← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 134

Sashe 34

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi ba ta san abun da ake ciki ba, tana can tana jinyar cikinta da suka ƙona da dutsen guga.

Ta zauna ta yi shiru tana ta tunanin, me ta aikata da ya sanya kowa ba ya son ta ji daÉ—i, kowa babban burinsa shi ne ya ga ya cutar da ita ta yi kuka?

Ta É—auki vasaline ta shafawa wurin, duk da haka sai da ya fara É—urar ruwa, duk fatar cikin ta tashi.

***
Idiris a tunaninsa tafiyar ummi, shi ne samun sassauci a gare shi, ya yar da ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda.

Hashim kuma Iya ta sako shi gaba da cin mutunci, ko gaisuwarsa ta daina amsawa, saboda haushin gayawa kawu yahaya abun da ake ciki da yayi, ya sanya yahayan yana yi musu kallon azzalumai.

Idiris ya lallaɓa ya cigaba da zuwa wurin hindu, yana son ya hilace ta su aikata alfasha, tun da iyayenta sun ƙi ya aureta.

Gulmace-gulmace suka din ga yawo, a kan azabtarwar da Iya ta yi wa ummi, da wanda idris ya yi wa ummin, tare da ƙoƙarin bankaɗa asirin dalilin da ya sanya aka fasa auren idiris da hindu, ana ta zaginsu a unguwa, aure wata ɗaya ya mutu.

Haka nan sai ummi ta din ga yi wa Idris gizo, idan ya je gidan da suka zauna.

Ko kuma yayi ta mafarkinta tana yi masa mugun kallo tana kuka. Gashi duk wannan abun da ya faru, ya kasa daina jin sha'awar ummi, ya kuma kasa manta yadda jikinta ke da matuƙar taushi kamar auduga.

Tun da yake leƙe-leƙnsa, bai taɓa taɓa mace mai laushin fatar ummi ba, gashi dai ko man shafawar kirki ba ta da shi, amma fatarta har wani irin santsi take yi.

Ya din ga tuhumar kansa, da ganin wautar sa na kasa daurewa ya sauke abun da yake damunsa game da ummin kan su rabu, amma da ya tuna annakiyar dauÉ—ar da ke jikinta, da kuma warin da take yi sai yayi tsaki.

A rashin ummi ya cigaba da ƙoƙarin hilatar hindu, yayi lalata da ita, hindu yarinya ce ƴar shekara goma sha shida, gidan su suna da tarbiyya sosai, dan haka sai wahalar da Idiris take, taƙi bashi haɗin kai, sai dai tana matuƙar ƙaunar idiris.

***
Likitoci suka rufu a kan farida, ana ta ƙoƙarin ceto ranta, sai dai jini yaƙi tsayawa, ƙarshe aka ce tiyata za a shiga da ita da gaggawa a cire mata cikin, dan ta fara jijjiga ga jini ya ɓalle.

A daren aka shiga da ita tiyata, aka ciro Æ´a mace, sai dai ba ta san in da kanta yake ba, har aka fito da ita.

Ita kanta yarinyar taƙi yin kuka, aka yi ta fama, sai dai tayi kaɗan tayi shiru, ga rashin isashiyar oxygen a jikinta sai da aka saka mata oxygen.

Rahama ta din ga kuka, tare da É—ora zargin hakan a kan ummi, sai dai ta yi shiru ba ta gaya wa baban su Abdul abun da ya faru ba.

Abdul kuwa a gida aka bar shi, ya kasa zaune ya kasa tsaye, mussaman yadda ya kasa manta ganin jini na zuba a jikin.

Ummi bacci sai ɓarawo ya kwasheta, shi ma a rigingine ta kwana.

Da asuba ta tashi tayi salla, fatar cikinta duk ta ɗaga tayi wani iri, saboda ƙuna.

