Sashe 21
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana tafe tana yada hannu, saboda gajiya ga rana, yunwa da ƙishirwa duk sun addabeta, mutumin da ta hango a ƙofar gidan su ne tare da kawu Ilyasu, ya sanya ta tafiya a hankali, ta ƙarasa ƙofar gidan.
Shi ma ƙuri yayi da ido, yana kallonta, ta ƙarasa ta durƙusa ta ce masa "Ina wuni?"
Jiki a sanyaye ya amsa ya ce "Ummi kin gane ni?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
"To waye ni?"
Maimakon ta bashi amsa sai ta ce "Ina mama?"
"Haryanzu baki manta da ita ba?"
Da sauri Ummi ta sake kallonsa ta ce "Da ita ku ka zo?"
"A'a, na zo dai neman alfarmar na tafi da ke na kai ki wurinta, amma sun ƙi yarda"
Kawu Ilyasu ya wani haÉ—a rai, cikin haushi kamar tsohon kare ya ce "Ke! Tashi ki wuce ki shiga cikin gida"
Ƙafafuwanta suka yi mata sanyi, ta ji tamkar ba zasu iya ɗaukarta ba"
"Ba zaki tashi ba?" Ya sake yi mata tsawa. Cikin rawar jiki ta tashi, yaya magaji ya kamo hannunta ya danƙa mata kuɗi, yana riƙe da hannunta ya kalli Kawu Ilyasu ya ce "Da ku da mahaifiyarku, ku shirya amsar da zaku bawa Allah, kalli wai wannan ƴar ɗan uwanku ce dan abun kunya, kalli kayan makarantar da suke jikinta, kalli ƙafafuwanta. Kun ce idan na tafi da ita babu ku babu ita, ku ba dangin mahaifinta bane ba, duk in da aka je aka dawo, da dangin uba ake ado, kuma ba zan cigaba da jayayya da ku ba, muna raba abun faɗa, Allah zai zama gatan marainiya"
"Ummi ki kula da kanki kin ji ko? Ki yi ta yi wa mamanki addu'a, hankalinta yana kan ki, Allah ya yi miki albarka".
"Wai ba zan sake ganinta ba?"
"Zaki sake in sha Allah, Allah ya shiga lamarin ki"
Rirriƙe hannunsa tayi tana kuka, tana yi masa magiyar ya tafi da ita.
Da ƙarfin tsiya kawu Ilyasu, ya fizgi hannunta, ya angizata zuwa cikin gida.
Tana kuka suka ƙarasa shashinsu, sai dai da munanan kalaman iya ta fara cin karo, tana ɗaga murya tana cewa "Ni dai azo a nema mini magani, a rabani da wannan dangin maitar da jaraba, sun kashe mini ɗa suna bibiyata saboda ƴar su na hannuna, ba dole mariya ta haukace ba, ai kaɗan ta gani, hauka bata ma fara shi ba, tun shekarun baya da na karɓi ƴar ba ta yi haukan ba sai yanzu, Allah ya ƙara tuburata, yadda ta rabani da ɗa na babu ita babu sukunin duniya!!".
Bright pens fans group, da sauran masoya ummin Iya, ina ganin sharhinku, ina godiya sosai da sosai ðŸ™ðŸ™ðŸ™
Ayshercool
08081012143
            *CUTARWA!*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
BRIGHT PENS
(FREE BATCH)
P9
Gaba ɗaya Ummi ta ji ƙafafuwan ta sun yi mata sanyi, har suna neman gaza ɗaukarta, tayi ta maza ta ja jikinta ta shiga, kai tsaye ɗakin da take ta wuce, ba ta tsaya a in da Iya ke banbaminta ba.
Wucewar ta bai sanya Iya jan baki tayi shiru ba, sai ma haƙiƙancewa da tayi, tana cigaba da masifa "Ni dai na gaji da wannan maitar da masifar, dole in miƙe in nemi tsari da bala'i da tashin hankalin wannan mutanen su daina yi mini sintiri da bibiyata, ba dole mariya ta haukace ba, hakkin ɗa na ba zai taɓa barinta ba, daga haka ma in Allah ya yarda sai ta fara yawo tsirara, ni bai dame ni ba, hakkina da na ɗa na ba zai bar ta ji daɗin rayuwa ba, hauka ma yanzu ta fara ba ta ga komai ba tukuna".
