← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 134

Sashe 98

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yadda yake ta tattalin ta, da nuna mata kulawa kawai ya ga hawaye na zubowa daga idonta, tun daga kan auren Idiris ba ta taɓa zaton zata samu miji da zai nuna mata kulawa ba, hakan ba ƙaramin tayar masa da hankali ba.

"Sweetheart na yi miki wani abu ne da ba dai-dai ba? Dan Allah ki gaya mini menene me na yi miki? Ko abum da na yi ne ya ɓata miki rai?"

Ummi ta share hawayen ta ce "Bakomai fa, wani abu na tuna ne kawai"

"Dan Allah kar ki sake tuna abun da zai saka mini ke kuka please, kar ki ɓata mana farincikin da muke ciki mana, abun da ya wuce ki bar shi a baya, yanzu sabuwar rayuwa zamu gina baby, dan Allah ki daina" yayi maganar yana share mata hawayen fuskarta, ya rungumeta suka kwanta.

Sai yanzu yake yi mata abun novel É—in da take tunani, yana ta yi mata magana mai sanyaya zuciya, wasu maganganun ma kamar ta toshe kunneta dan kunya, dan a duk rashin jin raihan, ba ta yi zaton jin wasu maganganun daga bakinsa ba.

Can gida kuwa Æ´an gagarawa na koÉ—a gidan ummi, dan sai da kausar ta je gidan, kuma sai da ta É—aukko wa babr su videon komai, ta zo ta nuna mata.
Nan ɓangaren su mariya ma haka ne, ana ta santin gidan ummi, da irin maƙudan kuɗin da mijinta ya kashe a kan aurenta.

Mariya ta ce "Yaya maryam kin gani ko? Ina da kyakywan yaƙinin ummina ba za ta tozarta ba, na yaba sosai da nutsuwar mijin nan nata"

Yaya maryam ta ce "Shiyasa kullum nake cewa ki din ga yi mata addu'a, yawan damuwar ba shi ne ba, ke dan ma baki je kin ga gidan ba, zuwa gobe in Allah ya kaimu kafin mu tafi, sai mu je ki gani"

Mariya ta yi murmushi ta ce "Yaya Maryam kenan, mai É—aki shi ya san in da yake yi masa yoyo, ba zaku fahimci halin da na shiga ba a kan raba ni da Æ´a ta"

"Eh dama ya za ayi mu gane mara kunya, Æ´ar farin ki ke wa haka" mariya ta sunkuyar da kai tana murmushi.

Kiran sallar farko, Raihan ya tashi, da ƙyar ya yaƙi shaiɗan ya saukko daga kan gadon, ya je yayi alwala ya gabatar da nafiloli, sai da aka kira sallar asuba, ya tashi ummi shi kuma ya fita masallaci.

Kafin ya dawo ta yi salla, ta koma kan gado, saboda gajiya da kuma bacci da take ji.

Jin motsinsa a kan gadon ne ya sanya ta farka ta buɗe idonta da ƙyar.

"Kin yi sallar ne?" Ta jinjina masa kai tare da cewa "Good morning" cikin kasalalliyar muryar bacci.

"Morning honey, duk gajiyar ce ne, ake yi mini shagwaɓa" murmushi ta yi tana ƙoƙarin juyawa, amma ya riƙe ta ya sumbaci goshinta, ya gyara kwanciyarsa shima a gajiyen yake, dan haka bacci duk yayi awon gaba da su.

A hankali ya yi juyi, ya nemi ummi ya rasa, kamar aljana, ya daɗe a kwance yana miƙa, sannan ya saukko ya fito, can ɗaya falon ya ganota, tana ta zazzagawa tana kallon ko ina, ta saka dogon hijjabi abun ta.

Fito yayi, hakan ya É—an razanata ta waiwaya.

"Me ki ke nema ne?"

