Sashe 124
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Farida ta saki baki, hangal tana kallon ummi, ba ta gama mamakin ba ummi ta ce "Yauwwa tun da bani da abun baki, zaki iya tafiya, na ga kin yi mini aike noor ta koma, in dai noor ce, sai dr. Ya ɗauke ta ya ba wa mamana, saboda kin raini ƴar ki da ƙiyayyarki, saboda banzan dalilinki, na an saka mata sunan mahaifiyata, duk shaƙuwar ɗa da uwa, ta fi son babanta a kanki, cikin sauƙi zan sanya ya karɓe ta ya bawa mama ita, ba zan so ta tashi da rashin imani irin naki da su kausar ba, masu baƙar zuciya ba, tayi aure tana hali irin naki ba, idan kin fita ki rufe mini ƙofar falo, kar ƙuda ya shigo mini bana son ƙuda" ko jiran amsar farida ba ta jira ba, ta bar falon ta bi wata hanyar, ta tafi can bedroom ɗin da noor take, wadda ba ta san ma farida ta zo ba.
Ƙarfe huɗun yamma, dr. Ya sauka, basu tsaya ko ina ba sai gidan raihan, ta rungume ummi suka din ga murna, kamar sun shekara ba su ga juna ba.
Sam farida ba ta san ranar ma maiduguri ya je ba, yana komawa gida, ta dira masa bala'i tana gaya masa abun da ummi ta yi mata.
Kai tsaye ya ce ƙarya take yi wa ummi, sharrinta ne kawai ummi ba zata aikata haka ba, tsabar kishi ne kawai, idam ma hakan ne meyasa da ba ta je gidan ummi ba sai yanzu da wannan lamarin ya zo.
Abun duniya duk ya ishi farida, asirin tayi har ta gaji, ya shammaceta, da kan ayi ne da ta yi yaƙinin asirin zai kama shi, maganar ta rushe.
Raihan ma ba ƙaramin daɗin zuwan mariya ya ji ba, tayi ƙalau da ita.
Noor kuwa tun bikin ummi da suka je maiduguri, suka saba da mama, tun da dr. Ya gaya mata takwararta ce.
Kuma aka yi sa'a ba ta manta ta ba, a ranar da daddare, sai ga Salim ya zo har da Sagir.
Mariya ta din ga murna, duk idan tana magana wasu lokutan ta kan haɗa da shirme, amma a hakan take yi musu nasiha, tare da ƙara musu haske a kan rayuwa.
Sagir ya din ga mamaki da aka ce ita ce maman ummi, ita da haskenta ma, ummi ce dai baƙa, sai dai idan tayi wani abun kamar ummin.
Ta tsiro da batun cewa lallai, a kai ta su gaisa da babar raihan, da babansa sun gaisa da Alhaji, babar raihan ce ba su taɓa haɗuwa ba.
Gaban raihan ya faÉ—i, amma ya basar ya ce zai kaita su gaisa.
Su Salim sun daɗe sosai, duk da a zahiri bayan mama, noor ce ta riƙe shi, dan chatting suke a wayar ummi ba ta sani ba, idan suka gama sai ta goge.
Ummi ta yi iya ƙoƙarinta, ta mantar da mariya, batun haɗuwa da babar raihan.
Allah ya taimaki Iya, ba ta samu mumunan rauni ba, sai dai ta fasa kai, fuskarta duk ta ƙuje, sannan ta targaɗe ƙashin ƙafarta, da hannunta, gashi kuma kanta sai da aka yi mata ɗinki, kan ayi ɗinkin nan kuwa sai da aka sauke gashin kan gaba ɗaya, ga bakinta ya kumbura saboda wahala.
Da ƙyar suka yi karo-karon haɗa kuɗin magani, likita ya rubuta hoton ƙwaƙwalwa, saboda kai da take ta kuka da shi, amma babu kuɗin yi, maganin ma ba duka suka saya ba.
Suna tsaka da wannan gaganiyar, ana ƙoƙarin kiran dr. Suka samu labarin yayi aure, ya auri mariya.
Gaba É—aya sai suka manta da halin da iya take ciki, suka shiga salallami.
Iya na daga kwance ta tuna yadda tun bayan ya gano in da mariya take, ya ce zai aureta, amma ta ce ba ta lamunta ba, tun da ya riƙe ummi shikenan, ba zai sake kwasota ya kawo musu dangi ba, saboda a cewarta mariya annoba ce, mugun abun ta ne ya sanya ta haukace.
Su ummi suna airport, tare da dr., Ta wani ɓangaren ransa a ɓace, saboda tijarar da ya sha a wurin farida daren jiya, da ya ce yau zai koma uganda, tare da babar ummi.
Har da zaginsa ta ƙare masa cin mutunci, abubuwa da dama yana duba yaransu ne ya sanya yake ɗaga mata ƙafa, kuma tun ainihi, shi mutum ne mai sanyi ba shi da hayaniya, shiyasa take yi masa duk abun da ta ga dama.
Suna airport sun rako su dr. Mariya sai kalle-kalle take yi, da alama a tsorace take.
Sai ga wayar kawu Sagir, dr. Ya É—aga tare da amsa masa sallamar.
"Yanzu yahaya tsakaninmu da kai abun har ya kai haka? Muna Æ´an uwanka amma sai dai mu ji a gari ka yi aure? Abokanka sun fi mu kenan?"
