← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 134

Sashe 23

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To na yanke hukunci, ya auri ummi dan mutuncinmu ba zai zube ba, a sakamu a bakin duniya da wannan iskancin da yayi ba kamar É—an taure"

Ayshercool
08081012143.
                      *CUTARWA*

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

*BRIGHT PENS (FREE BATCH)*

Mafaka gidan ƙamshi, na da kyakywan albishir ga amare uwar gida, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

P10

Saminu ya numfasa ya ce "To shikenan, Allah ya sanya alkhairi"

Iya ta ce "Yauwwa ka turo mini shi, ko kuma ya jira ni a É—akinsu, zan same shi"

"To shikenan, bari na je na nemo shi"

Hashim kuwa dariya yake yi wa ummi, yana cewa ta tafi a hankali, saboda yadda ta kwasa da gudu cikin tsoro.

Da Iya tayi karo, iya ta kalleta ta ce "Daga ina ki ke?"

A tsorace ta ce "Dan Allah kiyi haƙuri, huwaila ce ba ta yi mini lallen da wuri ba"

"Yenyenyen da an yi magana, dan Allah ki yi haƙuri, ki wuce ki nemi wuri ki zauna kar ki sake fita". Ummi ta ce "to" dan ba ta yi zaton Iya ba zata yi mata tijara ba.

Iya duk ta bi ƴaƴanta da ta haifa da na riƙonta, ta sanar musu da halin da ake ciki.

Ilyas ya ce "Amma Iya naga yarinya ce ƙarama sosai, girman jiki ne kawai ba zata iya jure ɗawainiyar aure ba"

"Yarinya kuma? Ni ma shekarata sha uku aka yi mini aure, uwarta ba sha huɗu aka auro ta ba? Da ta shiga bulunbuƙui za ta yi, yaran yanzu da sun san komai, to idan ba haka ba ya zamu yi?"

Sagir ya ce "To ai Iya ba a shirya ba, da wani kayan É—akin za ta tare?"

"Wani shirin za ayi? A sayo mata katifa a gidan dillalai, tsohuwa ba sabuwa ba, mai biyar mai goma ku yi karo-karo, ku  haɗa a saya mata buta, murhu tukunya da ƴar tabarma, ina da tsofaffin labulaye, da abun da ba a rasa ba, a saka mata kowa da haka yake farawa ai, rufin asirin ɗan uwanta ai na ta ne"

Gaba ɗaya suka amince a kan haka, baiwar Allah ummi sam ba ta san wainar da ake toyawa ba, tamkar ba mace mai ƙananan shekaru ba, ita take ta ɗawainiyar aike da girkin abincin gidan bikin, ko nauyin jikinta ba ta ji, saboda tsabar sabo da wahala, ba ta san zama wuri ɗaya bata aikin komai ba.

Idiris kuwa tun da aka gaya masa, hukuncin da Iya ta yanke, wanda da kanta ta gaya masa, ya kada baki ya ce "Allah ya kiyaye, uban ne zan ci da wannan baƙar yarinyar mummuna ragowa, ni wallahi bana son ta".

Mahaifinsa ya ce "Rufe mini baki, ko na mangare ka, shashasha mara hankali, kai ka isa ka yi jayayya da maganar Iya? Ba kai ka janyo koma menene ba, aure ne babu fashi sai an yi shi wallahi, dan ba zamu ji kunya a idon mutane ba"

Iya cewa take "Bi shi a hankali saminu, na sani ba son ta ka ke yi ba, muni kam akwai shi amma ka yi haƙuri, tun da kai ka janyo komai, mun riga mun tara mutane, idan muka ce an fasa dole za a so jin ba'asin abun da ya faru uban me zamu ce musu? Ko kuma gaya musu abun da ka aikata zamu yi?".

Cike da iskanci, da rashin É—a'a ya ke kumbura baki yana masifar, shi fa baya son ummi, hindu yake so.

Iya ta fusata ta ce "Uwar hindu ka ke so ba hindu ba, É—an iska mara mutunci, ba gata aka yi maka ba? Ka je ka yi abun da ka ke ganin zai fishsheka"

Suka tafi suka bar shi, yana wani irin huci da takaici, yarinyar da aka gama lalubewa, wanda yana da tabbacin ba shikaɗai yake yi mata ba, ga baƙi ga muni, ace ita zai aura dan an raina masa hankali, ga hindunsa ƴar fara mai kyau, ace wai ya auri ummi, za ta ci ubanta kuwa, da ƙafarta zata gudu.

Magaji ne ya shiga ɗakin su da kayansa da ya karɓo daga guga, ya kalli idiris ya cika yayi fam, yake ta tsaki da ƙanan maganganu.

"Gunagunin me ka ke yi haka ne?"

"Ba dole in yi gunaguni ba, saboda an tsane ni, za a cuce ni a kassara rayuwata da ta yaran da zan haifa"

"Wai ka da waye ne? Me kuma aka yi maka?"

"Iya mana" ya faÉ—a a fusace.

"Too iya kuma? Duk kusancin naku, yau a ganku a rana?"

"Ba wani kusanci, za a zalunce ni, wai dan an fasa aurena da hindu, wai sai an ɗaura mini aure da wannan buranyar yarinyar, mummuna wai ni za a aurawa ummi, wai ba zasu ji kunya ba, wannan jakar yarinya mai kama da mayu, ita fa iyan da kanta take faɗar baƙin halin uwarta, kuma za a liƙa mini"

Sakin kayan hashim yayi, bakinsa na rawa ya ce "Wace ummin?"