Bayan ta idar da sallar, ta lallaɓa ta fito falon, ta tarar da wurin duk jini, ga kayan gugar duk a watse a wurin, tsaf ta gyara wurin ta kwashe kayan gugar, ta shiga kitchen, ta ɗora ruwan shayi, sai lallaɓa jikinta take yi, saboda raɗaɗin da take ji a cikinta.

Ta sake fitowa falo, ta tarar da Abdul a tsaye yana kallonta.

Ta kalleshi ta ce "Yaya Abdul".

"Na'am, ya jikin wurin ya ƙone?"

Ta ce "Eh, amma ba sosai ba".

Ya ce "Maama fa a asibiti ta kwana"

Zaro ido ummi tayi ta ce "Meya sameta?".

"FaÉ—uwa tayi" yayi maganar cikin damuwa.

Sai a lokacin ummi ta tuna taga farida ta zame ta faÉ—i, ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, to yanzu ya jikinta?".

"Nima ban sani ba, tun da suka tafi basu dawo ba".

Ummi ta ce "Allah ya sa tana lafiya".

Ya amsa da amin.

Suna tsaye suna jajantawa, sai ga Abba yayi sallama, duk suka zura masa ido suna yi masa sannu da zuwa.

"An yi wa mamanku aiki, an ciro baby girl, sai dai dukkannin su, they are under special care, duk basu da lafiya"

Ummi ta ce "Subhanallah, Allah ya basu lafiya".

Ya amsa da "Amin, ummina na san kin yi breakfast, ki zuba wani a flask a kai musu asibiti, ku shirya na ajiye ku a makaranta, ina su kausar?"

"Ba su tashi ba"
"Kamar yaya, ƙarfe bakwai saura, ba zasu makaranta bane?" A fusace ya nufi ɗakinsu, ya taso su da bulala.

Ƙarshe dai sai da suka makara, jin mamansu na asibiti, ya sanya suka din ga kuka, haka ya kai su makaranta ya wuce asibiti.

Gumin da ummi take ta yi, ya din ga taɓa wurin ƙunar nan, ga kuma rigar makaranta, hakan ba ƙaramin takurata yayi ba.

Sai dai duk da abun da farida da ƙamwarta suka yi mata, tunaninta yana kan yaya jin faridan yake.

Kasancewar rahama ce a can asibiti tare da farida, sai ya zamana kusan kula da ragamar gidan yana hannun ummi, kai ba ka ce babu mace a gidan ba, duk aikin gida ita take yi, har kawunta sai da ya yabawa ƙoƙarin ta tare da jinjina mata, dan hatta abincin da za a kai asibiti ita take dafawa.

Gefe guda Abdul ne yake takawa su intee burki, dan tana yi musu wahala amma ba sa gani, dan sai suka tsiri cewa ai anty rahama ta ce musu, ummi ce ta saka mamansu ta faɗi, su yi ta yi mata rashin mutunci da wulaƙanci.

Kwanan farida biyu a asibiti, aka samo kanta da ƙyar, kawu yahaya ya ɗauki su ummi ya tafi da su asibitin dubata.

Sai dai yanayin kallon da ƴan uwan farida ke yi mata, ya sanya ta sha jinin jikinta, dan ko sannun da tayi wa faridan ba ta amsa ba. Tana kwance jaririyar a kusa da ita, ana ƙara mata jini. Sai dai kasancewar babansu Abdul yana wurin, ba su iya ce wa ummi komai ba.

Ummi fa ƙuna ta din ga jagwalewa, ga ƙaiƙayi tana yi mata, ta tuna ta taɓa ƙonewa a ƙafarta lokacin tana ƙauye, na'ima ta din ga shafa mata zuma, dan haka ta cewa baban su Abdul, ya sammata zumar da yake shan shayi.

Yayi murmushi ya ce "Zumar da gata nan kaya guda, ai ba sai kin tambayeni ba ummana" ta samu abu ta tsiyaya take amfani da ita a ƙunar, dan har wurin cibiyarta ta ƙone.

