← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 134

Sashe 14

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunani kawai take yi, ko ta saci jiki ba a sani ba ta je ganin ummi, amma ta tuna wulaƙancin da iya ta yi wa yayyenta, ta san muddin ta je, ba abun da zai sauya, kuma hakan tamkar watsawa mahaifinsu da yayyenta ƙasa a ido ne.

Ummi ba wanda yake kula da bata magani, sai idan magaji ya shigo sashin Iya, ya sanya ta a gaba ta sha, duk da iya ta ƙwace kuɗin da kawunsu ya bawa ummi, da kuɗinsa ya saya mata yadin uniform, ya canza mata nata da suka yayyage suka yi mata kaɗan.
Ummi ta ji daɗi sosai da sosai, ga sabuwar jakarta dan haka cike da ƙwarin gwiwa take zuwa makaranta.
Kafin kwana bakwai, tuni kan ummi ya cika da gashi, kamar ba ayi mata aski ba, kalar wanda ya fita kalar sa ne dai yake sake fitowa a kanta, ba baƙi ne wuluk ba.

Duk wannan murnar da take yi na komawa makaranta, da tarin ƙoƙarin da ummi take da shi, ya zama a banza, saboda ko tambaya aka yi a aji, ba ta iya bayar da amsa, saboda gudun cin zarafi da tsokana da ƴan uwanta ɗalibai za su yi mata, koma malaman da kansu.

Wujiga-wujiga ta dawo daga makaranta, saboda azabar yunwa, koko ne kawai a cikin ta, shima tun sha É—aya da tayi fitsari, take jin kamar an sace mata kayan ciki saboda yunwa.

Da ƙyar ta ƙarasa gida, tana zuwa iya ta ɗora mata kai niƙa, haka ta kuma kwasar rana, ta kai wa iya niƙan ta dawo, a wannan wahalen da take, wannan ya ja ya aika, wancan ya ja aika, har lokacin shiga makarantar allo yayi.

Iya ta rage mata abincin rana, bai fi loma uku ba, a loma É—aya da kaÉ—an ta cinye, ta tashi ta tafi makarantar allo.

Naima ce ta hangota tana share hawaye da hijjabinta, ta ƙarasa in da take ta ce "Ummi, ya aka yi ki ka makara? Kuma kukan me ki ke yi?".

Cikin kuka ta ce "Malam babba ne ya dake ni, na makara"

"To meyasa ki ka makara?"

"Iya ce ta aike ni"

"Shegiyar mata, mai zuciyar kafirai" Naima ta faɗa a ƙule, ummi kuma ta kalli fuskar naima tana mamakin yadda take zagin babba kamar iya.

Ta ja hannunta ajinsu, ta ɗaukko wani ɗan kwano ta bata abinci, aikuwa hannu baka hannu ƙwarya ummi take danna abincin.

Na'ima ta dubi ummi ta ce "Ya jikin amma dai kin warke ko?" Ummi ta É—aga mata kai alamar eh.

"Gashin ya fara fitowa?"

Ummi ta saka hannu É—aya ta buÉ—e mata kan, Na'ima ta rufe mata ta ce "Masha Allah, ya fara fitowa, kin wanke kayanki na makarantar boko?"

"A'a yaya magaji ya saya mini sabon uniform na makarantar boko" ta faÉ—a cike da jin daÉ—i.

Na'ima ta ce "Alhamdilillah, Allah ya saka masa da alkhairi, na bayar a É—inka miki atamfar bikina"

Ummi ta kalleta ta ce "Biki, aure kenan?"

Na'ima ta ce "Eh, aure zan yi ko in tafi da ke gidana?"

"Eh yaya Na'ima zan biki dan Allah"

Na'ima ta ciro ɗan ƙaramin tsumma a jakarta da ruwa a jarka, ta bawa ummi ta sha, sannan ta shiga goge mata hannu ta ce "Zan so ace za a bani ke na tafi da ke ummi, sai dai hakan ba zai yiwu ba, ki je aji idan an tashi ki jirani mu tafi tare, zamu je gidan mansura, an kawo mata takalma daga Kano, idan da wanda zai yi miki, sai na saya miki na biki"

Ummi ta ce"Ba zaki tafi da ni ba?"

