Sashe 96
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai dai dr. Ya aika Abdul, ya ce ya kai su tsohon gidansa, ya saka an gyara, a can za su zauna, su yi nasu taron bikin, saboda sanin halin farida.
A yammacin da suka zo, raihan ya zo, suka kuma gaisawa da su mama, kamar ya sace ummi, tana magana tana lumshe ido saboda azabar gajiya.
Ya ce "Madam, tun yanzu har kin gaji har haka?"
A É—an raunane ta ce "Ba zaka gane ba MD, a gajiye nake sosai wallahi"
"Kar ki damu, akwai kulawa ta mussaman jibi in Allah ya kaimu da zan baki" tayi masa shiru.
"Babyna am talking fa" taƙi kula shi.
Ya sake cewa "Ina fatan da ki ka je gagarawan babu wata damuwa? Kuma ba ku haÉ—u da tsohon mijinki ba?"
Ta ce "To meya kawo wannan maganar kuma?"
"Saboda ina kishinki fiye da yadda ki ke tunani, duk da É—an uwanki ne, ba zai sake saka ki a idonsa ba"
"Saboda me?"
"Saboda haka na ce" yayi maganar cikin isa, tare da tsareta da ido, sai da ta É—an sha jinin jikinta. Ta tura baki ba tare da ta ce masa komai ba.
Ya É—ora da cewa "Gobe in Allah ya kaimu da wuri mai yi miki kwalliya za ta zo, duk in da huÉ—u tayi, ki kammala shirinki, zamu zo É—aukar ki".
"Tom Allah ya kaimu"
"Gobe in Allah ya kaimu i yanzu, kin zama matar Muhammad, inyeee babyn ba" zolayar raihan ta yi yawa, sai da ya sakata murmushi tana rufe fuska.
Ya ce "Bari na tafi, ki je ki huta, ki ci abinci sosai da sosai" ta jinjina masa kai suka yi sallama.
Washegari da sassafe Æ´an gagarawa suka isa kano, sai dai babu Iya, dan cewa tayi ba zata je ba.
Ranar juma'a tun sassafe, su Yaya maryam suka je kafin kaya, sai dai sun riƙe baki da ganin gidan ummi, gida ya haɗu sosai da sosai, ya ƙawatu kai da gani ka san an kashewa gidan kuɗi ba kaɗan ba.
Ba ƙaramin murna ummi ta yi ba, ganin an zo da Nana, ƴan gagarawa a gidan dr. Suka sauka, su mama kuma suna ɗaya gidan.
Bayan sallar juma'a, aka É—aura auren Ummi da raihan, a kan sadaki naira dubu É—ari biyar.
An sha surutu shi ma a kan sadakin nan, mussaman Æ´an gagarawa, har da cewa dr. Zai aurar da ummi ga É—an yankan kai, tana bazawara ana wannan bushashasha haka a aurenta.
Manager yayi mamakin ganin wai raihan ne mijin da ummi za ta aura, dan ko da ya ga katin ma, bai kawo shi ne ba, dan Muhammad Muhammad Tahir aka saka a katin bikin.
Duk in da ummi ta yi, noor da Nana ne ke biye da ita, su ne ƙawayen nata, can gidan su raihan Hajiya ce take hidima da jama'ar da suke ta shiga suna fita.
Wani irin danƙareren leshi da raihan ya saya mata ta saka, ɗinkin doguwar riga, da mayafi, ba wani make up aka yi mata ba, komai dai-dai kalar fatarta.
Idan ba an gaya maka ba zaka ce mama ba ta da lafiya ba, ta sha kwalliya cikin atamfa ita ma, tayi kyau sosai da sosai.
Ƙarfe huɗu da rabi raihan ya aika motocin da zasu tafi da waɗanda zasu je walimar da za ayi.
Daga baya kuma motarsa ta je É—aukar ummi, ta yi kyau sosai da sosai, cikin tausaywa da soyayya yake kallon ummi.
Ta shiga cikin motar da sallama, tuni ƙamshin turaren ta ya cika motar, ta sunkuyar da kanta ta ce "Ina wuni?"
"My wife, legally sealed you now belongs to me Salma" yayi maganar yana riƙe hannunta.
Tayi murmushi ta ce "Ka rabani da headmaster ko...
Ba ta gama ba, ya riƙe hannunta da ƙarfi ya ce "Ki sake maganar wani a gabana ki gani, da kin aure shi in ba sai ya gaji ya sakar mini ke ba, idan na din ga sintiri a gidan ki har uwar ɗakinki" ƙunshe baki tayi tana dariya, haryanzu gani take kamar ba ita ba, wai raihan za ta aura, abun da mamaki.
Babu mutane da yawa a wurin, an ci an sha sosai, sai dai duk da mayafi ne a jikin ummi irin na amare, daga sama har ƙasa, tana ta rufe jikinta, amma sai da raihan ya ji wani abu a ransa na kishi.
Ana ta hotuna, a nan Æ´an gagarawa suka ga mariya, tsaf da ita kamar ba ita ta haifi ummi ba, tsaf da ita gashi ta yi kyau sosai da sosai, shekara sha takwas rabon da a haÉ—u.
Suka din ga gaisawa da facalolinta, ta kalli sa'adatu ta c "Ina Alhassan mai yi mini Albishir da mutuwar mijina?" Tayi tsuru-tsuru tana basar da zancen, dan ba su zaci ganinta a haka ba, sun É—auka hauka take yi tuburan.
Ana ƙoƙarin yin hoto, noor na ta ture Sagir, wai ya koma kusa da raihan shi ne ɗan uwansu, su kuma su ne ƴan uwan ummi, a kusa da ita za su tsaya.
