← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 134

Sashe 24

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yaya magaji, wai iya ta ce ni yaya Idris zai aura?" ta riƙo hannunsa ta ce "Dan Allah mu je ka bata haƙuri, dukana zai din ga yi, ya ce ya tsane ni a rayuwarsa dan Allah mu je ka bawa iya haƙuri, dan Allah kar a aura mini shi".

Hawaye take tsiyayarwa daga idonta, kamar an kunna famfo.

"Ummi ki yi haƙuri, ƙaddararki ce a haka, na yi iya yi na, sun ƙi fahimta ta, ki yi haƙuri"

Ummi ta É—ora hannu a ka ta ce "Shikenan na shiga uku, wallahi kasheni zai yi da duka, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku" tayi maganar jikinta har rawa yake yi saboda tashin hankali da kiÉ—imewa.

"Ki yi haƙuri ummi, ki cigaba da addu'a, babu abun da ya gagari Allah, idiris bai isa yayi miki abun da Allah bai yi miki ba"

Kasa magana tayi, sai kuka tana jin yadda fargaba da tsoron idiris ke ƙara shigar ta.

Muryar Hashim ta ji ya na cewa "Ki tafi gida, kar ki su yi ta nemanki, ki ja wa kan ki matsala"

Ummi ta jinjina kai, ta tafi hannunta a tana zubar da hawaye, gaba ta yi ta bar cikin gari, ta samu wani wuri tayi zamanta, ta din ga kuka, idanuwanta suka haye suka kumbura sosai da sosai.

Har azahar ta yi bata da niyyar tashi, sai da rana ta take sosai da sosai, sannan ta tashi ta tafi gida, daga nesa take hangen gidan, gabanta ya sake faÉ—uwa, tayi kwana ta tafi gidansu na'ima.

Maman na'ima ta tarar a tsakar gida tana girki, ta na yi mata magana, amma ba ta iya tankawa ba, kawai ta shige cikin É—aki ta kwanta.

"Ummi ko ba lafiya ne?"

Ummi ta girgiza mata kai, kanta na yi mata wani irin ciwo, ta hau bacci.

Ƴan biki suka din ga tambayar Iya, ba za aje gidan su amarya kamu da suaran al'adu ba?
Iya ta ce musu ba sai an je ba, gidan su amaryar malamai ne, ba sa gabatar da al'adun aure, sai É—aurin aure da tariya kawai.

Iya bata farga Ummi ba ta nan ba sai la'asar, hankalinta ya tashi aka shiga nemanta, nan da nan Iya ta kawowa ranta ko guduwa ummi ta yi, to ta gudu ta je ina?
Aka din ga nemanta, har tasha aka je, amma aka ce ba a ga ummi ba.

Hashim hankalinsa ya tashi sosai da sosai, saboda shi ya yi wa ummi ganin ƙarshe, dan sai da iya ta rutsa shi tana tuhumarsa a kan ko shi ne yayi wani abu, ya ɓoye ummi ko makamancin haka.

Ummi kuwa bayan ta tashi, tayi salla, maman na'ima ta bata abinci, ta ci kaÉ—an kanta na cigaba da sara mata.

Sai dai ƙememe ta ƙi yi wa maman su na'ima magana, balle ta gaya mata abun da yake faruwa.

Har aka yi sallar magariba tana gidan, tayi sallar magariba, sannan ta cewa maman ta tafi.

Ko da ta shiga gida, da yawan an watse, an tafi yawon nemanta, dan haka kai tsaye ta tafi É—akinta, duk an baje itace a É—akin, ta tutture su ta kwanta a kan buhunta.

Iya ta dawo afujajan, saboda tashin hankali, ta din ga tsinewa ummi, da mariya tare da aibata mariya da cewa duk baƙin halinta ne yake gudanawa a jinin Ummi.

Ummi na jiyo ta, tana jin wani abu mai ɗaci ya tsaya mata a ƙirjinta, da ta kasa haɗiyewa, ta sake ƙudindinewa tana kuka, tana wata irin ajiyar zuciya mai ban tsoro.

