← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 134

Sashe 20

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maganar Iya ta jiyo da idris ta ce "Ka tambayeta ina ta kai mini kuɗi, ka yi ta dukanta, har sai ta faɗa" kan ummi ta ankara sai ganin idiris ta yi a kan ta, hannunsa riƙe da manyan reshen bishiyar darbejiya.

Kafin ta yi magana, ya shiga shimfiɗa mata tsumagiyar nan a jikinta, gashi ya tare duk wata hanya da zata bi ta fita. Kasancewar dama haushinta yake ji, ya sanya ya zage duk wani ƙarfin sa, ya dinga jibgarta, har da taka ta da ƙafa.

"Fito mini da ita daga ɗaki, ɓarauniyar banza da ta wofi, kuma daga yau kin bar kwanar mini a ɗaki" a ƙasa haka ya din ga jan ummi, ya fito da ita tsakar gida.

"Ga É—akin uwarta can da ake tara itace yanzu, rufe mini ita a ciki, ko abinci kin daina ci, sai kin bani kuÉ—ina"

Haka kuwa aka yi, idris ya rufe ummi a É—akin mariya, da yanzu ake tara itace da hatsi a ciki, ya rufe É—akin bisa umarnin iya.

Ummi ta kwanta a ƙasa, jikinta sai zafi yake yi, hannunta da Idris ya din ga hauri da ƙafarsa, tamkar ba a jikinta yake ba, hannun yayi sanyi ga ciwo yana yi nata.

Sai da ummi ta kwana ta wuni a cikin É—akin nan, shima magaji ne ya ga baya ganinta, ya matsa da tambaya, su Alhassan suka ce masa ai Iya ta sacewa kuÉ—i dubu goma sha biyu, ta saka idiris ya zane ta, aka kulle ta a É—aki.

Hashim ya ji kamar ya É—ora hannu a ka yayi ihu, ya buge kwaÉ—on, ya tarar da ummi a zaune a takure wuri É—aya, saman idonta ya kumbura, ko ina jikinta rauni ne. Dogon gashin nan duk ya kwashi datti da karare.

"Ummi" ya kira sunanta, ta É—ago ta kalleshi ta sunkuyar da kai.

"Da gaske kin É—aukar wa iya kuÉ—i"

Ta girgiza masa kai, ya ce "Na san ba zaki ɗauka ba ummi, yi haƙuri taso ki fito"

Ta girgiza masa kai ta ce "Dan Allah yaya magaji ka ce Allah ya sa na mutu, bana son zama da iya, dan Allah ka kai ni wurin mama, wallahi zan mutu" tayi maganar tana sheshsheƙar kuka.

Ya kalleta yarinya shakaf, amma tana iƙirarin ta mutu, "Ba zaki mutu ba, wuya bata kisa ummi, tashi kar wani abun ya cije ki" Da ƙyar ya fito da ita daga ɗakin.

Iya kuwa duk ta gama barbaÉ—awa mutanen gidan ummi ta sace mata kuÉ—i.

Ko kallonsu Iyan ba ta yi ba, ya nemo abinci ya bata, ya ce tayi wanka.

Tana banɗaki, Hashim ya samu Iya ya ce "Iya dan Allah meyasa ba kya ƙaunar ummi ne?"

"Kamar yaya, in haifi ubanta ka ce bana son ta? Tarbiyya nake bata, uwarta na tsana ne, bana ƙaunar uwarta ne, kuma alamu sun nuna halin uwarta ta yi"

"Ba wannan ba, Iya kin duba ɗakin nan da kyau baki ga kuɗin ba? Ummi bata taɓa yi miki sata ba fa?"

"In ji uban wa? Faɗa ne kawai ba na yi, amma sata kam ba yau ta fara ba, kamar ta sha nonon ɓeranya"

Zai yi magana ummi ta fito daga wankan, tana ɗingisa ƙafarta.

Bai cewa iya komai ba, ya tashi ya bata kujera ta zauna, ya kamo hannunta da ya kumbura, ya fara matsawa a hankali. Nan ta din ga yarfe hannu tana kuka.