Kwanan farida biyar a asibiti aka sallamo su, babu tsammani ummi ta dawo daga makarantar boko ta dawo ta tarar an cika gidan.

Ta ƙarasa falon ta durƙusa tana gaishe su, sai dai basu amsa ba, rahama ta janyo hijjabinta har tsakiyar falon ta ce "Kun ganta nan azzaluma, ita ta kusa kashe anty farida, ita ta kayar da ita"

"To ai da farida cewa tayi mai aikinta ce".

"Ba Æ´ar aiki ba ce ba, Æ´ar wan maigidan nan ce".

Ƙanwar babansu farida ta ce "Kuma shi babu matakin da ya ɗauka?"

Farida na daga kwance ta ce "Wane matakin zai É—auka, kin ga faman da nayi a kan ba zan zauna da ita ba ya dage, ni kuwa na samu Æ´ar aiki"

"Aikuwa idan baki yi hankali ba ta kashe ki wataran".

Ummi tayi shiru ta sunkuyar da kai, wata yayar su ta dunƙule hannu, ta ɗirka mata duka a tsakiyar ka ta ce "Wallahi da kin kasheta, sai kin yi prison daga ke har ubanki".

Rahama ta ce "An ce ubanta ya mutu ai".

"Matsiyaciyar yarinya da ya bar wata tsiyar, da ba a ganki a nan ba, har ki ke ƙoƙarin kashe mana ƴa, ni wannan anya ma ba mayya bace ba, kalli ƙwayar idonta fa".

Wata a gefe tayi caraf ta ce "Wace iri ce? Turo mini ita nan, ai ni ina gane maye"

Matar ta ja ummi kamar tana jan shara, ta dungurarwa da É—aya matar ita, tuni ummi ta fara kuka, ga zafin duka ga na cin mutunci.

"Ke É—ago idonki na gani"

Ummi ta sunkuyar da kai ta kasa É—agowa.

"Ba zaki É—ago ba sai na mareki" ummi ta kasa ta sake fashewa da kuka.

Aikuwa matar nan babu tsoron Allah, ta sauke wa ummi yatsunta a fuska iya ƙarfinta, sai da ta hantsula gefe.

"Wallahi zata iya yiwuwa mayya ce, tun da ta kasa haɗa ido da ni, shegiya ga baƙi kamar ƴar maƙera".

Suka ciwa ummi mutunci son ransu saboda abun kunya, da yawansu zasu haifi ummi, amma kasancewar ba Æ´ar su ba ce ba, suka din ga muzanta ta suna aibata ta.

Tayi kukan da tun da aka kawota gidan ba ta yi irin sa ba, har ta fara tunanin ko roƙon kawu yahaya za ta yi, ya mayar da ita ƙauye.

Sai dai gabanta ya faɗi, da tuna irin azabar da ta sha a ƙauye, da sauri ta girgiza kanta, har da istigfari, ta fara ƙoƙarin auna zaman nan da na can wanne yafi sauƙi.

Duk zaluncin iya, ba ta taɓa ƙonata da wuta ba, illa iyaka duk laifin da tayi jikinta zai gaya mata.
Nan kuma duk rintsi, ko ba a bata abinci sau uku ba, ba zata kwana da yunwa ba, kuma tana da kayan makaranta da na sawa duk da babu yawa, kuma tana da takalmi da sauran abun da ba a rasa ba.

"Mama meyasa ba so na ne? Laifin me nayi, meyasa idona yake ba kalar na mutane ba? Duk abun da nayi mutane sai sun tsaneni, ko a gida ko a makaranta?" Tayi maganar tana ganin fuskar mariya a idonta, tana jin tamkar ta ga mamanta ta bayyana.

Tayi kuka ta gaji, ta duba sabulun wankanta ya ƙare, tayi wankan a haka, ta shirya islamiyya, ta fice ba tare da kowa ya sani ba.
Chapter 34 · 0% Book details