"Laaa, ummi, nan ki ka zo ki ka kwanta ana ta neman ki?" Matar tayi maganar tana haske ummi da fitila.

Iya ta ce "Wace ummin? A ina?"

"Gata a nan a kwance"

Iya ta ƙarasa ta leƙa, ta ga ummi ta dunƙule wuri guda.

"Shegiya matsiyaciyar yarinya, ina ki ka tafi ki ka tayar mini da hankali?"

Ummi ta tashi zaune, amma ta kasa magana, ta sunkuyar da kanta ƙasa.

"Ba magana nake yi miki ba, sai na zo na hau ruwan cikinki? Wurin wani É—an iskan ki ka je? Wurin maza ki ka tafi ko?"

Ummi ta yi shiru tana tunanin ta je wurin maza tayi me?.

"Dan ubanki tun safe, da yake ba mutunci ne da ke ba, ki ka saka ƙafa ki ka fice, ba zaki gaya mini in da ki ka tafi ba, tsinanniya ƴar matsiyata" salati wasu suka din ga yi,  suna hana Iya tsinewa Ummi.

"Ku rabu da ni, ba ku san mugun halin yarinyar nan ba, riƙonta kawai nake yi, baƙin cikinta ya kusa kasheni, ku kalli ina yi mata magana ta yi mini banza, balle in san in da ta tafi, kuna ji ina tambayarta tayi shiru".

Hawaye wani na bin wani a fuskar ummi, amma ta kasa magana, kawai iya ta rarumi itace, ta sauke mata shi a kafaɗarta, gantsarewa tayi saboda zafi da ciwo, amma ta kasa guduwa, aikuwa ta cigaba da kwaɗa mata duk in da ta samu, da ƙyar ƴan biki aka hanata.

Wata Æ´ar yayar Iya ta ce "Haba Iya, yanzu wannan Æ´ar yarinyar da baki ki goya ba a bayanki, ki ke rafkawa wannan itacen, wannan ai mugunta ce. Ni tun da na zo gidan nan, wallahi ban ga yarinyar nan tayi wani abun ashsha ba".

"Bar ni marka da hatsabibiyar yarinyar nan, baƙin cikin uwarta bai kasheni ba, na ta zai kasheni, ni na fara tunanin ko dai ba jinina ba ce, dan kaf zuriyarmu babu wannan munin kamar baƙar buranya".

Aka yi ta bawa Iya haƙuri, ummi kuwa tayi mursisi ta kwanta, ta cigaba da kuka, tana jin kamar bayanta ya karye.

Ƙaiƙayin nan ne ya cigaba ta taso mata, duk yadda ta so ta daure, kasawa tayi, ta din ga soshe-soshe, kamar za ta zaee.

Da aka yi sallar magariba, ta tafi banɗaki tayi fitsari, ba tare da wurin ya tsane ba, ta tashi ta fito da jiƙaƙƙen wando, aikuwa ƙaiƙayi ya sake tasowa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, ganin wurin da duhu, ya sanya ta kai hannu ta fara sosawa, wanda har ta shagala saboda azabar zafi da ƙaiƙayi.

"Ai dama na faÉ—a, na faÉ—a wurin maza ki ke zuwa ko ummi, wurin maza ki ka je tun safe ba kya nan" zabura ummi tayi, ta girgiza mata kai, saboda yadda Iya ta haske ta da fitila.

"Uban me ya kai hannunki gabanki, ki na  soshe-soshe a duhuwa? Na faɗa wurin maza ki ke zuwa, kina sakarci, an ƙi yadda, na ce ayi miki aure, sun ce kin yi ƙanƙanta, yanzu meye Wannan?" rasa amsar da zata bata tayi, Iya ta din ga yi mata kwarmato, a cikin mutane da duk wasu kalaman cin mutunci da muzantawa, kunya baƙin ciki duk suka cika zuciyar ummi.

