Sashe 32
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yanzu kwana É—aya tal a gidan nan ta fara haÉ—a ni da shi? To wallahi da sake ba zai yiwu ba"
Ran farida yayi matuƙar ɓaci, ta din ga cin alwashi kala-kala na mugunta a kan ummi.
Ya tafi da ita wurin aikinsa, ya kulleta a office ɗin sa, ya je ya gabatar da lectures ɗin da zai yi, wajen ƙarfe sha biyu na rana, ya tafi da ummi kasuwa.
Ya sai heater da nurse É—in nan ta ce ya saya, ya sai mata phants dozen É—aya, ya saya mata soso sabulu, brush, manyan jakar omo. Ya saya mata sababbin kaya wasu ready made wasu kuma sai an É—inka, kasancewar yana da yara mata, kuma shi yake sayen komai na gidan sa, dan haka duk wani abu na É—awainiyar yara mata ya sani, hatta É—an kunne sai da ya saiwa ummi, under wear vest duk ya saya mata.
Ya ce suje mota ta zauna ta huta, ya ƙarasa sayayyar, wani irin farinciki ummi take ji, saboda kayan nan da aka saya mata, gani take kamar a mafarki, wai duk wannan kayan nata ne, har da su ɗan kunne da ribbon, ga takalmi mai kyau, ta din ga kwarara masa addu'a a cikin zuciyarta.
Wurin masu sayar da kayan ƙamshi yaje, domin haɗa magungunan da aka gaya masa a yi wa ummi.
Sai dai wasu abubuwan duk ya manta yadda aka gaya masa, mai kayan ya tambaye shi, mai zai yi da su, yake gaya masa ai maganin sanyi za a haÉ—a.
Kasancewar mutumin sana'arsa ce, sai ya haÉ—a masa komai da yadda ake amfani shi.
(Previous page, na bayar da magungunan in breif, wasu sun biyo ni suna so, yanzu zan rubuta full yadda ake amfani da su)
_Kanumfari
_Tafarnuwa Æ´ar kaÉ—an ba mai yawa ba, saboda idan tafarnuwa ta huda jikin mace, tana sanya warin baki, na jiki har da na al'aura ma, sai dai maganin sanyi ce sosai.
_Tumeric (yellown kur-kur)
_Namijin goro
_Citta mai yatsu
_Lemon tsami
Kowanne za a zuba shi in a moderate amount, lemon tsami babba guda ɗaya mai ruwa ya isa, namijin goron ma za a iya daddatsa shi, yana da ɗaci sosai, tafarnuwa one clove, sai citta mai yatsu madaidaiciya guda ɗaya, sai 1 table spoon of tumeric, sai a zuba ruwa kamar 2cups, a dafa su a din ga sha, za a iya zuba zuma, saboda yana da ɗaci, za kuma a iya haɗe su a mazubi guda, a jiƙa su, su jiƙu sosai a din ga tsiyaya ana sha.
Idan wannan bai samu ba, ana iya jiƙa kanumfari, a din ga sha yana maganin sanyi sosai, amma sai an juri sha.
Sai kuma ana samun saiwar zogale, a É—aurayeta da É—an gishiri, a tafasa ta da jar kanwa, a din ga sha, salam yake babu É—aci, amma yana maganin sanyi sosai.
Sai kuma kama ruwa da ruwan magarya da bagaruwa ba da yawa ba kaɗan a haɗa su a tafasa, ana kama ruwa da shi, ganyen magarya yana gyara jikin mace, mussaman bayan gama al'ada, ayi shaving a din ga kama ruwa da shi, kuma a din ga ɗiga farin miski a kan phant, ba a jiki ba, yana kawar da ƙarni ko wani wari mara daɗi, but mark you ba kowane wari ne yake fita a gaban mace na infection ba, akwai bacterias ɗin da suke wurin wanda ba masu cutarwa ba ne ba, suna haifar da wannan ƙarnin wasu lokutan.