Dr. Ya ce "Ba abun ɗaga hankali bane ba, abun ne ya zo ba shiri, na ga akwai buƙatar tun ina raye ya zamana ummi tana da madogara ko bayan raina, dan yadda ba a kula da ita bayan ran mahaifinta ba, bayan raina ma ba za ta sauya zani ba, dan na san kun san wadda na aura, kuma da na neme ku, ba zaku bari ba, da kaina zan zo har gida na yi muku bayanu"
"Aishikenan, ni ba ma wannan ba, ka ganmu fa a asibiti da iya"
"Subhanallah me ya same ta?"
"Wallahi dai tsautsayi ne, Auwwalu ne ya sha ta gaya masa ƙarya, ta yi masa faɗan rashin sana'a sai bacci, ya din ga tamaula da ita, saura ƙiris ya jefa ta a rijiya. Yanzu dai gamu a asibiti, magunguna an sayi wasu, wasu kuma ba a saya ba, ga hoton kai an rubuta shi ma ba kuɗin"
Dr. Ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka ga illar rashin mayar da hankali a kan tarbiyyar yara da iliminsu ko? Ina Auwwalun yake?"
"Ya gudu ba a san in da yake ba".
"To ka ga ni yanzu ina filin jirgin sama, zan koma makaranta, zan turawa Abdul kuɗi ya zo ya dubata ya baku, Ubangiji Allah ya sauwwaƙe"
"Amin, amma dan Allah yayi sauri ana buƙatar kuɗin"
Dr. Ya ce "Sai ya tura muku, idan ya so daga baya sai ya zo ya dubata"
Kawu Sagir ya ce "To hakan ma yayi, bari na ga Idris yana da lambar banki, sai a turo ya saka kuÉ—in, an gode" bayan dr. Ya gama wayar suka din ga jajantawa, mariya kuwa ko Allah ya kyauta ba ta ce ba.
Ummi har da hawayen murna, ganin mama tare da dr. Za su keta hazo tare, ko ba komai tana sanyawa mama ran samun kulawa daga dr. Kasancewarsa jajirtaccen mutum.
A ranta ta ce "So so ne, amma son kai ya fi, in sha Allah a kujerun hajji da umaran da Alhaji yake rabawa sai kun samu, ko ban je ba ku je a tare hakan nan, ku yi mini Addu'a.
Bayan jirginsu ya É—aga, suka koma gida.
A cikin jirgin ƙanƙame dr. Ta yi, saboda gani take kamar za su faɗo daga cikin jirgin.
Dariya ya din ga yi mata, ganin yadda take a rikice gaba ɗaya, hakan ya bashi damar rungumeta a jikinsa, sai wani irin daddaɗan ƙamshi take yi.
A hankali take tambayar sa "Baban ummi ba zamu faÉ—o ba kuwa? Tsoro nake ji sosai"
"In sha Allah ba zamu faÉ—o ba, lafiya zamu sauka".
Dr. Dubu hamsin ya turawa Abdul, ya ce masa ya tura wa su iya idan sun turo account number, shima ya ƙara dubu talatin ya tura musu dubu tamanin.
Ummi bayan sun koma gida, raihan ne ya sakata a gaba, yana mammatsa mata jikinta a hankali cikin tsantsar soyayya da kulawa yake ce mata "Am sorry sweetheart, kwanan nan am very busy, kamar bana kula da ke sosai, kuma na san kina buƙatata"
Tayi murmushi ta ce "Saboda jin daÉ—i yayi mini yawa ko? A cikin mata hamsin nawa ne suke samun kulawar da nake samu, idan suna da juna biyu, kana iya yinka aiki ne yayi maka yawa".
Ya numfasa ya ce "Duk da haka dai, wallahi ummi wasu lokutan kaina kamar ya fashe, ina jinjinawa Alhaji yayi ƙoƙari, kin ga yakamata ace Yaya salim yana cikin system ɗin nan, tun da bamu muka tara dukiyar ba, mu kula mu tattalata ta haɓaka, ga branch ɗin mu na Abuja, ina ga a watan da zaki haihu za a buɗe shi, ban san ma ya zan yi ba, wa za a mayar can Abujan, atleast yakamata ace da wani daga cikin mu"
Ummi ta ce "Mhmm ka lura zuwan yaya Salim gidan nan ya ƙaru sosai?"
Ya jinjina kai ya ce "Magana ce kawai ban yi ba"
"Anya nan gaba magana ba zata taso tsakanin sa da noor ba, shaƙuwarsu ta yi yawa"
Cikin murna raihan ya ce "Wallahi sam ban kula ba, tun da ya ce ke ƙanwarsa ce na zata saboda ke ne, yana cigaba da bibiyata ne kar na yi miki wani abu. Amma kina ganin dr. Zai bashi ita? Kamar yayi mata tsufa kuma ga yanayin sa"
Ummi ta ce 'Aikuwa yaya Salim ya shiryu, a kan lokacin da na san shi, ba abun da zai hana ya bashi ita, nima haka aka yi mini surtu da na aureka, in dai suna son juna ba shikenan ba"
Ya jinjina kai ya ce "To Allah ya tabattar mana da alkhairi, Kairun nisa'i, wannan cikin naki kamar ya fi ƙarfin watanninsa, kafin mu koma awo, sai mu je ayi miki scanic kawai mu tafi da shi"
Ummi ta shafa cikin ta ce "Nima na gani, kamar girman yayi yawa a wata biyar, amma sai a sake hoton"
Sun jima suna hirarsu cikin nishadi, har ta nemi izininsa a kan zuwa duba Iya, an kai ruwa rana kan ya amince, ta ce idan Abdul zai tafi sai ta bishi ita da noor.
Ummi tun bayan dawowarta, ta duƙufa Addu'a, da roƙon Allah ya sassauta mata mugun kishin da yake damunta.