← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 134

Sashe 83

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Raihan, dan Allah idan a kaina ne, kar ka samu matsala da Æ´an gidanku, ahali sun fi komai daÉ—i, ni daga baya ka sanni, zaka iya canza ni, su kuwa fa, in dai nice babu komai zan fahimceka amma ahalinka na da muhimmanci a rayuwar ka, ni tsangwama da kyara na saba da su"

"Amma ba zaki dauwwama a cikin su ba, akwai hatsari mai girman gaske a rabani da ke, ko kin auri wani ba ni ba, ba zan iya rabuwa da ke ba, zan tafi bauci wataƙila zan shafe tsayin lokaci, amma zamu din ga waya in sha Allah, take care am going to miss you dear" yayi maganar yana shafar gefen fuskarta. Ya tashi ya fice.

Haka kurum gabanta ya tsananta faÉ—uwa, a duk lokacin da ya ce ko tayi aure ba zai iya rabuwa da ita ba, sai ita ma ta din ga jin irin haka a zuciyarta, kamar itama ba zata iya rabuwa da shi É—in ba.

Jikinta duk yayi sanyi, har ta kammala aiki ta tashi, bayan ta koma gida tana ta neman layukansa, amma shiru ba ta samunsa a wayar.

Sai washegari ya kirata da wata lambar daban, ya ce mata yana bauchi cikin ƙoshin lafiya, da wannan lambar za ta din ga kiransa.

Jin muryarsa wasai ya sanya ta cewa "To amma yanzu zaka dawo ko?"

"Ko zan dawo ba yanzu ba, kewarki ce kawai take damuna"

"Dan Allah ka dawo ka ji babban mutum, manya ba sa haka, idan laifi muka yi mutanen kano, tuba muke yi kar a hora mu da yi mana yaji, ka san menene zan dafa maka abinci mai daÉ—in gaske, na san abun da ya saka bar garin zuwa yanzu ka huce ai ko? Zan yi maka girki"

Raihan yayi dariya ya ce "Matar raihan, kirarin nan kawai ya ƙara sanyaya mini zuciya, kar ki saka na ɗaukko mota na taho mana. Ke dai ki yi ta addu'a kamar yadda na ce miki kin ji ko?"

"To shikenan, amma dai ka yi tunani a kan lamarin nan".

Can gida kuwa Alhaji Tahir ya saka mami a gaba da masifa, tare da cewa duk in da É—an sa yake sai ta fita ta nemo shi, dan ba a samun sa a waya, baya gida kuma baya office.

Abu kamar wasa, hankalin mami ma ya tashi, ba ta yi zaton raihan zai yi haka ba.

kwana kusan biyar, babu raihan babu dalilinsa.

Dr. Ya samu ummi ya ce mata ta shirya kayanta, washegari za su yi tafiya ta kwanaki uku, ta sanar a wurin aikinta.

Ummi tayi ta mamakin, ina za su je haka afujajan babu cikekken shiri babu komai.

Ba ta matsa masa da tambaya ba, ta shirya kayan kamar yadda ya umarce ta.

Mami kuwa, Anty rakiya ta bata shawarar ta je har gida ta ci mutuncin ummi, kuma ta tursasata ta gaya mata in da raihan yake, dan ba zata kasa sani ba.

Alhaji Tahir ya shigo a fusace ya ce "Kin yi naki role É—in, barkana tun da na san in da É—a na yake, amma bari na gaya miki wani abu, idan har kin cigaba da dagewa ba za ayi auren nan ba, to ki tabattar da zan kawo yarinyar nan matsayin matata ta uku, dan ba zaki zubar mini da mutunci a idon duniya ba"

Gabanta ne yayi wata irin mummunar faÉ—uwa, wayarta ta fara ringing, cikin rawar jiki ta É—aga. Saboda kura ta san gidan mai babban sanda bijirewa É—aga wayar ka iya jefata cikin matsala.