Idiris yayi masa mugun kallo ya ce "Wace ummin ban da wannan baƙar yarinya, da goshi kamar tsinin jirgi, mummuna ido kamar na kyanwa wallahi ni an cuce ni, kuma wallahi ko an yi auren sakinta zan yi"

Bai bi ta kan kayan ba, ya fita da sauri, ya nufi sashin mahaifiyar su, wanda nan ma ya ɗau harama da mutane, uwar ɗakin mahaifiyarsu ya shiga, ya tarar da ita tana ƙirga kuɗi.

'yaya" ya kira sunanta.

Ta kalleshi ta ce "Ya aka yi?"

"Wai da gaske Idris ummi, za a aura masa?".

Ta ce "Mhmm nima haka na ji"

"Amma yaya meyasa?"

"Kafi kowa sanin ai abun da ya aikata, Iya ce ta kawo wannan shawarar, mu ma rufin asirinmu ne ai"

Kamar Hashim zai yi kuka ya ce "Amma yaya kin san yadda Idris yake da yarinyar nan, gata yarinya ƙarama,a haka zaku bari ayi auren nan?"

"To ni na isa in hana ne? Kai ka san babu mai ja da maganar Iya ai ko?"

Bai sake cewa komai ba ya fita, ya nufi sashin iya, a ƙofar ɗakinta ta hange shi, yana tsaye yana kallonta, fuskarsa babu walwala.

Cikin azama ta fito, dan kar magajin ya faÉ—i wata maganar banzar, a cikin mutane ya tona musu asiri.

Ta ce "Menene?"

"Iya wai kin ce a aurawa idiris ummi, saboda an fasa auren sa?"

"Eh sai yaya?"

"Amma Iya kin san ba son ummi yake yi ba...

Ta katse shi ta hanyar cewa "To ina ruwanka, ku yaran zamani ku kuka san wata soyyaya, mu duk bamu santa ba, idan ya aureta ko daga baya ya saketa, ba shikenan ba in dai asirin ya rufu, ai ba ana nufin yayi ta zama da ita bane ba din-din"

Galala yake kallon Iya, idan dai-dai ya ji, kamar ta ce ko daga baya ya saketa, wato rufin asirin kawai suke nema, ko da hakan yana nufin tarwatsa rayuwar marainiyar.

"Amma iya"

"Kai rufe mini baki, bana son ƙauli da ba'adin banza, sai in ci maka mutunci yanzun nan, fice ka bani wuri" zuciyarsa na wani irin tafasa ya bar sashin na iya.

Shikenan saboda ummi bata da gata kowa ya goyi bayan Idris, ummi ko Æ´ar tsintuwa ce, ya ci ta ci albarkacin ita ma É—an adam ce a kula rayuwarta, balle ita ma cikakkiyar Æ´a ce a gidan, yadda idiris yake cika yana batsewa yana masifa, ka sam babu Allah a ransa kuma babu abun da ba zai iya yi ba.

Suka cigaba da shiri, sai washegari da safe, Iya ta kira ummi, da ta sha uban wanke-wanke.
Ta hura wutar kunu, ƙanwar Iya nata yabonta tana cewa taje ta huta.

Iya ta kira Ummi, ta kalleta ta ce "Ki je ki duba a tsummokaranki masu kyau ki wanke su, an fasa auren Idris da ke za a É—aura, ki wanke kayan da zaki tafi da su, idan ya so daga baya a É—inka wasu daga kayan auren da aka dawo da su a kai miki, atamfarki da na saya miki ki sakata gobe É—aurin aure"

Sai da numfashin ummi ya kusa É—aukewa, na wucin gadi, ta haÉ—iye wani irin yawu da taji tamkar tana haÉ—iye wuta ta ce "Iy..Iya aure kuma?"

"Kurma ce ke ba ki ji me na ce ba?"

Karon farko da ummi tayi yinƙurin yin musu da Iya ta ce "Iya makarantar fa? Kuma yaya idiris dukana yake yi, dan Allah kar ayi mini aure da shi, ko da wa aka yi mini auren na yarda amma dan Allah ban da yaya Idris, wallahi dukana zai yi"

"Ke dalla rufawa mutane baki, ba taimakonki ma za ayi ba, da wannan munin uban wa ye zai aureki ya zauna da ke? Ai idiris taimaka miki zai yi, kamata yayi ki yi mana godiya, idan ma bai zauna da ke ba, ai an samu asiri ya rufu, da mu da ku baki ɗaya, ita dauɗar gora ai ciki ka sha ta,  ki je ki tsami kayanki ki wanke"

Kuka ne ya ƙwacewa ummi, ta juya ta tafi ɗakinta, ta kalli viva da take zuba kaya a ciki, ina wasu kaya ma suka banda tarkacen tsummokara, kuka kawai take tare da tabattarwa da kanta kashinta ya bushe.

Karo na farko da ba ta taɓa neman taimakon kowa, wurin gaya wa wani matsalar ta ko damuwarta ba, amma ta fito cikin tashin hankali, ta tunkari sashin su Hashim tana nemansa, da ta rasa shi a gidan, ta fita waje a can ta samo shi wata majalissa da suke zama, ba kowa a wurin sai shi.

Ya miƙe tsaye ya taro ta, jikinsa ya bashi wataƙila ummi ta samu labari, cikin dakiya ya ce  "Ummi lafiya?"

"Yaya magaji"

"Na'am Ummi"
Chapter 23 · 0% Book details