Ta ce "Bakomai, kawai na gaji da kwanciyar ne na tashi"

Ya ƙaraso falon ya ce "Sai ki ka tashi ki kar bar ni? Ni fa yunwa ce ta taso ni ma, bari na kira hajiya a kawo mana abun karyawa kan mutane su fara zuwa"

Ta ce "Da in girka mana, kar a wahalar da su" ya girgiza kai ya ce "No, kina buƙatar hutu, kuma gidan bakomai na masarufi, ban sayo ba tukuna bari na kira ta, akwai sponge da sabulu da toothpaste a drower mudubin ɗakin da muka kwana, ki shirya kan mu fara baƙi".

Ta ce "To"

A ƙalla ta kai awa guda, sannan ta dawo falon, yana kwance a kan doguwar kujera, yana danna wayarsa, ya ɗaga kai ya kalleta cikin dogon hijjabinta, ya girgiza kai tare da yin murmushi ya ce "Wane irin wanka ne haka fiye da awa goma?"

Ta ce "awa goma tun jiya kenan fa"

"Ai kin daɗe ne, ƙaraso mu gaisa mana amaryata"

Cikin matsananciyar kunya, ta ƙarasa gaban sa, ya tashi ya zauna, tare da zaunar da ita a kusa da shi, ya ce "Kin tashi lafiya?"

"Lafiya ƙalau"

"To ya jikin naki? Are you ok now?"

Ta sunkuyar da kai, tana murza yatsun hannunta, da ya zame mata É—abi'a idan ba ta da amsar bayarwa ga tambaya.

Cikin son ƙureta ya sake cewa "To ya daren jiyan?"

Mutsu-mutsu ta hau yi, za ta tashi ta tafi, dan raihan É—in ya wuce tunanin ta, kamar an canzo wani.

Riƙeta yayi ya ce "Ba in da zaki fa, yanzu dai bari in rama dukan da ki ka yi mini jiya, poor me kin kusa karya mini ƙashi, you even bite my tongue daga kiss"

"Zan je É—aki in yi abu" tayi maganar cikin rauni.

Yana dariya ya ce "Koma menene yi a nan, amma sai na rama" wayarsa ce ta fara ringing, ya É—aga yayi sallama, daga bisani ya ce "Ok"

Ya katse wayar ya ce "Bari na karɓo mana abincin, hajiya ta aiko" ta jinjina masa kai ya tashi ya fita.

Tayi ajiyar zuciya tana bin bayansa da kallo.

Shiru ta yi ta tuna irin cin zarafin da idiris yayi mata, ta kwana a waje tsirara cikin ruwan sama, saboda kawai ya same ta da larura, ta girgiza kai abun kamar ba zai wuce ba.

Raihan ya yi sallama da ƙaton kwando, ta tashi ta karɓe shi, suka iso falon suka zauna.

Sai dai ita ta kasa sakewa ta ci abinci, sai cakala take yi, ya ci ya ƙoshi, ya hau kan kujera ya kwanta sai bacci.

Ummi ta lallaɓa ta bar masa falon.

Sai azahar sai ga su yaya maryam da mama, dan a washegari za su koma maiduguri, ummi ta ji daÉ—in zuwansu, kamar ba jiya suka rabu ba.

Suka kawo mata soyayyayiyar miya ta sha kaji, har da kayan gara, sun kai ruwa rana da dr. A kan kayan garar nan, ya ce ba addini ba ce ba, idan ma sai an yi su bari a kwana biyu shi zai yi mata da kansa, suka ce sun riga sun zo da ita, sai dai ya yi haƙuri.

A nan wasu daga dangin su raihan ma suka zo, suka tarar da su, wanda ba su samu damar zuwa ganin gida ba, ciki har da wasu daga ƙannen mamin raihan.

Kallonta suke suna zunÉ—en ummi, ganin yadda take tafiya a takure, kamar mara kuzari.

"Ji munafuka, kowa fa ya san bazawara ce, amma ji salon kinibibi da iskanci, wai a dole sai ta nuna wa mutane budurwa ce" suka yi ta surutun su, ummi ba ta ma san suna yi ba.