Galibi na infection ko na ƙazanta ya fita daban mussman idan ya haɗa da ƙaiƙayi ko ƙuraje shi ne na infection.
Shi ma wannan warin, ana iya amfani da apple cider vinegar, ruwa kal da hausa, ana zuba tablespoon É—in sa biyu, a ruwa cikin kofin shan shayi a din ga sha, yana magance warin gaba.
Sai dai dole a kula da abincin da ake ci, domin cin abinci mai ƙarni, ko wari kamar kifi, albasa ko tafarnuwa suna da tasiri a gumin mu da sauran fluids da muke fitarwa a jikinmu.
Kawu yahaya duk ya haÉ—owa ummi abubuwan da suka kamata, suna tafe yana sake yi mata bayanin yadda zata yi amfani da su.
Sai azahar suka koma gida, sai dai matar gidan bata nan, da kansa ya bi ummi É—akin masu aikin, ya dudduba abun da babu ya ce zai sayo mata.
Tamkar yar da ya haifa a cikinsa haka yake jin ummi,kuma haka yake burin ta samu lafiya daga wannan ciwon, dan ya san illarsa da hatsarinsa, dan ya san halinsu maza bakomai suke iya jurewa su kawar wa da kai ba.
Ya nuna mata yadda za ta din ga amfani da heater, da sabon flask É—in ruwan zafi.
Da kansa ya tafasa magungunan, ya zuba mata a jarka, na kama ruwan ya zuba mata a cikin flask É—in shayi, ya É—aukko tsintsiya ya taimaka mata wurin gyara É—akin saboda an kwana biyu ba a gyara shi ba.
Ya je É—akinsa ya duba bedsheet É—in da shi ya saya da kuÉ—insa, har da bargo ya kawowa ummi.
Ya bata babban gwangwanin turare a cikin nasa ya ce ta din ga fesawa.
Kallonsa kawai ummi take yi, cikin jin daÉ—i da annashuwa, yadda ya zage yake ta É—awainiya da ita, daga jiya zuwa yau, idan ta ce ya bari tayi da kanta, sai ya ce mata ai bata da lafiya, kuma cikin barkwanci ya ce mata albarkar ummansa yake nema.
Haka nan ummi ta din ga murmushi tana yi masa godiya.
Ya ce "Yauwwa ummina, Allah yayi miki albarka, saura makaranta ita ma in sha Allah sati mai kamawa, zaki koma makaranta ki manta da duk abu da ya faru, iyaka dai kar ki sake ki gaya wa wani kin taɓa aure kin ji ko?"
Ta jinjina masa kai ya ce "Good, yi wanka ki yi salla, a cikin kayan nan akwai gurasa ki ci kiyi kwanciyarki ki huta"
Murmushin kawai da ya gani a fuskar ummi, ya sanya shi cikin farinciki, kullum yaje ƙauye sai dai ya tarar da ita cikin kuka, sai kuma Murmushin yaƙe.
Hatta yadda zata din ga amfani da banÉ—aki, sai da ya nuna mata komai.
Fitowa yayi daga ɗakinta, a zuciyarsa yana tawasalli da farincikin da ya saka marainiya yana addu'a Allah ya biya masa buƙatunsa na alkhairi.
Ba yau farida ta fara fita yawonta ba, tun yana faÉ—a har ya gaji ya daina yi.
Ummi kuwa tun daga kama ruwan da tayi, ta ji daÉ—in jikinta, ta tsiyayi maganinta ta sha bayan ta ci gurasar nan, ta É—auki sabon phanta ta canza.
Wani irin daÉ—i take ji da nishaÉ—i, ta sake bubbuÉ—e kayan da ya saya mata tana jin daÉ—in hakan.
Ko da wasa ba ta yi gangancin fitowa daga ɗakin nan ba, dan ta fuskanci ƴan gidan ba ƙaunar ganinta suke yi ba.
