← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 134

Sashe 81

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kawu Ilyasu ya ce "Ai dama kar ku ga an rufe ku ne, ku kallemu a matsayin mutanen banza, shiyasa na bayyana komai ko ba gaskiya ba? Kar ku zo a saka yaro yayi ta kashe kuɗi, tun da an ce shi bai taɓa aure ba, kar ya narka dukiya a auren bazawara ya zata budurwa ce, amma dubu ɗari biyar sun yi yawa a kuɗin auren bazawara, kar a cutar da shi"

Alhaji Tahir ya gyara zamansa ya kalli kawu Ilyasu ya ce "Ka san da wa ka ke magana kuwa? Bana alfahari da fariya, amma ko yafi haka ya bayar in kawo zan kawo, ba bazawara ba ko da tsohuwa ce kuwa, ka kuwa san wa Æ´ar ku zata aura ne? Da alama dr. ShikaÉ—ai yayi binciken nan yakamata ya faÉ—aÉ—a muku bayanin waye Muhammad Raihan Tahir, zuriyarmu mun gaji yi wa iyali hidima. Ai ni da raihan ya ce mini mahaifiyar ta Æ´ar maiduguri ce, na yi zaton zaku yanka mana sadaki ne da sisin gwal, dan an ce auren Æ´aÆ´anku sai jarumi" yayi maganar cikin barkwanci.

Dr. Da kunya kamar ya nutse ya ce "Ai kamar yadda na gaya maka, mu Æ´an jigawa ne gagarawa, mahaifiyarta ce Æ´ar maiduguri"

"Allah sarki, to ace wa sirikata ina nan ina jiran turaren wuta, dan mutanen barno akwai ƙamshi"

Kawu Ilyasu ya ce "Kuma akwai ta'addanci da surkulle ba, ai da yake ma babartata ba wanda ya san a in da take yanzu, shekarun baya aka ce mana ta haukace ma"

Alhaji Tahir ya yi masa banza ya ce "Yanzu kun amince a kan watanni huÉ—un?"

Dr. Ya ce "Ubangiji Allah ya nuna mana, ya sa zamu gani"

Suka kammala, suka tashi suka tafi, suna tafiya dr. Ya dirar wa Iliyasu da bala'i.

"Wane irin mutum ne kai mara mutunci, ka ke tozarta yarinya a gaban sirikanta, wannan ai ba daidai bane ba"

"A'a yaya yahaya, haka shi ne kankaro mutuncinmu da kimar mu, haka kurum su gano daga baya, su ga mun zalunce su ai gara mu faÉ—a"

Kawu Saminu ya ce "To yanzu da ka faÉ—a É—in me ya sauya?"

Cikin takaici kawu yahaya ya ce "Auren na ta na fari, ba a gabanku Idiris ya saketa ba, ko kusantarta bai taɓa yi ba ya ce saboda larurar da take fama, ya tozarta ta da bakinsa ya faɗa, da na taho da ummi daga gagarawa na kaita asibiti a kan larurar da take damunta, shi ma da bakinta ta tabattar babu mu'amalar aure a tsakanin ta da idiris ba ta da iddarsa.
Idan ka tona wa ummi asiri meye ribar ka? Sigar yadda ka faɗi maganar salon tozarci ne kawai, In da na gode wa Allah mutumin wayayye ne, kuma magana ake ta zunzurutun ilimi, kuma wannan maganar duk mun yi ta da shi, na gaya masa ummi bazawara ce ta taɓa yin aure, ya ce mini in dai ɗan sa yana son ta, shi ba shi da matsala da ita, kuma ɗaukakace kuna raye sai ummi ta yi ta, dan yaron manyan mutane ne, in sha Allah sai yarinyar nan ta huta.