Da za su tafi, mariya ta kama hannun ummi, tayi ƙasa da muryarta ta ce "Mamana, kin shiga sabuwar rayuwa, duk da baki da wayo sosai lokacin da na yi rayuwar nawa auren, amma aure ba soyayya ba ce kawai, kowane aure da kalar jarrabawarsa, ni na samu soyayyar miji, ƙalubale na danginsa ne.
Ki riƙe Allah ki ji tsoron Allah, babu abun da ya gagari Allah, kar ki bari ki yi nesa da Allah, babu abun da zai yi galaba a kanki, sai abun da Allah ya ƙaddara. Ki riƙe mijinki domin Allah, banda yaji ko kan ƙara, matar da ta isa a ɗakinta take yi wa miji yaji, ayi haƙuri, ayi haƙuri da juna" sosai mariya ta yi wa ummi nasiha, sai dai a ƙarshe ne kuma ta koma shirme.

Da za su tafi ummi ta je ta kira shi, sai dai bai ji daÉ—in garar da suka kawo ba, yaya maryam ta ce masa ai su normal ne al'adar su ce.

Bayan tafiyar su ummi ta dudduba kayan da suka kawo mata, ta je kitchen ta jera wanda za ta jera, kayan miya, busasshshen kifi, man shanu da sauran su.

Kasancewar raihan ba ya ɓangaren da take, kuma duk baƙin sun tafi, ya sanya ta ɗan sake, tana ta ɗan gyara in da aka ɓata.

Tana ta gyara abun da bai yi mata ba, tana yi wa kawu addu'ar samun buÉ—i da alkhairi mara yankewa a duniya da lahira, kamar an ce ta É—aga kai, ta hango raihan a tsaye yana kallonta.

Ta miƙe tsaye ta ce "In zo ne, kana buƙatar wani abu?" Ya ɗaga mata gira.

Ta nufi in da yake tana takawa a hankali, cikin tafiyarta da yake cewa yanga ce tayi mata yawa.

Ta ƙarasa ta ce "Gani"

Ya riƙo hannunta ya ce "Dama kin tambaye ni ina buƙatar wani abun ne, mu je daga ciki to, sai na gaya miki me nake buƙata" danƙarewa ta yi a wurin taƙi yin gaba.

"Ya haka kuma? Ke fa ki ka tambaye ni"

"A'a to na janye tambayar" ta yi maganar tana son ƙwace hannunta.

Raihan ya yi dariya ya riƙe hijjabin jikinta ya ce "Ummi nan fa ba muhallin hijjabi bane yanzu, aure muka yi, dan Allah ki cire shi na din ga ganin kwalliyar ke ko zafi ba kya ji"

Ummi ta ce "To, zan din ga cirewa"

"Ai yanzu nake son ki cire" yayi maganar yana cire hijjabin daga jikinta.

Doguwar rigar material ta saka, sai ƙamshi take yi, ya cire mata ribbon ɗin kanta, gashin ya sauka a jikinta, ya gyagygyara mata zaman gashin ya ce "Masha Allah, what a beautiful creature" yayi maganar yana murmushi.

Tura baki tayi tana ƙoƙarin karɓar hijjabinta daga hannunsa.

Ya riƙo ƙugunta yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, tabbas ba dan ummi ta kasance ma'abociyar suturta jikinta ba, da babu shakka mutanen banza su din ga bin ta, saboda duk in da ake fasalta mace mai diri, Allah ya yi wa ummi dirin jiki mai kyau da ɗaukar hankali.

Suka koma falon suka zauna, sai dai ya hana ummi sakat da tsokana kala-kala, kuma ya riƙeta a jikinsa.

"Komai na ki perfect baby, da headmastern nan ya yi gardama, da na yi masa abun da ban taɓa yi ba"
Chapter 98 · 0% Book details