Fatar ummi duk wannan wahalar da take sha, jikinta tamkar auduga saboda taushi.

Iya ta watso mata ƙullin kayanta, ta ce sai dai ta koma ɗakin itace ta cigaba da zama.

Babu magiyar da magaji bai yi mata ba, amma ta ce bata san zancen ba.

Da kansa ya share wa ummi ɗakin, ya samo buhu ya shimfiɗa mata, ya kawo tabarma ya shimfiɗa mata, ya din ga rarrashin ta, yana bata haƙuri, ji yake kamar ya zauna ya yi wa ummi kuka.

Iya ta aika a kirawo mata Alhassan zata aike shi, ta ce ya duba ƙasan katifarta ya ɗaukko ɗari biyu, Alhassan ya fito da wata leda a hannunsa ya ce "Iya ba wannan kuɗin ki ke nema ba?"

A razane ta karɓa tana ƙifta masa ido, gaba ɗaya ta manta ina ta ajiye su.

Hashim yayi kamar bai ji me ta ce ba, haka ummi, sarai ummi ta ji Alhassan yana gaya mata kuɗinta, duk wasu kalaman rarrashi, sai da Hashim yayi amfani da su, wurin ba wa ummi haƙuri, saboda ƙarfin hali, har da Murmushin ta, tare da ƙoƙarin nuna bakomai.

Da daddare ya sayo gyaɗa da rake, ya kai wa ummi, duk cikin son ya ƙara rarrashin ta, ya daɗe yana sake kallon ɗakin da zata kwana a ciki, babu ko fitila a ɗakin, kuma ba za a rasa ƙwari masu cizo a ciki ba.

Ya kalli ummi ya ce "In sha Allah zan sayo miki fitila, sai ki din ga haskawa, sannan tun yamma ki din ga karkaÉ—e ko ina, ki tabattar babu wani abu a É—akin kan ki kwanta".

"To yaya na gode" ya jinjina mata kai ya fice.

Iya tana kallonsa daga tagar ɗakin ta, yanayin yadda yake shishshigewa ummi, abun ya fara ƙular da ita, dan haka tayi ƙwafa, tare da aniyar ɗaukar mataki a kansa.

Sai dai can ƙasan ranta, ta ji babu daɗi ganin kuɗin da aka yi, gashi ta riga ta saka an zane ummin, an rufeta a ɗaki kwana da wuni, ba tare da hakkinta ba. Haka nan abun ya din ga damunta, da safe ummi ta je har ɗaki ta gaisheta, da uniform za ta tafi makaranta.

"Kin karya ne zaki tafi makaranta?"

Ummi ta ce "A'a"

"Ki je wurin sa'adatu ta zuba miki kunu idan ta dama" ummi ta ɗan yi shiru ta tuna yadda sa'adatun ke haɗe rai idan ta je karɓar kunun.

Ummi ta ce "Na san idan na je ya ƙare"

Iya ta bankaÉ—a É—an tofinta, ta ciro naira É—ari, ta ajiye wa ummi ta ce "Gashi nan ki sai waina a hanya ki ci"

Ummi ta kalli kuɗin, tana wani irin murmushi da ita kaɗai ta san ma'anarsa, ta miƙe tsaye idonta fal hawaye ta ce "Ki bar shi iya, idan na dawo na ci abincin" tayi waje.

Tana jin Iya na zazzaga mata masifa, tana zaginta, amma tayi waje tana share hawaye.

"Ƴar ƙanƙanuwarki da ke, kin san munafunci, to kin yi wa kanki, halin uwar taki da nake ta gudu sai da ki ka kwaso shi? To ki ci kanki, da ke da mugun halin naki" Haka iya ta cigaba da sababi da kame-kamen borin kunya.

Ummi na tafe a hanya tana kuka, haka ta ƙarasa makaranta, suna ta shirye-shiryen shiga sakandare, sun kusa zana jarrabawar common entrance, shi ma kuɗin jarrabawar da ƙyar, ta biya, shi ma Naima ce ta zo gida, ta sa aka kirawo ta, take ta yi mata tambayoyi da ƙyar ta gaya mata batun kuɗin jarrabawar.