"Ki yi haƙuri ummi, ba zai yiwu ba"

"Kema tafiya zaki yi ki bar ni? Mama ma ta tafi taƙi dawowa"

Na'ima ta yi ajiyar zuciya ta ce "Maza je ki ajinku, ga malam can ya tafi" ta miƙar da ummi tsaye, ummi ta tafi ajinsu.

Naja da take ƙawar na'ima, ta ce "Ke dai ki na son yarinyar nan naima, gashi kin saka mata ran tafiya da ita"

Na'ima da hawaye ya taru a idonta ta ce "Wallahi naja ina tausayin ummi sosai, wallahi da za a bani ita zan ɗauke ta, kakarta matsiyaciyar tsohuwa ce, ai babarta uwar ɗakina ce, mun yi mutunci sosai, baban ummi ya rasu, ta koma garinsu, Kakarta ta ƙwacw ta take azabtar da ita, ko a lahira na ganni gani g matar nan na san ban yi kyakkyawan ƙarshe ba" Duk da a ƙufule Na'ima tayi maganar, bai hana naja dariya ba, saboda maganar ta ta ƙarshe ta bata dariya.

Bayan tashi daga makaranta, tare suka tafi da ummi, hannunta cikin nata suna tafe tana yi wa ummi hira, tana bugun cikinta, dan jin zaman da take yi, sai dai abun babu daÉ—i mussman da ta gaya mata abun da su auwwalu suka yi mata, da aka yi mata aski.
Na'ima ta ce "Bakomai Allah ya isanki wallahi, duk wanda yayi nagari kansa,. Ki yi ta haƙuri kin ji ummi, duk tsanani duk yunwar da ki ke ji, kar ki bari wani a mazan gidan ku, manya ko yara, su kai ki wani wuri, su saka hannu a jikinki, kin ji ko?" Maimakon ummi ta amsa sai ta ɗaga kai tana kallon na'ima.

Cikin sauri na'ima ta tsaya ta ce "Suna yi miki wasan banza ko?"

Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a"

"Ki gaya mini gaskiya, suna taɓa ki ko?"

Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a"

"Duk wanda ya saka hannu a cikin jikinki, kar ki yadda kar ki tsaya, ki yi masa ihu ki gudu kin ji ko" ta jinjina mata kai alamar eh.

"Ko bayan na tafi, idan kina jin yunwa, ki je gidanmu wurin babarmu ta baki abinci"

Da haka suka ƙarasa gidan mai takalmi, aka yi sa'a aka samu dai-dai ƙafar ummi.

Na'ima ta ce "Zan ajiye a wurina, ranar bikina in yi miki kwalliya ko?"

Ummi ta ɗaga kai tana murmushi, daga nan suka ƙarasa gida.

Ummi ta shiga gida hannunta riƙe da wani kara tana wasa da shi "Ke!" Idris ya kwaɗa mata kira a wulaƙance.

Ta juyo tana kallon sa.

"Zo ki sayo mini sukari a kanti" yayi maganar yana watso mata kuÉ—i.

Ta durƙusa ta ɗauka, ta je ta sayo masa, sai dai ta din ga tuna gargaɗin Na'ima na hanata zuwa ɗakin su idris.

Ta nemi wuri ta zauna a ƙofar shiga wurin, ya gaji da jiranta ya fito.

"Dan ubanki ina aiken da na yi miki?"

Da sauri ta miƙe tana nuna masa sukarin.

"Ba zaki shigo ki kawo mini ba saboda baki da mutunci, sai ki nemi wuri ki zauna?"

Tayi shiru tana kallon sa, "Ba zaki kawo mini ba" ya sake yi mata maganar cikin tsawa.

