meyasa ka ke haka? Ba zaka tsaya ka ƙwato wa yarinya ƴancinta ba? Ai ba haihuwa ne ba ta yi ba, ɓari take yi bayan ya hanata karatu, ga wulaƙancin danginsa kuma yanzu ace an bashi ƴa zai ƙara aure haka ake yi?"

"Shut up farida, ki daina cusa mata wannan banzar aƙidar taki, bai hanata ci da sha da muhallin zama ba, a kan useless excuse ɗinku, ba zan kira yaron nan muna musayar yawu mutuncina ya zube ba, karatu kume ku ka janyowa kanku, dan haka dole inteesar ta koma ɗakinta a yau ba sai gobe ba, ke kuma" yayi maganar yana nuna kausar da yatsa.

"Abun da ki ka aikata a makaranta kin kyauta mini kenan, kuma kin kyautawa kanki? Carryover shida a courses goma sha É—aya, uban me ki ke yi a makarantar? Duk uban kuÉ—in da na kashe? Kuma baku gaya mini ba HOD É—in su ne ya kirani ya gaya mini, haka ki ka ga ummi tayi ko Abdul? carryover shida fa, courses shida ki ka faÉ—i a sha biyu, ba ma É—aya ko biyu ba balle ace tsautsayi ne, me hakan yake nufi? In cigaba da asarar kuÉ—ina? Idan auren ki ke so kema sai ki yi mini bayani ki fidda miji"

"Kaga duk ba a kai ga wannan maganar ba, tsautsayi ne bai kuma wuce kan kowa ba, ita ummin kana da tabbacin ƙoƙarinta ne ba satar amsa"

"Ki yi mini shiru farida kan na yi miki rashin mutunci, ƴa ta tafi ƙarfin ta yi satar amsa, dan haka zaɓi biyu zan baku, ko dai in ga canji next semester ko kuma ta fitar da miji, in yi mata aure ta bar mini gida, ta daina tara mini ƙarti a ƙofar gida tun da hankalinta a kan su yake ba karatun ba".

A harzuƙe farida ta ce "Waccan guzumar yakamata ka bawa wannan zaɓin ba kausar ba? Da ta gaji da balaga ta riƙe a gida taƙi fitar da miji, ita ma sai a saka mata wannan dokar, ai an yi na Allah, an riƙeta tayi karatu, ko ta fitar da mijin aure ko a san yadda za ayi da ita, dan wallahi nima sai ta bar mini gida ba zan cigaba da zama da zabgegiyar mace a cikin gida ba, kuma kana sakawa ƴaƴana doka ba, wallahi ita ma sai ta bar gidan nan "

Ganin da ya yi idan ya yi magana komai na iya faruwa, ya sanya ya É—auki mukullin motarsa ya fice, ummi tana jin abun da yake faruwa ta dake, ta fito daga kitchen ta É—aukko takalminta tana gogewa za ta fita.

"Ke ummi! Da ke nake na san kin ji komai ai" ummi ta yi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa.

"Na gaji da zama da ke a gidana, ina buƙatar space nima, tun da komai ke ce ki ka iya, ƴaƴansa ba su iya ba, duk in da miji yake ki nemo shi, sai kin bar mini gida ko kuma wallahi ki koma ƙauye in da ki ka fito"

Kausar da take kuka ta ce "Wallahi maama ta bar mana gida, banza mummuna ko kuma koma waye a aura mata, ta rabamu da ubanmu ji yadda ya ci mini mutunci"

Inteesar ma ta fito falon tana faɗin "Ai wallahi maama ki tarka mata tsummokaranta baya nan, ta bar mana gida, tuntuni ki ke cewa sai ta bar gidan nan, idan ki ka cigaba da zama da ita wannan dai ba auruwa za ta yi ba, idan ba sadakarta za ayi ba, sadakin ma shi Abba ya biya ba, ko a mayar da ita can ƙauyen ta samu dai-dai da ita".
Chapter 60 · 0% Book details