"Bilki, ashe baki da mutunci baki da hankali? Ashe wayewar ta ki ta ƙarya ce, saboda wulaƙanci da rashin mutunci ke da ba a aure, da zamu bari Tahir ya aureki ne? Ke kin san auren zumunta muke yi, da matarsa ƴar uwassa tana son shi yana son ta, ya auro ki, mu a cikinmu waye ya hanakk zaman lafiya? Saboda rashin kunya yaro ya kawo mace yana so ki ce a'a, saboda wulaƙanci idan shima ya faɗa shaye-shayen ki ce me? Bar ganin ke ki ka haifi raihan, wallahi ba zamu lamunci son zuciya ba, ko tsohuwa ya ce yana so, zamu bashi goyon baya, ba dan Allah ya sa ya taho nan bauchin wurin mu ba, wani wurin yayi ba, to ahir ɗinki wallahi idan ba haka ba da ni ki ke zancen, kuma bauchi ya zo kenan, ku nemi wanda zai riƙe muku kasuwancin naku, tun da kin hana shi auren".

Cikin tsuma Mami ta ce "Dan Allah Hajiya Aisha ki yi haƙuri, in sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba"

"Oho miki ta cigaba da faruwar ma, kin ce ya fasa aure, ai ke uwa ce yayi biyayya ya janye, amma ya ce a gaya miki, shi da aure har abada, sai kuma ki shirya idan ya kawo miki ɗan gaba da fatiha ki karɓa ki riƙe tun da ba ki da hankali" ta kaste wayar.

What's app only please, masu so daga farko su yi joining channel É—in nan.
08081012143

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books É—ina, da free pages duk akwai a kan watpad account É—ina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

  *CUTARWA*

*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

FOLLOW AND SHARE
AYSHERCOOL
08081012143

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

Wani irin gumi ne ya dinga gangaro wa mami, duk da yadda sanyin AC ke ratsa ko ina a falon.

Raihan ƙararta ya je ya kai wa wannan masifaffiyar yar uban nasa kenan? tuno maganar Alhaji Tahir, da tuni ya bar falon da yayi ya sanya ta jin wata muguwar gudawa, saboda yadda cikinta ya murɗa mata.

Afujajan ta fita ta nufi sashinsa, har da tuntuɓe.

"Wallahi Baka isa ka gaya mini maganar da zata hana ni sukuni ka fice ka bar ni ba, kai yanzu saboda abun kunya goÉ—ai-goÉ—ai da kai sai ka auri yarinyar da É—an ka ya ce yana so?"

Alhaji Tahir ya ce "In dai haka shi ne mafita a gareni me zai hana? Ku mata ku kuka san wani abun kunya, mu maza abu in dai mu yayi mana ba ruwanmu da abun kunya, kuma ina sake tunatar da ke, bana magana biyu, wallahi da gaske nake, sai dai idan na aureta wanda ba zai iya zama da ni ba ya ƙara gaba, shawara ta rage ga mai shiga shiga rijiya" ya ƙarasa maganar tare da ɗaukar wayarsa ya fita.

Kamar wadda ta zare, haka ta sake kwasa har da gudu, ta tafi ta kira Anty rakiya a waya.

Rakiya na É—agawa mami ta fashe da kuka, "Anty rakiya na shiga uku na lalace"

"Wane irin kin shiga uku, meyafaru ba yanzu muka gama waya lafiya ba?"

"Ashe raihan bauchi ya tafi, ya je ya haÉ—o ni da wannan masifaffiyar matar yayar babansa, kin ga yadda ta ci mini mutunci kuwa? shi kuma Alhaji wai idan ban bari an yi auren ba, wai shi zai aureta ya kawota gidan nan a matsayin matarsa"

Anty Rakiya ta ce "Kai haba, dalla rabu da shi, barazana ce kar ki fasa wallahi, kar ki yadda a kawo miki bazawara a matsayin sirika"

"Anty Rakiya waye ya gaya miki Alhaji Tahir yana barazana ne? Magana É—aya yake yi ko ta yi maka daÉ—i, ko kuma akasin haka, har rantsuwa yayi mini, na shiga uku, kuma wai raihan ya ajiye aikin nan ina na kama?"

Anty Rakiya ta ce "Taɓ, lallai raihan ba shi da hankali, to wallahi idan ki ka zuba masa ido, haka zai aurota ya fi ƙarfinki, tun da har ya san yayi miki yaji, ki kira shi ki ce lallai ya dawo dan ubansa"
Chapter 83 · 0% Book details