← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 134

Sashe 106

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da suka dawo ya hanata gaya wa kowa sun dawo, ya ce sai sun gama hutawa. Ita kuwa ba ta zauna hutun ba, saboda ganin yadda gidan yayi mata ƙura da yawa.

"Dan Allah ki zauna ki huta, aikin nan yayi miki yawa, ki yi da kaÉ—an-kaÉ—an, an ce a samo miki Æ´ar aiki kin ce ba kya so".

Ta ce "Bana son in ga wurin da datti ne, dan Allah ka yi haƙuri" haka ya ƙyaleta ta yi ta share-sharenta.

Sai da suka kwana biyu da dawowa, ya je gida, ya gaida su mami. Alhaji ya din ga mitar meyasa bai zo da ummi ba.

Raihan ya ce "Ta gaji ne sosai, ba ta saba doguwar tafiya ba, kamar ma dai ba ta jin daÉ—i shiyasa na baro ta a gida".

"Allah sarki, with time za ta saba ne in sha Allah" ya samu kyakkyawar karɓa daga Hajiya da Alhaji banda mami, da ke masa abu kamar agola ba ɗanta ba.

Ganin shirun yayi yawa ya sanya ya miƙe zai tafi, da mamaki mami take kallonsa kamar yanayin ko in kular da take yi masa baya damunsa balle ya saduda.

"Ya maganar mu?"

Ya É—an yi turus ya ce "Wace maganar?"

Ta ce "Tambayata ma ka ke yi?"

"Mami ki dubi girman Allah ki yi haƙuri, wallahi ni bana son yarinyar nan, ummi ba ta yi mini laifin komai ba, watanmu shida fa da aure har kuma sai na ƙara aure, da ƙanan shekaruna in tara mata"

"Raihan ni ka ke gayawa ba ka son safiyya? Kuma da ka ji maganata tun farko ai da haka ba ta faru ba, kuma wallahi ka cigaba da bujire mini sai na kashe auren nan a kwanakin nan dan bana ƙaunar yarinyar nan".

"Mami, dan Allah ki taimaki rayuwata, ki ka rabani da ummi, ba zaki iya sama mini matar da zata maye mini gurbinta ba!.

Ayshercool
08081012143

                      *CUTARWA*

*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

40

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

AYSHERCOOL
08081012143

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

41

Galala mami ta buɗe baki tana kallon raihan, ba ta taɓa zaton wannan kalaman daga bakinsa ba ko a mafarki, ta rasa wace amsar ma yakamata ta bashi, ganin ba ta da abun cewa ya sanya jiki a sanyaye ya fice, zuciyarsa na wani irin zafi.

Har ya nufi motarsa ya ji an riƙe hannunsa, ya waiwaya ya ga Salim.

Ya gyara nutsuwarsa cikin girmamawa ya ce "Yaya ina wuni?"

"Meyafaru ne?"

Raihan ya kalleshi ya ce "A ina?"

"Dambe ka yi ne? Ba ka ga yadda ka ke gumi ba, idonka ma yayi ja?"

Ya girgiza kai ya ce "Bakomai, dama mun dawo ne na zo gida mu gaisa ban zaci ma kana nan ba"

Salim ya kama hannun raihan ya wuce da shi É—akinsa, Sagir na kwance a falo yana kallon tv suka shigo, sallamar su kawai ya amsa ya cigaba da abun da yake yi.

Ya zaunar da raihan a kan kujera, shima ya mayar da hankali a kan kallon ba tare da ya cewa raihan É—in komai ba.

Sun shafe a ƙalla mintuna talatin a haka, sannan Salim ya numfasa ya kalli raihan ya ce "Are you ok now?"

Ya jinjina masa kai ya ce "Yes, na gode sosai"

Salim ya sake tattara nutsuwar sa a kan raihan ya ce "Me yake faruwa? Kar ka ɓoye mini" raihan ya yi shiru yana yi wa Salim kallon mamaki, dan sam ba mai shiga abun da bai shafe shi ba ne ba.

Kamar ya san me raihan yake tunani a kai ya ce "Na san zaka yi mamakin tambayarka da nake yi, na samu labarin matsin lambar da ake yi maka a kan ƙara aure a wurin Hajiya, kuma daga dawowarka ba zai yiwu ace har  wani abun ɓacin rai ya faru da za ka shiga cikin tashin hankali ba, in dai ba a kan maganar ba ne ba.
Ka san meyasa na titsuyeka nake tambayar ka?"

Raihan ya girgiza masa kai alamar a'a.

"Alƙawarin da muka ɗaukko wa mahaifiyarta da ni da kai, Allah ya sani ina tausayin baiwar Allah nan sosai, kuma kai ka bani labarin irin wahalar da take sha a rayuwa, idan har ka rabu da ita, ka yi wa mahaifiyarka biyayya haka ake son ɗa na gari amma ka sa a ranka ko da ranka ko bayan ranka sai wani ya auri ƴar ka ya saketa!.
Haka zalika idan ka auri wannan yarinyar ka zalunci ummi, ko ita wadda zaka aura É—in, shi ma ka shirya kare kanka a gaban Allah"

Gaba ɗaya raihan ya sake rikicewa ya ce "Wallahi yaya na rasa yadda zan yi, ina son ummi muna zaune lafiya tana kyautata mini, me zai saka na saketa ko ace sai na yi wani auren? Ni ba na son safiyya a matsayin matar aure, kuma bana son saɓa wa mami"

Salim ya kaɗa ƙafa ya ce "Am sorry to say, iyayenmu mata wasu lokutan na da gajeren tunani, iyayenmu da suke aure fa, ba daga sama suka faɗo ba, su ma ƴaƴan wasu ne. Anyway Allah ya kyauta, na kira ka ne dama dan na yi maka tuni a kan amanar da ka ɗaukko, kayi ƙoƙarin gyara tsakanin ka da mahaifiyar ka, ba tare da wani ya cutu ba".