***
Manema na ta zuwar wa mariya, duk da ba fita take yi ba, amma mariya tayi burus, mahaifinta ya kaɗa ya raya, amma taƙi tsayar da kowa, da yayi mata zancen auren ma sai ta hau koke-koke.
Yayi ta rarrashin ta, a tunanin sa ko saboda tsohon mijinta ya sanya take jin ba zata sake yin aure ba, yayi nasihar, yayi rarrashin saboda kusan shekaru huÉ—u kenan rabonta da aure.
Kuma shekarun nan huÉ—u cif, ita ba mai lafiya ba ita ba mara lafiya ba.
Takura mata da maganar aure, ya sanya ta daina cin abinci ma, ta ƙara tsananta kaɗaice kanta, ga rashin barcci da ya sarƙafe ta, ta wuni ciwon kai dare yayi ta kasa bacci.

Tsananin ciwon kai ya sakata a gaba, gashi tayi shiru ba wanda ta gayawa, abu kamar wasa tun tana daurewa har ta kasa, ta din ga burgima a ƙasa tana wayyo kanta.

Sai a lokacin suka san ba ta da lafiya, aka kaita asibiti, sai dai babu cigaba, idan an kaita asibitin sai an tursasata shan magani, idan ta sha ɗin ma babu cigaba, wasu lokutan haka zata riƙe kanta tana ihu, tana kuka saboda rashin iya bacci, idan aka kaita asibiti sai dai su yi ta yi mata allurai.

Ƙarshe aka tura su ganin likitan ƙwaƙwalwa, hankalin mahaifin mariya ya tashi da ƴan uwanta, jin an tura su ɓangaren likitan ƙwaƙwalwa.

Likita ya duba ta sosai da sosai, ya basu shawarar a kula da ita sosai, saboda depression ne ya kamata, idam ba a kula da ita sosai ba, za a rasa hankalinta gaba É—aya.

Karo na farko da iyalan su mariya suka ji mahaifinsu yayi wa wani ɗan adam Allah ya isa, wanda sai da ya zubar da hawaye, yana matuƙar tausaya wa mariya, dan haka bai gaza ba, ya sake tashin yaya magaji, tare da Maryam, ya ce su je su bawa uwar mijin mariya haƙuri, ko sau ɗaya ta bayar da ummi, ta zo ta kwana biyu tare da mariya, ko a samu hankalinta ya kwanta.

Yaya magaji ya ce "Baba, ka san matar nan ba zata bayar da yarinyar nan ba, sai dai a tafi da mariyar, ta je ta ganta mu dawo"

Maryam ta ce "A hakan zamu tafi da ita? Ba zai yiwu ba ai, kana kallon abun da take yi, ai salon ta sake jin daÉ—i ne, dan matar nan ba mutunci ne da ita ba, kuma muddin aka bawa mariya ummi, ba zata bari a sake rabata da ita ba, a ganina kawai mu mayar da hankali a kan nema mata lafiya"

Yaya magaji ya ce "Duk da haka, zan jarraba zuwa, duk da na san ba zamu wanyeta ƙalau ba, amma zan jarraba zuwa na ga yarinyar ma daga nan, Allah sarki ummi, na san yanzu ta yi wayo sosai.

"Zata shekara goma zuwa sha É—aya fa yanzu, ai ta zama budurwa"

Suka bar maganar a kan cewa, yaya magaji zai je ya gano ummi, idan ya ga fuska ya sako zancen tahowa da ummi.

Ummi ta daina zuwa É—akin iya idan ba dole ba, saboda gudun kar ace ta yi wani abun, kullum cikin itace nan da buhhunan hatsi take kwana.
Tsabar daka kuwa hannunta duk yayi kanta, yayi ta É—urar ruwa yana fashewa, saboda tana da taushin fata sosai.
Chapter 20 · 0% Book details