Saboda azaba a zaune ta yi salla, da ta motsa sai ta ji kamar ana yayyanka naman gabanta da reza, saboda wurin duk ya kwailaye.

Ummi haka tayi kwanan baƙin ciki, ta rasa yadda za ta yi, saboda abubuwa kashi-kashi, da wasu ma ko sanin kan su ma ba ta yi ba, da yawa wasu daga maganganun Iyan ba ta san in da suka dosa ba, amma abun da ta fahimta kawai shi ne, ta san cin mutunci ne maganganun Iyan, uwa uba kamata da ta yi tana susa take yi mata kwarmato, da cewa tana zuwa wurin maza, to ta je ta yi me?.

Hashim kasa bacci yayi, tsananin tausayin ummi na cin zuciyarsa, mussaman yadda ya ji Idiris ya na alwashin cin mutuncin ummi, da kuma azabtar da ita, da duk iya ƙarfin sa.

Duk yadda ya so yi wa idiris nasiha, yayi mursisi yaƙi ganewa, ya din ga kumfar baki tare da muzantar halittar ummi.

Bayan sallar asuba, Ummi ba ta fito ba, sai da Iya ta zo ta sakata a gaba, aka ce tayi wanka, da yawa sai a lokacin suka san cewa wai Ummi ce amarya.

Da yawa akwai magana a bakin mutane, sai da ana jin tsoron Iya, babu wanda zai iya tofawa.

Sai a lokacin Iya ta bata sabon kaya ta saka, ta nemi wuri ta zauna kamar gunki, kan nan a ƙasa tana aikin kuka.

Ƴan uwan Iya suka din ga tambayar, ina dangin mariya, duk ba su zo ba?Iya ta ce "Ai auren ne ba shiri, wancan Yarinyar iyayenta sun raina ƙoƙarin idris, shiyasa aka fasa auren na ce ya auri ummi, ƙara zumunci, dan haka daga baya zasu zo".

Ƙanwar babar idiris ta ce "Amma idiris yayi jihadi, na ji kin ce yarinyar ba ta ji, kina iƙirarin tana zuwa wurin maza".

Kowa ya din ga faɗar albarkacin bakinsa, a kan auren, wasu suka din ga cewa idiris ya samu yarinya ƙarama mai nutsuwa da ƙoƙarin aiki, wasu kuma sun hau maganar Iya sun zauna, suna yi wa ummi hukunci da shi.

Da azahar aka ɗaurawa ummi aure da Idris, a kan sadaki naira dubu takwas, mutane aka din ga yi wa ummi nasiha, ana ta cewa ta yi haƙuri, aure ɗan haƙuri ne.
Abun da ummi ta kawo a ranta shi ne, ashe sun san halinsa dukanta zai din ga yi, amma aka aura mata shi.

Cikin matsanancin tashin hankali, babar na'ima ta shigo gidan, dan tabattar idan da gaske ummi aka yi wa aure, aikuwa ta samu dahir, an riga an É—aura aure ma.

Galibi maƙwabtan su, sun girgiza da jin wai ummi aka yi wa aure, ummin da guda nawa take, da kuma mutum kamar idris, da ba wanda bai san shi a fagen iya rashin mutunci ba.

Tsohuwar katifar ce dai da tabarma, katifar tsirarta, babu ko zani, gefenta duk ɓera yayi kalaci da ita, domin kuwa tsohuwar katifa ce, a gidan dillalai aka sayo ta, aka sakawa ummi a ɗaki, sai tsofaffin labulaye na Iya, labulayen nan sun sha jiki, dan ita ma kwancensu aka bata, daga baya ta samu wasu ta cire su, kitchen daga tukunya babba da ƙarama, sai ƴan tasoshi, da kofunan silba kamar bazawarar ƙauye.

Bayan sallar magariba, aka bata wasu kayan, ta saka, aka tafi kai ta. Da ƙafafuwan ta, har gidan Idris!.

Ayshercool
08081012143

                       *CUTARWA!*

*BRIGHT PENS (FREE BATCH)*
Chapter 24 · 0% Book details