← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 134

Sashe 47

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kawu yahaya yayi rawar gani, ya yi wa inteesar kaya na kece raini, ya so ace ta fara makaranta kan yayi mata aure, amma ta dage soyayya ta rufe mata ido, ta ce ita fa aure take so, dan haka ba yadda ya iya ya ƙyale ta.

Sagir ya danƙaro mata uban kayan lefe, kaya ba na wasa ba, ya ciko akwatuna da kaya, sai iyayi take tana rawar kai.

Albarkacin auren inteesar, a wannan karon da kawu yahaya ya yi mata ɗinki, farida ba ta ƙwace ba, har da sabon takalmi, farida kuma ta bata tsohon mayafi, kalar kayan.

Ranar party, farida ta ce ta zauna a gida, ta kula da baƙi masu shige da fice, kuma ta tsaya a kan girke-girken da za ayi.

Ummi ta zage ana can ana party, tana gida suna aikin girki, dan ita ta jagoranci aikin abincin bikin.

Ranar wuni ya kama ranar da za'ayi É—aurin aure, dan haka da wuri motoci suka kawo Æ´an gagarawa.
Su Idris da babarsa, su magaji kafatanin ahalin Iya.

Lokacin ummi ba ta gidan, suna can tana ta hidima da ƙawayen inteesar, ana yi wa inteesar kwalliya.

Ummi ta yi wanka, ta yi wa noor, ta saka kayan ankonta da ita da noor.

Sai da inteesar ta kalli ummi ganinta babu mayafi, dan zata iya ƙirga rabonta da ta ga ummi babu hijjabi.

Tayi ture ka ga tsiya, ta kanannaɗe gashinta a ƙeyarta, ɗaurin ya zauna cas a kanta, ga ɗinkin ma dai-dai jikinta.

Ta shafa man leɓe, ta yafa mayafinta a kanta, ta rufe jikinta sosai, ta kama hannun noor, suka fice.

Wani irin farinciki ya kama ummi, ganin Æ´an gida gaba É—aya sun zo, dan rabonta da su tun da ta baro gagarawa.

Duk bin ummi suka yi da kallo, yadda ta girma ta zama budurwa.

Cikin su ummi ta shiga tana gaishe su, Iya sai wani hura hanci take yi.

Ta ce "Ina yaya magaji?"

Sa'adatu ta ce "Sun tafi wurin É—aurin aure".

Ummi ta karrama su da abinci, dan matar gidan ba ta ta su take yi ba, ta kai su É—akinta, ta yi ta É—awainiya da su.
Bayan azahar su Hashim suka dawo daga wurin ɗaurin aure, ummi baki yaƙi rufuwa saboda duk ƴan uwan mahaifinta sun zo.
ÆŠaya bayan É—aya ta din ga gaishe su, suna mamakin yadda ta girma, ta zama cikakkiyar mace, sai dai ko kusa bata kalli in da Idris yake ba.

Farida sai bin ummi take yi da kallo, dan ba ta taɓa tsayawa ta kalli ummi sosai cikakken kallo ba sai yau, rashin gyara ne ke ƙara munanta ummi, idan ka kalleta sau ɗaya sai ka sake kallonta, mussaman yadda take kokowa da mayafin, kasancewar ita ba ma'abociyar ta'amalli da shi ba ne ba.

kasancewar hashim shi ne mutumin ummi, can harabar gidan suka koma, suna ta hira.

Ya dubeta ya ce "Ummi, kawu yayi miki magana kuwa a kan batun nemo mamanki?"

Cikin sauri ta ce "A'a, ya ake ciki?"

"Subhanallah, ya ce dai kar na kuskura na gaya miki saboda wani dalilinsa, amma dai idan bai ganta ba yana daf".

"Ya salam, bai gaya mini ba, ko maganar zan yi masa?"

"A'a, dan ya yi mini kashedin kar na gaya miki, ki kwantar da hankalinki duk abu zai haÉ—aku".

Cikin karaya ta ce "Yaushe hankalina zai kwanta, tana raye amma rabona da ita kusan shekara goma sha, ina son ganinta".

Idiris kuwa wani abu ne ya din ga yi masa zillo a maƙogwaronsa, ganin ummi tare da Hashim, gashi ta gayar da kowa, amma ko sashin in da yake ba ta kalla ba, balle ta gaishe shi.
Kasa daurewa yayi, ya nufi in da suke zaune.

Sai dai ummi na hango shi, ta miƙe tsaye ba tare da ta gama maganar da take yi da Hashim ba.

Cikin zafin nama ya sha gabanta, ya kalleta ya ce "Ina zaki je? Saboda wulaƙanci ki ka gaida kowa baki iya gaisheni ba, kuma na taho da ki ka ga nan zan zo, shine ki ka tashi".