Ta ƙarasa in da yake cikin jin tsoro, sai dai ya ya haɗa da hannunta, ya ja ta cikin ɗakin.

Kuka ta fara yi masa iya ƙarfin ta, yau ya samu damar da rabonsa da ita an daɗe, amma ta nuna masa tayi wayo yanzu, dan haka ta din ga yi masa kuka da ƙarfi, kamar yadda Na'ima ta gama gaya mata ɗazu.

Wawan marin da ya kifa mata ne, ya tafi da ji da ganinta na wani É—an lokaci, ta dafe kuncinta jikinta na wata irin tsuma, tana karkarwa.

Wata sharɓeɓiyar wuƙa ya nuna mata ya ce "Ki ka cigaba da yi mini kuka, sai na yanka wuyanki" kallonsa take yi, kallo mai cike da tsoro da tsana, ya ajiye wuƙar tare da sanya hannayensa cikin rigarta, rigar da bakomai a ciki sai teɓa dan wannan dai ba nono bane.

Ba ta karaya ba, ta fara kokowar cire hannayensa daga jikinta, tana kuka mai cin rai, iya ƙarfin ta.

Bankaɗo ƙofar ɗakin aka yi, hakan ya razana shi, dan bai yi zaton zuwan wani a dai-dai wannan lokacin ba.

"Idris meye haka?" Hashim yayi maganar yana kallon sa.

"Kamar yaya meye haka, abun da ka gani" a fusace ya ƙarasa ya hankaɗe idiris, ya janye ummi, ya kalli idiris ya ce "Wani irin banza ne kai, ba zaka girma ba a rayuwarka, da me yarinyar nan za ta ji ne?"

Wani uban tsaki idiris yayi, ya ce "Ka daina shiga sabgata ba ruwanka da ni".

"an shiga sabgar taka, wallahi idan baka rabu da yarinyar nan ba, sai na É—auki mummunan mataki a kan ka"

"To ka É—auka mana kar ka fasa" ya sake jan tsaki ya fice.

Cikin ƙunar ran yadda ƙaninsa ya raina shi, duk saboda iya na goya masa baya, ya kalli ummi ya share mata hawaye, ya fito da ita daga ɗakin, shaidar yastun idiris kwance a kan baƙar fuskarta, da har idonta yayi taruwar jini.

Ya zubawa ummi ido, da haryanzu jikinta yake tsuma, ga wata irin nannauyar ajiyar zuciya da take yi, har a lokacin a tsaorace take, kuma hawayenta ya ƙi tsayawa.

"Ummi" ya kira sunanta, sai dai bata amsa ba, ta sake fashewa da kuka.

Wani irin tausayinta ya ratsa zuciyarsa, ya din ga share mata hawayen, ya riƙe hannunta suka nufi sashin iya, tana ta dakan fura tana waƙe-waƙe.

Tana ganinsu tare ta hau bala'in tun É—azu take neman ummi, zata aiketa amma daga zuwa makaranta ta zauna.

Magaji ya ce "Iya"

"Ya aka yi"

"Dan Allah idan ba za a iya riƙon yarinyar nan ba, a mayar wa da uwarta ita, idiris fa na kama yana neman haike mata a ɗakinmu, wace irin rayuwa ce wannan, kalli yadda ya mare ta, haba dan Allah"

Iya ta dafe ƙirji ta ce "Shi idiris ɗin? Ita uban me ya kaita in da yake, me ya kaita ɗakin ku, ai ita ta kai kanta, amma shima zai zo ya same ni, da ni yake zancen. Kai kuma sai ka ce ba ɗan uwanka ba, ka ke ɗaga murya tona masa asiri zaka yi?"

"Iya to zuba masa ido za ayi, idan abun da ba a so ya faru fa?"

"Ba abun da zai faru sai alkhairi, jeka zai zo ya same ni, ke kuma canza kayan ki zo ki kai dusar nan gidan lami, ta bawa dabbobina"

Hashim ya ce "Ni bani dusar na kai, kalli yadda take a razane"
Chapter 14 · 0% Book details