Sashe 118
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Rufe mini baki, abun da na ce shi zaka yi tun da har ka yi ƙwarin sakin mace, tun da ka ke ko tafi gidanku ka ga na taɓa cewa wata a matana?"
Ganin Alhaji zai sake rufe raihan da faɗa ya sanya ta ce "Alhaji ka yi haƙuri, ba laifinsa bane ba laifina ne, rashin fahimta ne na zata sakina zai yi shi ne na tafi"
"A'a ban yadda ba, ƙoƙarin kare shi ki ke yi, babu yadda za ayi ki tafi ba tare da izininsa ba"
Dr. Ya ce "Ni bama haka ba, banda abunki ummi, da lamarin ya faru maimakon ki taho gida, sai ki yi wani wurin, ayi ta nemanki ba a san in da ki ke ba, haka ake yi? Ba ki taɓa ɓata mini rai kamar a wannan karon ba, ummi kuma saboda rashin neman albarka gidanmu na gado na iyaye da kakanni, ki ka sayar da shi haryanzu ina tantama idan ke ki ka aikata haka, kin bani kunya kuma fushi nake yi da ke"
Alhaji ya ce "A'a dr. Ban tari numfashinka ba, a fara jin ta bakinta"
"Haba Alhaji Tahir, ai komenene hanzarinta abun da ta aikata yayi muni, iyayenta ne fa a ciki har da babarmu, wane irin abu ne wannan? An ce mini ma ke ki ka yi sayi gidan, a ina ki ka samo kuÉ—in sayen gidan?"
Ummi ta fashe da kuka, sai kuma nadamar abun da ta yi ya ziyarci zuciyarta, ta ga lallai ta yanke mummunan hukunci cikin fushi.
Raihan ya ce "Dan Allah kawu ka yi haƙuri, ka yi mana afuwa mun yi kuskure, ba laifin ummi bane ba, ni ne na sayi gidan, saboda ta dawo, dan Allah ku yi haƙuri ku yafe mana mu koma gida ba ta da lafiya"
Salim ya girgiza kai, ana ƙoƙarin gyara abu, shi ta a koma gida yake yi, kuma sai ƙumbiya-ƙumbiya suke yi, sun ƙi magana sai kare juna.
Ummi ta ƙarasa gaban dr., Tana kuka ta riƙe ƙafarsa ta ce "Dan Allah kawu ka yi haƙuri, fushinka a gareni fitina ne, na yi laifi na yanke hukunci cikin fushi, na yi haka ne dan rage raɗaɗin da yake zuciyata, wallahi dr. Wanda ku ke so na a duniyar nan ba afi a ƙirga ku ba, shikenan ranar da babu ku haka zan tagayyara?.
Na zo gidan nan, Anty ta ce ba zan zauna ba, ba zan sake zaunar mata a gida ba, na je gagarawa iya ta kore ni, wai bani da mutunci babu gadon ubana a gidan, tayaya zan koma maiduguri daga yin aurena ace ya mutu, ai sai su tsane ni, na rasa yadda zan yi na kasa tunanin komai, zuciya ta ɗebe ni na yi abun da na aikata dan Allah ka yi haƙuri kawu"
Cikin takaici ya ce "Faridan ce ta kore ki daga gidan nan?x ummi ta jinjina kai alamar eh.
Raihan ya ce "Dan Allah kawu ka yi haƙuri, mun yi laifi ".
"Rufewa mutane baki, duk da baka saketa ba ya za ayi haka ta faru, kuma kema ummi waye ya gaya miki dr. ne kawai babanki, ni meyasa baki zo wurina ba? Ina da masaukin da zan ajiyeki ko da ba kwa tare da raihan, tun da ba shi da kirki bai san halacci ba".
Salim ya yi gyaran murya ya ce "Raihan ka yi haƙuri da abun da zan faɗa, Alhaji da raihan da ummi, duk ƙannena ne, kuma stll ina da ƴan uwa mata, da ba zan so su tozarta a gidan aure ba. Ummi da raihan suna zaune lafiya da junansu, mami ce ta saka ya saki ummi" gaba ɗaya suka kalli Salim. Bai damu ba ya cigaba da cewa "Na je gidan Raihan maigafi ya ce mini kwananta biyu ba ta gidan, kawai na ji jikina bai bani ba, mussaman tun da na ga maryam ta zo gida, da kuma saɓanin da suka samu.
Na zo nan gidan, na yi sa'a na haÉ—u da noor, ita ta gaya mini raihan ya saki ummi, kuma mami ce ta saka shi, nan gidan kuma matar gidan ta ce ba zata zauna ba.
Na koma gida na ritsa Nihal ta sake tabattar mini da hakan. Na je garinsu can gagarawa, na haÉ—u da ummi kan ta bar gidan, ta gaya mini abun da ya faru, da yadda ta koma gidan yayanta ta zauna. Na yi ta zuba ido in ji ko raihan zai faÉ—i abun da ya faru amma shiru bai yi magana ba"
Tsit falon yayi, raihan ya É—aga kai yana kallon Salim, kenan duk wannan wahalar ya san in da ummi take, amma bai gaya masa ba?.
Dr. Ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"
Alhajin ma Innalillahi wa Innalillahi raji'un ɗin yake maimaitawa "Wai mata wane irin tunani ne da su haka? Har ki saka ya saki yarinya saboda wulaƙanci me tayi mata?"
Raihan ya yi farat ya ce "Wallahi ban saketa ba Alhaji, ban ba ta takarda ba, ban faÉ—a mata da baki ba kawai tafiya ta yi"
"Rufe mini baki, tun da nake banbamina ka gaya mini abun da ya faru?" Raihan ya sunkuyar da kai.