Zuwa sallar isha'i aka tashi daga wurin, noor da Nana suka shige motar Salim, noor ta ce "Bawan Allah dan Allah ka mayar da mu mukaɗai gida, kar ka ɗauki kowa, motar daɗi" kallonsu yake yi, har gara Nana akwai ƙauyanci a tare da ita, amma ya lura da noor, tun a wurin bikin tana da rawar kawai sosai da sosai.
Ya kalli noor ya ce "Ke bana son surutu, ke ki shiga bayan mota, ke kuma dawo gaba" yayi maganar yana nuna Nana.
"A'a ka barmu mu zauna a baya daukkanmu"
"To ku nemi wani"
Noor ta ce "A'a yi haƙuri, Nana ki koma gaban" suna tafe suna ta surutu ita da Nana.
Nana tana magana tana fulatanci, Noor ta ce "Nana, Allah ya sa nima na auri irin yaya raihan, mai kyau kamarsa"
Sai da Salim ya waiwaya ya kalli noor, ba ya tunanin ko fitsarin kwance ta daina take zancen wani miji.
Suka yi ta surutu, ko gajiya ba sa yi, har ya kai su gida.
Washegari aka yi wunin biki, da isha'i aka kawo motocin É—aukar ummi, da mariya da yaya maryam da wasu daga Æ´an uwan su, suka tafi da ummi gidan farida, domin yi mata sallama.
Yaya maryam ta din ga yi wa farida godiya, saboda riƙe ummi da ta yi, sai wani cika take tana batsewa, ta zata za ta gan su ƴan ƙauye, sai dai ta ga sun sha dressing, sun yi kyau, tayi mamakin ganin babar ummi, ta ɗauka ita ma baƙa ce wuluk, amma ta ganta da haske kuma shar da ita.
Dressing ɗin da aka yi wa ummi, ta din ga kallo, ita kanta a ƙasan zuciyarta ta san son zuciya ne ke sanya suke ce wa ummi mummuna, tana da baƙi ne dai kawai amma ba wani muni.
Dr. Ya yi wa ummi nasiha sosai da sosai, ummi ta yi masa godiya tare da neman yafiyarsa, ya ce shi ba ta yi masa komai na laifi ba.
Ƙarfe tara na dare, aka kai ummi gidan raihan, dr. Da kansa ya kaita a motarsa bayan yi mata nasihohi masu ratsa jiki, mutane sun yi santin gidan nan sosai da sosai, dr. Sai da ya cika ko ina, kitchen ɗin ta kuma su yaya maryam sun yi rawar gani, ga uban kayan turaren wuta duk an yi mata, komai nata sai masha Allah.
Dangin mami da ta din ga ce musu ba ta da gata, sun É—auka ba za a zuba mata kayan kirki ba, su samu na gori, amma suka sha mamakin kayan da dr. Ya zuba mata.
Kowa ya watse, ummi idonta ko kuka ba ta yi ba, saboda ita a wurinta cigaba ta samu, ta bar wa farida gidanta, sai fatan Ubangiji Allah ya sassauta mata ƙalubalen gidan raihan.
Sai sha É—aya ya shigo, daga shi sai Salim da wasu mutum uku, da take kyautata zaton Æ´an uwansa ne, suma suka yi musu nasiha, tare da addu'a zaman lafiya, suka watse suka bar su.
Ya dawo ya tarar da ummi a zaune a in da ya bar ta, ya yi gyaran murya ya ce "Yaya" ta ɗago kai ta kalleshi yayi murmushi ya ce "Kin yi kyau fiye da kullum" ta sunkuyar da kanta ƙasa.
Ya zauna a kusa da ita, ya miÆ™a mata hannunsa ya ce "Æalle mini" jikinta na rawa ta É“alle masa maÉ“allan hannun rigarsa, ya cire babbar rigarsa, da ta cikin, ya shiga banÉ—aki yayi alwala, yayi mata umarnin yi ita ma.
Bayan sun yi salla raka'a biyu, raihan ya daÉ—e yana yi musu addu'a, bayan ya kammala kuma, ya din ga yi wa ummi nasiha.
"Salma, bayan gwagwarmaya daban-daban, Allah ya cika mini burina a kanki, ina da yaƙinin na kawo mace ta gari, kuma uwa ta gari ga ƴaƴana, ummi duk wani aure da nasa ƙalubale, amma in sha Allah, daga gareni babu ƙalubale, sai abun da ba a rasa ba, amma zaki yi haƙuri da wanda zaki fuskanta daga ƴan uwana, mu zama masu haƙuri da riƙe sirrin junanmu, kamar yadda na yi wa mama alƙawari, zan riƙe ki amana na kula da ke, in sha Allah zan yi iya yi na, Allah ya bamu zaman lafiya. Na san ba a za a rasa ɓacin rai a harkar auratayya ba, kin san halina wasu lokutan ina da zafi, amma ki zama mai yi mini uzuri, Ubangiji Allah ya bamu ikon kula da juna" ta amsa da Amin, ya tambayeta ko ta na da abun cewa ta ce masa a'a.
Duk yadda yayi da ita ta saki jiki ta ci abinci, ummi fafur taƙi, shi yayi ciye-ciyen sa.
Ita kuwa ummi wata irin fargaba da tsoro ne ya addabwa zuciyarta, abun da ya faru a aurenta na farko ne ya din ga ya dawo mata, tana ta fargaba da addu'ar kar ta sake cin karo da matsalar da ta faru a farko.
Ya fita daga ɗakin, ya dawo da wasu kaya a hannunsa, ya ce "Ƙaraso" yayi maganar yana yi mata nuni da hannunsa.
Ta tashi tana sinnewa ta ƙarasa, ya ɗaga mata wata doguwar rigar bacci, ja mai kyau, nasa kayan ma jajaye, ya ce "Ungo naki"