Raihan ya jinjina kai ya ce "Na gode sosai yaya da tunatarwa, zan yi iya ƙoƙarina in sha Allah" yayi musu sallama ya fice.

Sagir ya bi bayansa da kallo, yana wani tunani a ransa na kowa da irin jarrabawar sa, shi da yake mai biyayya babarsa ta saka shi a gaba, su da suke sai a hankali su suka saka tasu uwar a gaba, kuma ya san su ta su uwar ba za ta taɓa yi musu haka ba, amma tabbas da shi ne a matsayin raihan, ba wanda ya isa ya tursasa shi yin abun da ba ya so.

Mami kuwa hankalinta ya gama tashi, tare da tabattar wa da kanta, ummi da danginta sun haÉ—u sun mallake mata É—a, dama ance irin su ba sa zaman aure haka sai sun yi asiri.

Cikin rashin dabara, ta kira yayarta da ke yi mata baƙi jagoranci, ta zayyane mata komai, aikuwa ta ƙara zigata a kan ko dai ta raba raihan da ummi, ko kuma maganar Hajiya ta zama gaskiya, ɗan so ya auri matar so!.

Raihan ya koma gida, yana ta saƙe-saƙe, amma tunda ya ci ya ƙoshi, suka shiga soyayyarsu da ummi sai ya manta, ta hau bashi labarin aikin da ta sha na gyara gidan jikinta sai ciwo yake.

Ya yamutsa fuska ya ce "Ki daina gaya mini kin wahalar mini da kanki, tun da dai ba kya jin magana".

Tayi murmushi ta ce "Zaujul janna, wata alfarma nake nema dan Allah"

Ya ce "Yau Allah ya yi kenan, tun kan mu tafi nake ganin alamar akwai magana a bakinki, kin ƙi faɗa ne kawai. Ina jinki"

Ta É—an yi jimm tana jujjuya maganar sannan ta ce "Dan Allah idan ban takura maka ba, dan Allah so nake idan da É—an space a taimaka a É—auki yaya Abdul aiki dan Allah, amma idan babu shikenan bakomai"

Kawai ya zuba mata ido, dama wannan maganar take ta yi wa kwana-kwana.

Ya maze ya ce "Ki rubuta a rubuce ki kai mini office" hararsa tayi ta ce "zaka sake kenan ko?"

Yayi dariya ya ce "Ashe baki manta ba?"

"Ya za ayi na manta, waccan ranar sai da na yi kuka"

"Koma me na yi miki ai ke ki ka janyo, handsome guy kamar ni, a wanke hannu a taɓa ɗan kyakykyawa da ni, wai ki ka rufe ido ba zaki aureni ba, wai ni yaro ne ko?" Ta tura baki tana kawar da kanta gefe.

"Kuma yanzu ko kunya ba kya ji, kin kwanta a jikin yaro kina shagwaɓa, ko kuma yanzu na girma ne?"

"Wai kai abu ba ya wucewa?"

Yayi dariya ya ce "Ina zai wuce, memory ne mai girman gaske da ba zai shafe ba" yayi maganar yana kai bakinsa na ta, ta lumshe idonta ya ce "To buÉ—e idonki na fasa, ai ni yaro ne, ba ma a yaye ni ba, ki ke wani lumshe ido"

Ta buÉ—e idonta tana kallon sa, ba ta ce masa komai ba, tayi murmushi, dan ta fuskanci tsokana yake ji, ta shammace shi ta yi kissing É—in sa.

"Eh lallai kin waye baby, ke da ko kallon mutane ba kya iya yi"

"Ba zan kula ka yanzu ba, zan rama ne" ya rungume ta ya ce "Ai ba zaki iya hukunta ni ba, duk laifin da zan yi, ki tura mini CV Abdul ta email É—ina, i will find a position that will suit him, ko akwai wani position da ki ke so a bashi ne?"

"A'a kowanne ka bashi yayi, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi"

"Never mind sweetheart, ko wa ki ka kawo ki ka ce na yi masa abu zan yi masa, wannan dolena ne kar ki ji komai, gobe in Allah ya kaimu zan cigaba da koya miki driving, na ga kina da saurin gane abu, motarki ta kusa zuwa in sha Allah, da ke da mami da yaya Salim"

Ummi ta ce "A'a ni a naka ka bani É—aya, sai ka canza wata kar mami tayi maka faÉ—a" kamar bai ji ba, ya bar maganar suka shiga wata.

Bayan sallar asuba cikin bacci ya ji ummi na ƙwala masa kira a banɗaki, yana zuwa ya tarar da ita a tsaye jini yana bin ƙafafuwan ta.

A kiÉ—ime ya ce "Lafiya kuwa?"

Cikin kuka ta ce "Kawai marata na ji tana ciwo, sai kuma jini yake ta zuba da yawa, ba haka na saba yin period ba"

Ya girgiza kai ya ce "Wannan ai ya fi ƙarfin period, asibiti zamu tafi"
Chapter 106 · 0% Book details