Ya ciri dubu hamsin a aljihunsa ya ce "Ga wannan, ku bawa Iya dubu goma, ku É—au goma-goma sauran ku rabawa dangi an saka ranar ummi"

Kawu Saminu ya ce "Amma yaya, a bayar da kuÉ—i har dubu É—ari biyar amma ka bamu dubu hamsin, a duba lamarin nan mana"

"Da nake raye na yi auren ƴa ta nawa ku ka bani gudunmawa? Sai ummi da ba ta da gata sai Allah sai ni, yarinyar da ku ka son tozartawa zan baku kuɗin aurenta, a kuɗina ma na baku dubu hamsin ɗin nan, kuɗin aurenta sisi ba zan taɓa ba, kayan ɗaki zan yi mata na alfarma" Haka suka rabu baran-baran dutse a hannun riga.

Suna tafe a hanya kawu Saminu ya ce "Ilyasu meyasa ka yi haka? Kai ina ruwanka?"

Ilyasu ya yi tsaki ya ce "A gidanka ko a gidana meyasa ba a samu irin wannan ba, fin ƴaƴanmu kyau ta yi, kaf sirikanmu babu wani mai maiƙo, amma kalli ya kawota birni zai aura mata mai kuɗi, su haɗu su yi ta ci Allah ya isa wallahi"

"To yanzu da wa ka ke Allah ya isan?"

"Kai ba zaka gane ba, yarinyar nan idan ta samu daula, za ta iya aikata rashin mutunci, ina laifin a samo mata miji dai-dai ita, wai kuɗin aire kawai dubu ɗari biyar, wai ya zata sisin gwal za a yanke musu, a'a sisin uwarsa, sai wani baza babbar riga yake wai shi ga attajiri, shi kuma wannan banzan sai ƙaryar turanci, ƴaƴan mu ba su samu haka ba, sai wannan galmashurar yarinyar" har suka isa gagarawa bakin Ilyasu bai rufu ba yana bala'i.

Su Alhaji Tahir ma suna tafe, abokinsa Alhaji Sabo yake cewa "Tahir mutumin nan fa da gaskiyar sa, yaya za ayi ka bari raihan ya auri bazawara kuma ya kashe mata wannan kuÉ—in haka?"

Alhaji Tahir ya ce "Saboda ɗa na kowa ne, kuma dukiya ɗazu ce, muddin na bari yayi abun da mutuncinmu zai zube tun yanzu, to raihan ba zai taɓa kima a idonta ba, ina fatan ko bayan raina, nima Allah ya kawo masu kula da bayana, labarin nagartar yarinyar da na ji, ko tsohuwa ce ta kai a bayar da hakan"

Ƙanin Alhaji Tahir ya ce "Gaskiya ne wannan, Allah ya wuce mana gaba, amma daga yadda wannan kawun nata yake zaƙewa kawai na ji ta bani tausayi, Allah ya sanya musu albarka"

Suka amsa da Amin.

Tsananin ɓacin rai da farinciki, ya sanya dr. Gaya wa ummi abun da kawu Ilyasu ya yi, a ƙa'ida farida yakamata yayi zancen ya ji sanyi, amma ya san sai ta sake yin wani abun da zai tunzura shi, dan haka ya zaunar da ummi yana gaya mata, tare da nuna mata kuɗin, ya tambaye ta wani irin kaya take so.

Jiki a sanyaye ta ce "Duk abun da ka yi mini na gode kawu, Allah ya saka da alkhairi ya jiƙan magabata"

Ya amsa da "Amin ummana, ki yi ta addu'a kina haƙuri kin ji ko? Nasara ba ta zuwar wa bawa daga kwance babu jarrabawa"ta jinjina masa kai ta ce "In sha Allah"

Iya tayi mamakin jin abun da kawu Ilya suka ce mata an kai wa ummi, ta riƙe baki ta ce "Shi kuwa wani asarren ne zai kwashi wannan mummunar yarinyar mara fasali, har da kashe mata maƙudan kuɗi haka?"

Kawu Ilyasu ya ce "Oho musu, kuma yaron ma wai bai taɓa aure ba, amma an cuce shi gaskiya"

"Ai ba zai wuce yahaya shi yake ƙuƙƙula wannan abubuwan ba, kuma zai zo ya sameni har in da nake"

Magana ta cika gagarawa, cewar ummi ta samu wani hamshaƙin attajiri a kano za ta aura, kuɗin aurenta kawai naira dubu ɗari biyar.

