Sashe 90
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A fusace farida ta kasa jurewa, ta tafi harabar gidan, kausar tana riƙeta tana ƙoƙarin hanata.
Sai dai suka tarar da kujerun babu kowa, ta tambayi mai gadi, ya ce mata tun ɗazu suka shiga cikin gida. cikin zafin rai da zage-zage ta nufi ɗakin ummi, tana wani irin bugun ƙofar kamar za ta hau iskokai.
Noor ta fito ta ce "Maama maƙwabta fa suna jin ki, kina ta ɗaga murya"
Banza ta yi wa noor, ta cigaba da bugun ƙofar ɗakin ummi, tana ɗura mata ashar kamar bamagujiya.
Ummi kuma wani irin tsoro ya kamata, ta kasa buÉ—ewa tsoro take ji, ba ta san me faridan za ta iya yi mata ba idan ta buÉ—e.
Sai da farida ta ji ƙarar motar dr. Sannan ta saurara da bugun tana huci, dr. ya ƙaraso ya tarar da su a tsaitsaye, ya ce "Lafiya kuwa?"
Farida ta ce "Ina fa lafiya? wallahi na gaji, wai ba wurin uwarta ka kaita ba, meye na dawo da ita gidan nan, to wallaahi barin gidan nan za ta yi, ko a kan bola uwarta ta take, ta je su ƙarata"
Dr. Ya ce "Wai meyafaru ne?"
"Sai ka yi magana ta buɗe ƙofar ɗakin ka tambayeta ka ji, tun da kai ka isa da ita, ni tana ganin sa'arta ce"
Dr. Ya bubbuga ƙofar ɗakin ummi ya ce "Mamana ni ne buɗe ƙofar"
Cikin tsoro da fargaba ummi ta buɗe ƙofar, kallo ɗaya yayi mata ya san a tsorace take.
"Meyake faruwa?" Ya sake tambaya.
"Dole ka ce meyake faruwa tun da ta riga ta raina ni, wallahi ba zan cigaba da zama da yarinyar nan ba, ka mayar da ita wurin uwarta wallahi ba zan cigaba da zama da ita ba"
Cikin zafin rai ya ce "Dan Allah ki nutsu ki yi mini bayani, ummi ba ta taɓa yin haka ba, me ki ka yi mata?"
Cikin takaici farida ta ce "Au tambayata ma ka ke yi me na yi mata?"
"Dr. Maama ce fa ta aika anty kausar, wai ace ummi ta zo tayi girki alhalin yaya raihan ya zo, aikuwa ya ce ba za ta zo ba, anty kausar ta je ta yi girkin, ko su kwana da yunwa"
Gaba É—aya suka tsaya suna kallon noor, da ke wassafa abun da aka yi.
Ummi ta yi saurin cewa "Dan Allah anty ki yi haƙuri, wallahi ba ni na faɗa ba, kuma tsoron abun da ya faru da rashin sanin abun da zan ce miki ya sa na rufe ƙofar, kunya ma nake ji, dan girman Allah ki yi haƙuri"
Dr. Ya ce "Ummi wuce ki je ki kwanta, Allah ya yi miki albarka"
Ya kalli Farida ya ce "Ai gara da ya nuna miki ɗan zamani ne shi, kuma gaskiya ya faɗa miki, idan ba zaku girka ba ku zauna haka, dan ba baiwar ku ba ce ba, banda zubar da kai da son nunawa duniya rashin sanin ciwon kanki, su ƴaƴanki haka ki ke yi musu, shikenan yarinyar nan babu damar ta huta, har a gaban mijin da ta aura sai kin yi yinƙurin tozarta ta? Meye na wani ta zo ta yi girki, a bari ta dawo mana"
Babu kunyar idon Æ´aÆ´ansu farida ta din ga zuba wa dr. Rashin mutunci a gaban yaransa.
Yayi ƙoƙarin danne zuciyarsa ya shareta.
Har da iƙrarin ummi ba zata sake shigar mata kitchen ba, tun da ya fifita ummi a kan ta, sai ya ware mata kitchen ɗin ta ya raba musu kwana kuma.
Sosai ummi ta yi kuka, ba kowa ya ja wannan abun ba sai raihan.
Tun daga ranar takun saƙa mai zafin gaske ya shiga tsakanin ummi da farida, idan ta taho kausar ta taho, sai ta bangajeta, sabon wulaƙanci da tozarci iri-iri.
Farida har da iƙrarin in dai dan ta samu mijin aure ne, ta fara take-taken iskanci, sai gidan mijin ya zame mata gida mafi azaba da tashin hankali.
Ummi ta mayar da hankali a kan addu'a, tare da yaƙinin ko da raihan zai wulaƙanta ta bayan, ba zai kai yadda Idris ya ci zarafinta ba, tun da shi mutum me mai ilimi.
Can gida ma raihan Mami ta sake sako shi a gaba, duk ta in da ya motsa idonta na kansa, gashi sai cigaba da tura masa safiyya take yi, ɓangaren anty rakiya da safiyyan ma sun riƙe wuta sosai da sosai.
Ummi kullum sai sun yi waya da mama da su yaya maryam, maryam tayi ta gaya mata shirye-shiryen biki da suke yi, ummi sai dai ta yi murmushi ba ta iya cewa komai saboda kunya.
Ana tsukin wannan tashin hankalin, jami'ar bayero suka kori kausar daga makaranta, saboda rashin kawo points ɗin da ake buƙata, ga Inteesar gidan miji ya ƙara yi mata tsanani, saboda abokiyar zamanta ta samu ciki, da mijin da danginsa duk sun juya mata baya ta amarya suke yi.