"Kema kuma ummi baki faÉ—a ba duk ku ka yi shiru ko?"
Salim ya ce "Alhaji, dan Allah duk ku yi haƙuri aikin gama ya riga ya gama, tun da dai ya ce bai saketa ba, ayi haƙuri su koma gidansu"
Raihan ya ce "Eh Alhaji, ayi haƙuri dan Allah, kawu dan Allah ayi haƙuri dan girman Allah"
Dr. Ya ce "Shikenan, É—auki matarka ku tafi, Allah ya kiyaye gaba"
Alhaji ya ce "Da dai ka bari an hukunta shi daga shi har ita"
Raihan cikin zumuÉ—i ya cewa ummi ta tashi su tafi.
Daga dr. Har kawu sun ji takaicin abun da ya faru, sun daÉ—e suna tattaunawa sannan suka yi sallama.
Sai dai Alhaji ma ya yi wa Salim faɗa sosai na ɓoye masa abun da ya faru.
Sai dai danne fushinsa yayi, dan ba ƙaramin takaici da kunya ya sha ba, da aka ce wai Bilki ce ta saka raihan ya saki ummi.
Dr. Bai cewa Farida komai ba, dan haka ba ta kawo zai ce mata wani abu ba.
Daga ƙauye sagir ya kira dr. A waya, kamar zai fashe da kuka yana yi masa magiya a kan ya dubi Allah ya yi wani abu a kan lamarin nan, sun rasa yadda za su yi ba za su iya haya ba.
Dr. Ya ce "Sagir ai aikin gama ya riga ya gama, sun riga sun sai gida, sai ku yi magana da su, ko ku din ga biyanta haya ko kuma ku bar mata ni ban san yadda zan daidaita wannan al'amarin ba"
"Yanzu haka zamu tagayyara da mu da mahaifiyarmu?"
"To Sagir ya zan yi? Ku kuka nuna wa yarinyar nan ƙiyayya, kuna ina iya ta koreta daga gidan waye yayi magana a cikinku? Ko kana tunanin za ta manta wahalar da ta sha tana yarinya babu wanda ya iya jiɓantar lamarinta? Nima da fari na ɗau zafi amma daga baya na fahimce ta, kuma yanzu ummi ba a hannuna take ba, mijinta zaku tuntuɓa shi ne ke da alhaki da ita yanzu"
Haka dr. Ya yi ta artabu da Æ´an gagarawa, fafur ya ce ba ruwansa.
Alhaji yana zuwa gida, kai tsaye ya wuce sashin mami, tana zaune tana waya da Anty rakiya, a kan shirin auren Safiyya, yadda Alhaji ya shigo ya sanya ta É—an tsorata ta ajiye wayar ta ce "Alhaji lafiya?"
"Ban sani ba, biliki wace irin mace ce ke ne? Ina iliminki da tunaninki suke? Saboda tsabar wulaƙanci da rashin mutunci, ki je ki saka raihan ya saki matarsa? Ki zubarwa da kanki kima ki zubar mini? Na zo miki da zancen ya saketa ba a san in da ta tafi ba, ki ka nuna mini baki san zancen ba, ashe ke ce kanwa uwar gami ki ka raina mini hankali? Lokacin da na aureki bilki sa'an aurenki ne ni? Ban taɓa yi miki gori ba amma yau zan yi ke kin san idan nasabar dukiya ce ke ba sa'ar aurena ba ce, idan kyau ne na fiki ta ko ina, soyayya ce ta saka na aureki ke ba auren na aure ki, na zauna da ke nake kyautata miki? Ke ba a auren aka auri naki ƴaƴan? Kin tsiro da zancen yayi aure yana ta ƙoƙarin kaucewa, kina ta wasu abubuwa ashe ke kin je kin saka ya saketa. Wallahi bilki idan ba ki shiga hankalinki ba, idan baki bar yaron nan ya zauna lafiya da matarsa ba, kema zaki koma naku gidan, tun da ke ba mutuniyar kirki ba ce"
A razane ta kalleshi ta ce "Alhaji ni ce zan koma gidanmu, da girmana da komai?"
"Eh ke É—in, zama dake ai ba dole bane ba, tun da ba ki da girma kema" yayi mata ta tas ya fice a fusace.
"Lallai yarinyar nan, wato sai da ta faÉ—a kenan? To wallahi da ni take zancen, É—a na ne sai ta rabu da shi in dai ina raye".
Raihan kuwa cigaba da tattalin matarsa yayi, yana rarrashinta.
Kwanan ummi uku da komawa gidan raihan, dr. Ya saka noor ta koma gidan ummi ta É—an zauna da ita saboda rashin lafiya.
Ƙarshe Alhaji ne ya sake tafiya Abuja, wurin sabon kamfaninsu, saboda gaba ɗaya raihan hankalinsa ba ya jikinsa, saboda ummi kamar ba za ta yi rai ba, saboda wahalar laulayi.
Sai dai mami ba ta daddara ba, sai da ta je har gidan raihan, ta sake yi wa ummi wankin babban bargo, ta zageta tsaf raihan baya nan, noor kuma ta tafi makaranta.
Har ta yi ta gama cin mutuncin ta, ummi ba ta tanka mata ba, dan ita ciwon da take fama ya isheta.
Sai dai maganganun da ta gaya mata na cin mutunci sun yi mata zafi, amma ta shanye.
Share² da girki duk noor ce take yi wa ummi.
Da azahar raihan yake cewa ummi, dr. Ya ce zai zo, dan haka da kanta ta lallaɓa ta shiga kitchen ta taya noor suka yi girki.
Bayan la'asar sai ga dr. Da Æ´an uwan babanta na gagarawa, har da yaya magaji.