Ana kiran sallar la'asar ta yi salla, ta cigaba da zamanta a É—akin.
Kamar an watso su, taga farida da rahama a É—akin, hakan ya sanya ta tashi a razane.
Farida ta ce "Tashi munafuka, ai ba zama ki ka zo yi ba" a zabure ummi ta tashi tana rarraba ido.
"Ba dai kawo ki aka yi leƙen asiri da saka mini ido ba, zaki ci ubanki sai kin bar mini gida da ƙafarki" idonta ya sauka a kan ƙatuwar ghana must go sabuwa fil.
Ta ce "Rahama janyo mini jakar nan ki zazzageta, wato zuwa yayi ya kashe mata kuÉ—i, wallahi ba zai yiwu ba ya daidaita da Æ´aÆ´ana, kar ta san kar ai".
Rahama ta janyo jaka, suka zazzageta, farida har da ashar, farida ta saka farida ta tsitstsince mata kayan, phants É—in ma duk ta kwashe ta bar mata uku, Allah ya taimaketa, tana da sauran wanda ta zo da su, da na'ima ta saya mata.
Cikin ikon Allah, Allah ya taimaketa basu lura da ƙullin kayan maganin da ke bayan katifar ɗakin ba, heater da flask ɗin kuma suna cikin banɗaki.
Hatta omo da sabulun da ya saya mata, sai da suka kwashe ta bar mata É—ai É—ai.
Sannan ta sake dubanta a wulaƙance ta ce "Ki buɗe kunnenki da kyau ki saurareni, nan gidana ne, abun da na dama shi ake sha, shima kwana biyu na sarara masa ne, amma tun da haka ya zaɓa zan yi maganinku duka. Ki saka a ranki ke ƴar aiki ce kawai a gidan nan. Kullum da yamma idan yara suka taso daga makaranta, zaki wanke musu uniform ki goge musu shi tas, wanke-wanke da duk wani aiki a gidan nan ke zaki din ga yin sa, idan ki ga dama ki gaya masa babu abun da zai iya yi a kai, bari in gaya miki ƙiri-ƙiri idan ki ka sake kiransa da Abba sai kin bar gidan nan, dan bai haife ki ba.
Kuma wanki ba na yara kawai ba, kaya ko na waye sai kin wanke a gidan nan, tashi mu je ma ki fara aikin ki daga yanzu. mummunar banza kawai".
Rahama ta kwashe da dariya ta ce "Ni wallahi fuskarta ma dariya take bani, wannan baƙi kamar a dangwala".
"Rabu da ita tashi ki wuce" ummi kaf maganganun su babu wanda ya ɓata wa ummi rai, dan ba yanzu aka fara yi mata ba, ƙwace mata kaya yafi komai ɓata rai.
Sai dai wata zuciyar ta ce da kin san zaki samu ne?.
Saboda tsabar mugunta akwai injin wanki a gidan, kuma akwai mai guga, amma farida ta tula wa ummi kayan makarantar su Abdul, na boko da islamiyyar su, kusan kowanne nasa set uku, daga na makarantar boko har na islamiyya.
Ummi ko a jikinta, ta durƙusa ta fara wankin kayan nan.
Tas ummi ta wanke su, kasancewar ta riga ta saba da wahala tun a gaban Iya.
Bayan ta gama cike da mugunta, rahama ta ja ta kitchen, ta sakata sassauke kwanukan da sun fi wata shida ba a saukko su an yi amfani da su ba, ta ce ummi ta wanke.
Babu ƙyuya ko ƙosawa ummi ta wanke su.
Duk yadda suka wahalar da ummi a yammacin nan har zuwa bayan isha'i, ko da wasa bata nuna musu gazawarta ba.
Kwanaki uku da zuwanta gidan, rashin mutunci da kyara, haka babar su Abdul suke yi mata, da yaranta da ƙanwarta, kuma wasu lokutan a hana ummin abincin.