← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 134

Sashe 129

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya ta maze kamar babu abun da yake faruwa ta ce "Tun yanzu ka fara nuna wariya, ka tafi wurin matarka ko ɗaukar su ba ka yi ba" cikin washe baki ya ce "Tuba nake, dole in fara zuwa kanta, saboda su an yanka mini mata" yayi maganar ko a jikinsa yana ɗaukar su, wanda hakan ya sake ƙular da mami.

Ya ce "Tubarkallah, Hajiya irin idon ummi ne da su, brown masu kyau masha Allah, yaya ka ga namijin kallesu duk farare. Alhamdilillah" yayi maganar yana kallon Salim.

Farincikin da mariya ta gani a fuskar raihan, sai ya mantar da ita takaicin abun da mami ta yi musu.

Sauran mutanen maiduguri da suka zo ganin gidan mariya, suka cika asibitin. Ana jimawa ma sai ga dr. Ga Alhaji.

Raihan ya din ga sanar da Æ´an uwa batun haihuwar.

Tsabar takaicin yadda raihan yake rawar ƙafa, ya sanya ta tashi ta bar asibitin.

Sai da ummi ta yi awa shida tana bacci, sannan nurses suka tasheta, suka É—agata aka wanke ta, sannan aka bata abinci.
Ta saka kaya tayi kyau, kamar ba ita ba, sannan aka turo ta a kan gado aka mayar da ita main É—akin da take.

Suka din ga murna ganin an fito da ummi ras da ita.

Sai jerawa ummi sannu ake yi, aka miƙo mata yaran dan ta shayar da su, amma ta kasa saboda yadda ido ya yi yawa.

Hajiya tare da Salim suka koma gida, ta yi wanka ta yo girki, suka dawo da Alhaji.

Shi ma Alhaji baki buÉ—e yake ta murna, yana yi wa jariran addu'a, duk da babu wanda ya gaya masa abun da matarsa ta yi.

Sai dai noor ta gaya wa ummi, abun da mamin ta ce, wanda ba ƙaramin ciwo yayi mata ba, sai dai ta basar saboda tana cikin murnar kyautar da Allah ya bata.

Ummi ta ce "Mama, jikin yaran nan kamar jariran mage, basu da gashi kwata-kwata".

"Me ki ke ci na baka na zuba? Zai fito in sha Allah"

Dr. Ma da daddare ya zo ganin jariran, tare da yi mata sannu.

Kusan kwanaki uku, ana ta shigowa ana fita duba ummi, a kwanaki ukun nan gashi ya cika kan yaran nan fal.

Kwanan ummi biyar, aka sallame su daga asibiti, raihan ya ce bai yadda a É—auki hoton yaransa ba a saka a waya. Saboda masha Allah kai ba zaka ce ummi ce ta haife su ba, dan sun fi kama da larabawa sosai.

Su Hajiya Aishan bauchi, da sauran jama'arta, duk suna kano, sai da ummi ta yi kwana goma da haihuwa, sannan aka shirya gagarumin taron suna a wani katafaren event center.

Sai ranar suna Æ´an gagarawa suka zo, aka ci aka sha, ummi sun samu kyaututtuka sosai da sosai ita da yaran, manyan mutane abokan hulÉ—ar Alhaji Tahir, da abokan aikin Raihan, ban da Æ´an uwa da abokan arziki.

Sai dai kan ranar sunan nan, yaran nan sun juye kalar larabawa sosai da sosai, gashi ya cika kansu da girarsu, kuma dukkansu brown eyes ne da su, namijin mai baƙin gashi, macen kuma irin na ummi.

Sai dai sunan da aka sakawa yaran ya yamutsa hazo, dan kuwa raihan sunan ummi ya saka wa macen Salma, namijin ya saka masa Muhammad, wai ya yi wa kansa takwara, ya yi wa Alhajin su, kuma ya yi wa mahaifin Ummi, tun da duk sunansu Muhammad laƙanin ne daban-daban, aka yi musu laƙani da Iman da kuma Ayman.

Ba yadda ummi ba ta yi da raihan ba, a kan ya canzawa macen suna, kar ya janyo mata magana a cikin dangi.

Amma ya ce "Kome mutum zai ce ya ce, son da nake yi miki, dole na yi miki takwara dole duniya ta shaida ina son matata".

Noor ta sha kwalliya, kamar amarya.

Ta je ta saka salim a gaba, sai ya yi mata hotuna da iphone É—in sa.

Ya gama yi mata hotunan yana nuna mata, sai murmushi take yi, ya kalleta ya ce "Kin yi kyau kamar ranar bikinmu" a razane ta kalleshi ta ce "Bikinmu kuma?"

"Eh mana, ko ba kya so na?"

Ta É—an sosa kai ta ce "Yarinya ce fa ni"

"Ba kya son tsoho ko?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a kai ba tsoho ba ne"

Ya ce "Tsoho ne mana a kan ki, am 37 you are just 15, dama so nake bayan suna in yi wa Alhajinmu magana, amma tun da kin ce haka shikenan, idan kin gama hotunan ki kawo mini wayar"sai kuma ta ji babu daÉ—i.

Mami kuwa a ranar sunan sai da ta kira raihan, ta ƙare masa zagi da cin mutunci, wai ya ƙare a gidin mace, saboda asara har da saka wa ƴar sa sunanta, bayan uban kuɗin da ya kashe mata ita da yaranta.

Shi dai yayi shiru bai ce komai ba, dan ya san duk abun da ya yi wa ummi bai faÉ—i ba, kuma ba zai yi hidimar da Alhajinsu yake yi wa iyalinsa ba.