Aka din ga surutu da yayata zance, har da masu zuwa yi wa iya Allah ya sanya alkhairi.

Kasancewar Alhaji Sabo da suka kai wa raihan kuɗi, matarsa ƙawar mami ce sosai da sosai, bayan gama bawa matarsa labarin abun da ya faru, ta ɗauki waya tana yi wa mami mitar duk ga ƴaƴan su amma raihan ya tsallaka waje zai auri bazawara.

Mami ba ta gane zancen ba, sai da ta yi mata dalla-dalla, hakan ya ƙara tunzura mami, ta tafi sashin Alhaji kamar za ta kama da wuta.

"Alhaji Tahir" ta kira sunansa kai tsaye.

"Na'am Bilkisu ya aka yi ne?"

"Wallahi raihan ba zai auri bazawara ba, ba zai yiwu ba, wai ka san yarinyar da zai aura bazawara ce?"

"Na sani, ba shi ya ce yana so ba?"

"Kuma ka kwashi kuɗi har 500k ku ka kai, to wallahi sai dai ayi wadda za ayi, auren nan ba za ayi shi ba, ban lamunci auren fari ya auri wata bazawara ba, lallai yarinyar nan munafuka ce macuciya, har aure ma ta taɓa yi"

"A irin wannan ƙadamin, idan ɗa namiji yana son abu ba ya ji ba ya gani, ba ya ganin aibun abun, ki bi a sannu kan yaron nan ya fara bujure miki, na so ace matar Alhaji Sabo ba ta yi gaggawar gaya miki ba, da kaina zan gaya miki, amma tun da ta riga ta gaya miki shikenan "

"Ba wani baka yi niyyar gaya mini ba, to idan shi ba shi da hankali, ni ina da shi"

Ya girgiza kai ya ce "Hankalin nan dai ban ga alama ba da saura bilki, baki san rayuwa ba haryanzu "

"Ni ka ke cewa bani da hankali?"

Ya tashi tsaye ya riƙo hannunta da ƙarfi ya ce "Ni da ke duk musulmai ne, da aka haufa a cikin musulunci gaba da baya. Kuma muna koyi da rayuwar annabi sallalahu alaihi Wasallam ne, idan kuwa haka ne, sunna ce mai ƙarfi raihan zai yi koyi da ita.
Bilki yaranki Allah ne ya shirya miki su, ba wai dan kina da techniques na yadda ake tarbiyar yaran ba, mutane da yawa na ganin bai dace biye wa yarana da nake yi a kan abun da suke so ba, ina tunatar da ke zamani ya sauya, ka yi wa yaranka tarbiyya dai-dai da zamani sai a zauna lafiya. Wannan baloƙoƙon da ki ke kamar a zamanin da, ba abun da zai haifar miki, illa bijirewar yaron nan, shawara nake baki kar ki matsa da yawa, dan yana wani stage ne da ba ya ji ba ya gani, cikar muradi kawai yake fata, amma idan kin ƙi ji gaki nan ga shi" kamar ta shaƙe Alhaji Tahir haka take ji, tare da jinjina tsantsan rashin hankali da wauta irin na raihan, da ma ba ta ce za ta yi masa aure ba, ta bar shi a haka, kawai daga cewa za ta yi masa aure, ya jajubo wannan ina da munin wai ita zai aura.

Raihan ya fito daga Masallaci sallar la'asar, Ummi ta kira wayarsa, ya samu wuri ya tsaya tare da É—agawa "Hello my love"

Cikin sassanyar muryarta da yake cewa iyayi ta ce "Barka da yamma"

"Yauwwa barka, kin wuni lafiya?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya su mami?"

"Duk suna lafiya, ina noor É—ina?"

"Tana tahfiz" ta faÉ—a a hankali.

Ya ce "Kirana ki ka yi ki ji muryata love?"
Chapter 81 · 0% Book details