Cikin ƙwayar idon Idris ta kalla, wani abu mai kama da wuta yana zafi a ƙirjinta.

Tuni idanunta suka tara hawaye ta ce "Cikin abun da bana ƙaunar sake gani a nan duniya har da lahira, har da fuskarka, ka matsa ka bani hanya, ko kuma in yi maka abun da baka taɓa zato ba!"

Whats app only please 🙏
Ayshercool.
08081012143
  *CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P21

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books É—ina, da free pages duk akwai a kan watpad account É—ina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

21

Mamaki ne ya cika shi, har sai da ya bayyana a kan fuskarsa, bai taɓa tunanin ummi za ta iya furta abun da ta gaya masa ba, saboda tun fil azal tamkar sokuwa take ba ta da wani karsashi balle ta yi faɗa.

Bai gama nazarin ba, ta angije shi tayi wucewarta tana tsaki, abubuwan da suka faru a baya, suna sake dawo mata tamkar yanzu suke faruwa.

Ƙarshen cin mutunci da tozarci yayi mata a garin nan, wanda yana daga dalilan da ya sanya ba ta ƙaunar sake zuwa gagarawa, haryanzu baƙin ciki da mugun tabon da take da shi a garin, yana damunta.

Dan har cikin zuciyarta tana fatan a gidan duniya, Allah ya yi wa Idiris abun da ya yi mata kafin ya koma ga Allah, ba ta sani ba ko a gaba ta iya yafe masa, amma har zuwa wannan lokacin, ba ta ji alamar manta abun da yayi mata ba, balle ta yafe masa.

Ranar da ya fara kwana a É—akinta, ya korota waje, ta kwana cir a tsaye ruwa yana dukanta, saboda mugunta da zalunci.

Tayi iya ƙoƙarin ta wurin danne hawayen da ke ta ƙoƙarin zubo mata, ana ta hotuna, angon inteesar sagir, da kansa ya ce ummi ta zo ayi musu hotuna.

Idiris ya jinjina kai, tare da tabattarwa da kansa zaman birni, da kuma zuwa jami'a ne ya sanya ummi lalacewa, domin kuwa an ce dama Æ´an matan jami'a ba su da mutunci lalacewa suke yi.

Duk in da ummi tayi sai ya bita da kallo, tamkar wani shashasha, hindu da yake yi wa kallon wayayyiya kyakykyawa, yanzu duk ta tararraɓe, haihuwa uku tayi, har da waccan mai sunan Iyan, ƙirjints da yake ɗaukar hankalinsa, duk sun zube, kullum daga ciki sai shayarwa.

Amma yanzu ummi komai nata a tsaye kyam, dai-dai da jikinta, duk da tana ta rufe jikin nata da mayafi.

Bayan la'asar suka ce zasu yafi, dan ba su zo da niyyar kwana ba dama, saboda sanin halin farida.

Duk lalacewar naka naka ne, ummi ta ji daÉ—in zuwansu sosai da sosai, tayi ta yi musu fatan alkhairi har suka tafi.

Idiris kuwa kamar maye, saboda azabar kallo, har suka É—auki hanya suka tafi.

Kallo ɗaya zaka yi wa rahama da yaronta, ka san ba a kwanciyar hankali take ba, ga dai kuɗi miji yana da shi, amma yarkace-yarkace hak take, dan hatta kayan sawa wasu lokutan farida ke bata ko ta sayawa ɗan, duk wannan ƙafafar da ikon babu shi, duk ta zama so silent.

Taro ya watse, aka kai amarya, ummi kuma ta sake cin uban aikin gyaran gida, ranar monday kuma ta tafi makaranta.

Gaba ɗaya jikinta a mace yake, da ƙyar take tafiya ma duk jikinta ciwo, saboda azabar aikin da ta sha, ba ta samu damar hutawa ba, a haka a tafe har gajiyar ta ware.

Karatun ummi yayi nisa, kuma haryanzu ba a samu wanda ya doke point ɗin ta ba, duk da ba ta fasa fuskantar ƙalubale ba.

Dan haryanzu farida da kausar ke cin ƙaniyarta.

***
Tana zaune ta duƙufa tana ta aikin shirin dutse, ɗanlami yayi masa jagora har cikin ɗakin da take zaune.
Ɗakin tsaf da shi, sai ƙamshin turare yake yi, kai ba ka ce mara lafiya ce a ɗakin ba.
Ta É—aga kai ta kalleshi, ta sunkuyar da kanta ta cigaba da aikin gabanta.

Ya ɗan ƙare mata kallo, shekaru sun ɗan ja, ta girma yanzu, amma tsaf da ita, tana samun kyakywar kulawa.

Ya dubi É—anlami ya ce "ÆŠan uwa, kuma a haka ba ta da lafiya?"
Chapter 47 · 0% Book details