Da daddare ummi ta yi wanka ta saka kaya, Anty maryam ma ta wanke jariran, an samu sun yi bacci saboda sun gaji, sun sha kuka da jagwalgwalon Æ´an suna.

Raihan ya shigo yana yi wa ummi murmushi.

"My MD, murmushin me ka ke yi ne?"

"Kallonki kawai yana sani murmushi, amma murmushin na yau na musamman ne, guess what?"

Ta girgiza masa kai ta ce "I have no idea"

Ya kamo hannunta ya danƙa mata mukullin mota ya ce "Gashi in ji Alhaji, ya ce a baki ya riga ni"

Ummi ta waro ido ta ce "MD mota Alhaji ya bani" ta rungume raihan tana murna, ta din ga zuba masa addu'a da shi da Alhaji.

Da gudu ta fita falo, tana nuna wa su mama da ba su riga sun bar gidan ba, aka din ga yi mata murna.

Noor ta ce "Yaya ummi baki ji zuciyata ba, na taya ki murna, amma ina son mu yi magana"

Suka keɓe da noor, ta gaya wa ummi abun da ya faru tsakaninta da Salim.

"Noor meyasa baki da wayo ne? To meye aibun yayan?"

Noor ta ce "To ai ni yarinya ce, kuma ni bana son ayi ta yi mini surutu kamar yadda aka yi miki"

"To sai me? Wataƙila da ina nan a gida ban yi auren ba, ai yanzu ki samu mai sonki tsakani da Allah shi ne. Shi da ake son ya yi auren ma, kin san da manyan ƴan mata nawa aka haɗa shi, duk ya ce ba ya so dan ya ce yana sonki zaki wulaƙanta mini yaya, to kin yi wa kanki"

Noor ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri"

"Kin fi son ki koma gida kina jerawa da kausar kuna faÉ—a kenan? Ke ba kya son ki ganki kema a gidanki?"

"To ai yanzu ba a gida nake ba, gidan mama zan koma, ni ba zan koma gidanmu ba, maama haushina take ji kamar ba ta son ganina ma"

"A'a ba sonki ne ba ta yi ba, amma dai yaya Salim dai kin yi wa kanki"

"Na shiga uku, yanzu ya zan yi?"

"Ki ɗauki waya ki bashi haƙuri"

Noor ta tura baki ta ta ce "Salon ajina ya zube" ummi ta ƙare mata kallo kawai tayi tsaki ta bar ɗakin.

Ummi na komawa É—aki ta kira Salim, suka gaisa sannan ta ce "Yaya ka ji Alhaji ya bani mota?"

Yayi murmushi ya ce "Na riga ki sani ai, ina taya ki murna ƙanwata"

"Na gode sosai yaya salim, Allah ya saka muku da mafificin alkhairi"

"Amin ƙanwata, Allah ya raya mana su Iman"

"Amin yaya. Yauwwa noor ta gaya mini shirmen da ta yi maka, abun duk ya dame ta, dan Allah ka rabu da ita, Alhaji ya samu dr. Da maganar".

Yayi murmushi ya ce "Kin je kin takura mata ko? Bana son takura ta, daga baya nake ganin kamar na yi wauta nayi mata tsufa"

"Dan Allah ka bar wannan maganar, tana sonka, duk ta damu fa"

"Amma, kina ganin dr. Zai bani noor kuwa? Kin san ni ina da case"

"A'a yaya me zai hana? Kuma dan kana da case sai a ƙyamace ka? Ai yanzu ka shiryu a kan yadda na sanka a da, dan Allah ka ƙyale shirmen noor yaya"

Yayi murmushi ya ce "Auta danger, shikenan zan yi tunani, a bata lokaci"

"Dan Allah yaya ka ƙyaleta, mun yi magana da ita fa"

"To shikenan, sai da safe"

"Yauwwa yaya, a yi wa su hajiya bangajiya"

Suka yi sallama, ta din ga addu'a, Allah ya tabattar da alkhairi, dan tana fatan noor ta yi aure da wuri, tun kan farida ta ƙwace ta, ta siffantu da miyagun halayenta.

Har dr. Ummi ta kira, ta sanar masa da abun alkhairin da Alhaji ya yi mata.

Ƴan gagarawa sai da suka kwana uku a gidan ummi, da zasu tafi ta haɗa kayan suna ta basu suka tafi da shi.

Ummi ta saka noor a gaba, ta bata waya ta kira Salim.

Sai dai da ya É—aga wayar ya ji murayarta, bai kashe ba suka gaisa.

"First born"

"Mmmm auta"

"Fushi ka ke da ni ko?"

"Me ki ka yi mini zan yi fushi da ke?"

Ta É—an sosa kai ta ce "Maganar da muka yi ranar suna".

"Ai ta wuce auta"

"Ba ka so na yanzu?"

Yayi murmushi ya ce "Ke dai ba kya so na, an bar maganar bana son takura miki"

"To yanzu na canza shawara ka yi haƙuri"

"To" ta ɓata rai saboda yadda yake bata amsa a taƙaice da izza.

Ummi ta girgiza mata kai, alamar kar ta yi fushi.

"Yaya Salim"

"Noor"

"Idan muka yi auren zaka bar ni in yi makaranta, ka ga yaya inteesar mijinta hanata yayi daga baya".

"Zan barki in sha Allah"

"A'a rantse da Allah, kar ka canza shawara" yayi mata shiru, ummi ta dafe kai, saboda wautar da noor É—in ke yi.

Bayan sun gama wayar, ummi ta ce "Eh lallai akwai jan aiki a gabana, noor babban mutum yayi magana ki ce ya rantse? Ke fa baki da kai"

"To ba ki ji yadda yake yi mini magana da gadara ba, da fa ba haka yake yi mini ba"
Chapter 129 · 0% Book details