Hakan ya saka ummi ta É—an samu sassauci, kamar yadda farida ta ce ta daina shigar mata kitchen, abinci sai ta É—an sai abu ta ci, da ta ga babu sarki sai Allah idan an yi girki ba ya ciyuwa, sannan ta ce ai ita da yaranta ba bayin ummi ba ne, ita ce yakamata ta zama baiwa, tun da tana cin albarkacin su, dan haka dole ta fito ta yi musu girki su ci.
Duk wannan abun bai damu ummi ba, dan ko a jikinta, farida ta shiga cikin tashin hankalin yadda za su sanar da dr. An kori kausar daga makaranta.
Wani irin kyau da sheƙi fatar ummi ta din ga yi, tayi kyau sosai da sosai, ga wani irin ƙamshi na mussaman da yake ratsata.
Raihan daga ya dawo daga office, sai mami ta tsiri kirshe shi ta hana shi fita,wai dan kar ya je wurin ummi, abun da ba ta sani ba shi ne, yana tsaka da aikin ma idan ya so ganinta sai ya ajiye yayi tafiyarsa wurinta.
Ummi ta dage a kan cewar, raihan ba zai saka mata kuɗin lefe a account ba ita tsoro take ji, yayi yayi da ita taƙi yarda.
Hajiya Aisha ce ta din ga kiransa tana tambayar sa ya batun lefe, ya ce mata sai sun yi aure zai yi mata, yanzu akwai matsala.
Hajiya Aisha ba ta takura masa a kan sai ta ji matsalar ba, ta san ta mecece dan haka ta ƙyale shi.
Amma ta ce masa dole ya yi wa ummi kayan fitar biki na gani na faÉ—a, ya amince da hakan ya ce mata su ba zasu yi wasu bidi'oi ba, sai an É—aura aure juma'a zai yi reception da abokansa da Æ´an uwansa, ita kuma su yi taronsu Saturday a kaita.
Lokacin biki ya cigaba da ƙaratowa, dr. Shikaɗai yake faɗi tashin sa, babu mataimaki sai Allah, babu wani wanda zai ba shi shawara, shi yake ta ƙoƙarin playing both roles ɗin, ya kira raihan ya tambaye shi ya yanayin gidan da zai ajiye ummi, saboda ya san me zai saya, raihan ya ce masa kar ya takura kansa yayi iya abun da zai iya yi.
Ummi ta sanar da dr. Abun da raihan ya ce mata a kan kayan lefe, dr. Ya ce "Ummi, ba kayan lefen ba, zaman aure mai ƙarko dan dai kayan da zaki saka, ni zan yi miki kar ki damu"
Ummi ta ce "Dama ba damuwa na yi ba, gaya maka dai kawai na yi"
Ya ce "Yauwwa mamana, na san ba zaki damu ba dama, Allah ya yi miki albarka"
Ta amsa masa da amin.
Dr. Kallon farida kawai yake yi, dan tuni ya san an kori kausar daga makaranta, amma taƙi gaya masa sai gaba da take yi da shi ma, a kan abun da ya faru tsakanin ta da ummi.
Message É—in da ummi da tayi tozali da shi a wayarta ne ya girgiza ta, ta duba lambar ba ta maryam ba ce ba, dan ta daina É—aga kiran maryam, idan tayi mata message kuma gogewa take yi.
Ta duba lambar a Truecaller ta ga an rubuta safiyya.
Shiryayyen zagi ne na cin mutunci da cin zarafi ta shiryowa ummi mai zafin gaske, tare da tabattar wa da ummin cewa ita ce matar da aka zaɓa masaya aura, dan haka ko ta aure shi tamkar zaman haya za ta yi a gidansa.
Ran ummi yayi mummunan ɓaci, ta sake duba message ɗin, sai ga kiran wayar lambar ya shigo wayarta, kamar kar ta ɗaga, sai kuma ta ɗaga ta saka a kunnenta ta yi sallama.
"Na san zuwa yanzu kin ga message É—ina ko? To kina magana da safiyya matar da raihan zai aura, tun wuri idan ki na son kanki da arziki, ki fita harkarsa, domin kuwa babarsa ba son ki take yi ba, mummuna da ke har zaki ce zaki aure shi kin yi masa asiri dan mugunta, to wallahi raihan nawa ne kuma sai na aure shi, ke ban da mugunta ma kina bazawara ni kuwa budurwa ce, ba zaki haÉ—a kanki da ni ba, mummuna kawai" gaba É—aya kalaman yarinyar ya tabattar wa da ummi yarinya ce.
Ummi ta yi murmushi ta ce "To meye a ciki safiyya? Namiji ba mijin mace huɗu bane ba? Sai ya auremu duka mu yi zamanmu, da matar so da matar shige, sai a cika bakin bazawara da budurwa, ai ni bani da damuwa ki tambaye shi ki ji, lafiya ƙalau zamu zauna da ke, in dai wannan alfarmar ki ke nema, na yi miki ƙanwata Allah ya bamu zaman lafiya"
Ta katse kiran ƙirjinta na bugawa da sauri-sauri, dan ba ta tunanin daga ƙuruciyarta zuwa yanzu, ta taɓa tsaya wa ta mayar wa da wani martani ba.
Ƙasan zuciyarta kuma wani irin tafasa yake yi mata, da tuna yadda take ce mata wai ita ce matar da aka zaɓa masa, lallai akwai aiki a gabanta kamar yadda yake gaya mata, to meyasa bai gaya mini ba?' ta tambayi kanta.
Kiran Safiyya ne ya cigaba da shigowa, amma tayi banza ta ƙi kula wayar, har magariba tayi ranta a ɓace yake, da ta tuna maganganun Safiyya sai wani irin haushi ya kama ta.
Tana kallon kiran raihan da ta yi saving lambar da MD, amma ta yi burus da shi, taƙi ɗaga kiran.