Ummi ta ja ta tsaya a cikin ɗakin, tana ƙare masa kallo, kasancewar haddar yaro ƙarami, ba abu ne da yake gogewa cikin sauƙi ba, ya sanya take ummi ta shiga hasaso abubuwa da dama da suka faru a ɗakin nan.
Yanayin jeren ɗakin, ƙamshin turaren wuta ɗan tsinke da mamanta ke yawan kunnawa, yadda take zama a kan cinyar mahaifinta ta ci abinci, yadda daren da aka yi mata fyaɗe ya kasance, ko ba komai ummi ke iya tunawa ba, ba ta manta yadda mamanta take iya ƙoƙarin ta wurin yi wa Iya biyayya, ta kalli yadda ɗakin ya zame mata a yanzu baƙi ƙirin, tamkar dajin da wuta ta cinye bishiyun da suke ƙawata shi.
Durƙusawa tayi ta fashe da kuka tana sheshsheƙar kuka, tana jin Iya na cigaba da ci wa mahaifiyarta mutunci, tare da yi mata fatan masifa kala-kala da aibantata da sharruka.
Ummi ba ta samu fitowa daga É—akin nan ba, sai daf da la'asar, dan ma Allah ya taimake ta zuwa makarantar allo da take yi, ana horasu a kan kula da ibada, wanda dama ta samu wannan horon daga mahaifiyarta, amma dan ta Iya, ko za ta shekara ba ta yi salla ba, babu ruwanta da ita.
Ta yo alwala ta dawo É—akin tayi azahar da la'sar, ko tunanin zuwa makarantar allon ba ta yi.
Tana jiyo yadda duk wanda ya shigo sai Iya ta gaya masa ai Mariya ta haukace, tana can an sakata a turu, hakkin rai yana bibiyar ta, ta fara bi bola-bola tana tsince-tsince.
Ummi ta sha kuka, sai da idanunta suka kumbura, dan duk kukan da za ta yi idonta baya ja, sai dai ya É—an sirka, kuma su kumbura.
Ta kalli kuɗin da yaya ɗanlami ya bata, ta watsar da su a tsakar ɗakin, ta ƙanƙame jikinta, tana sauke numfashi hawaye na tsiyaya daga idonta.
Ba tsammani ta ga magaji a kanta.
"Ummi" ya kira sunanta a hankali.
Ta É—aga kai tana kallonsa. "Kukan me ki ke yi?"
"Yaya magaji"
"Na'am ummi".
"Wai mamana ta haukace?" Tayi maganar wasu hawayen na gangarowa saman kumatunta.
"Subhanallah waye ya gaya miki haka?"
"Wanda ya tafi da ita ne yazo, shi ya bani wannan kuÉ—in"
Hashim ya ce "Kar ki sake cewa ta haukace, bata da lafiya dai, tana ganin likitan ƙwaƙwalwa aka ce"
"Likitan ƙwaƙwalwa? An ce sai mutum ya haukace fa ake kai shi wurin likitan ƙwaƙwalwa"
"Ba haka bane ba"
"To meyasa Iya take cewa mama ce ta kashe baba, ba hatsari yayi ba?".
"Ki daina damuwa da maganar Iya, ki kwantar da hankalinki, ki ta yi wa mamanki addu'a Allah ya bata lafiya"
"Dan Allah yaya magaji ka kai ni wurinta, ina son in ganta dan Allah" tayi maganar tana haÉ—e hannayenta alamar magiya, tana kuka.
Cikin matsanancin tausayinta ya ce "Ummi Maiduguri ba nan ba ce akwai nisa, kuma ban san a ina mahaifiyarki take a Maiduguri ba, lokacin da aka aureta muna yara, kuma kin ga ba taɓa zuwa muka yi ba. Amma ki yi haƙuri ki daina kuka, zan bincika miki in sha Allah"
"Gidan uwarka zaka bincika mata, munafukin Allah ta'ala, to kar ka fasa, wallahi magaji idan ba ka kiyaye ni ba, sai na hau kujerar tsiya na ci ubanka la'ada waje a kanta, kar ka fasa kai ta inda uwarta take, zaka ga cin mutuncin da zan yi maka, dai-dai nake da kai.
Kema tsohuwar munafuka, halin uwarki haka halinki yake, duk wannan ƙoƙarin da nake yi a kanki ba kya gani, da ki ke hannunmu mutuwa ki ka yi? Kowa yazo sai ki ɓare baki, ke a kai ki wurinta, tun da namanki nake gutsura in ci, to ki cigaba kar ki fasa, amma ki sani nayi alwashin yadda mariya ta rabani da ɗa na, ke da ita har abada, sai ta ɗanɗani abun da ta ƙunsa mini, wannan kuɗin na meye?" Tayi maganar tana nuna kuɗin da ummi ta watsar a wurin.
Hashim ya ce "Yayan babarta ne ya bata"
"Tattaro mini su ki miƙo mini" ummi ta tarkata kuɗin ta miƙa mata.
Ta karɓe ta kalli Hashim ta ce "Zaka tashi ka fita ko sai na ɓata maka rai, kuma daga yau na yi maka tsakani da ita, tun da kai ne ka ke zigata, shashashai kawai"
Hashim ya tashi zuciyarsa na yi masa zafi, muddin ya buÉ—e bakinsa, zai iya É—urawa Iya ashar, dan haka yayi shiru ya bar É—akin.
"Tashi ki fice ki auni dawa ki surfa mini, tun da baki je makarantar allon ba"
Haka Ummi ta ja jiki ta fito, ta fara ƙoƙarin aikin da Iya ta saka ta, ƙasan zuciyarta tana fatan, ina ma Maiduguri babu nisa da guduwa za ta yi, ta tafi wurin mamanta.
Kayan da yaya ɗanlami ya kawowa Ummi kuwa, Iya ta tsince wanda zata tsince ta ce a fita da sauran, ba ta ƙaunar duk wani abu da ya shafi Mariya.
Duk salla sai ummi ta yi addu'ar Allah ya jiƙan babanta, ya bawa mamanta lafiya, ya sa ta dawo ta ɗauke ta.
Tun wannan tafiya da yaya ɗanlami yayi, wani daga danginsu, bai sake waiwayo in da Ummi take ba, suka mayar da hankalinsu a kan lafiyar ƴar uwar su. Dan abun na mariya gaba ya din ga yi, babu sauƙi ko sassauci, yanzu tana zaune lafiya idan aka jima, sai ta hau kuka tana burgima tare da surutai, irin na masu taɓin hankali.
Ummi kuma ta cigaba da karɓar gashi a gidansu, tsangwama da kyara a cikin yara a makaranta ko kuma a gida.
Iya ta sanya ido sosai a kan magaji, É—an taimakon da yake yi wa ummi, ta tasaya tsyin daka ta hana shi.
BAYAN SHEKARU BIYU!.
Sauri-sauri ta kammala tulin wanke-wanken da ke tsakar gidan, ta warewa kowane sashi kwanukansu ta kai musu.
Duk in da ta faki ido ta tsaya, sai ta yi soshe-soshe, dan itakaÉ—ai ta san me take ji.
Guntun omon da ya ragu, da shi ta wanke kayan makarantar bokonta, duk hantsar wandon ta fatattake, sun koɗe sun jeme, ƙafar wandon duk ta ɗage ta tattare, gwiwar duk a farfashe.
Kasancewar lokacin rani ne, rijiyoyi duk sun ƙafe, ta ɗau bokiti ta samo ruwan wanka, ta ɗauki ledar omon da babu komai a ciki, ta faɗa banɗaki wanka, da sosonta na buhu.
Ta daɗe a tsaye tana fargabar ta ina zata fara? Tun safe a makarantar boko take jin fitsari, ta riƙe shi bata yi ba, saboda azabar da take sha.