← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 134

Sashe 121

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Noor ta ce "Ohh, yaya ummi soyayya da daÉ—i ko? Ke ban da wannan abun da ya faru na ga yana sonki ba kwa faÉ—a, amma anty intee da wayona fa lokacin da mijinta Salim yake zuwa suke shan soyayya amma yanzu kullum cikin faÉ—a kamar abokiyar gabarsa"

Ummi ta ce "Waye ya ce miki bama faɗa? Babu wata soyayya da za ayi zaman aure ace babu saɓani, sai dai danganta da yadda aka gina soyayyar, idan har ta gaskiya ce kuma an fahimci juna, ko saɓani yazo za a warware cikin sauƙi. Ni kaina MD ba dan yana sona ba, kuma mutum ne mai fahimta ba da laifukan da na yi masa a kwanakin nan wani zancen ake yi ba wannan ba, shiyasa ko mun samu saɓani nake duba alkhairnsa bana taɓa yi masa hukunci da laifin da ya yi mini".

Noor ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ni wallahi soyayyar da ba a faÉ—a nake so, idan muka yi faÉ—a kuka zan yi"

Ummi tayi dariya ta ce "Sai ki tafi littafi ko film, ko kuma tatsuniya, a nan zaki samu wadda ba a faÉ—an. Bari na shiga daga ciki"

Noor ta yi shiru tana ta zancen zuci, ita har ga Allah ta fi son ayi ta soyayya babu faÉ—a.

Ummi daga yin wanka ta ji sanyin Ac, ta kwanta ta hau bacci a É—akinta. Noor ta zage tana ta gyara gidan, ta iya aiki sosai da sosai saboda zama da ummi.

Ta gama aikin ta shiga ta yi wanka ta saka wata ƴar doguwar riga da ɗan kwali, ta dawo falo tana shan lemo mai sanyi. Ba ta daɗe da zama ba a ka buga ƙofar falon.

Ta tashi ba tare da tambayar waye ba, ta buɗe ƙofar, kallonsa ta tsaya tana yi tana murmushi, hannunsa ɗauke da manyan kulolin abinci,  ta ce "Sai yanzu ko? To koma mun yafe" alama yayi mata da ido, ya tura ƙofar hajiya ta gani a bayansa.

Da sauri noor ta nutsu, ta durƙusa tana gaishe ta, saboda ta shaidata, ta karɓi kayan hannunta suka ƙarasa cikin falon.

Hajiya ta ce wa noor "Kamar na so na gane ki"

Salim ya ce "Ƙanwar ummi ce" ya kalli ummi ya ce "Ga hajiya, in faɗa mata me ki ka ce a kan ta?"

Noor ta kalleshi da sauri tana zare ido, ta girgiza masa kai.

Hajiya ta kalleshi ta kalleta, ta ce "Laifi na yi mata?"

Yayi murmushi ya ce "Hotonki ta gani a wayata, ta ce na sanki, na ce eh Æ´ar uwammu ce ke, wai ranar bikin su raihan tana ta kallonki, wai kwalliyar ki tayi kyau, gashi kin iya turanci, kina magana kina turanci, har gwada maganarta ki ka yi ko ba ayi ba?"

Noor tamkar ta nutse a wurin nan, ta sunkuyar da kai tana hararsa ta ƙasan ido.

Hajiya ta yi dariya ta ce "To ai da sauƙi tun da ba laifi na yi mata ba, ina ummin ne?" Duk da noor ta san ummi bacci take yi, ta tashi da sauri ta ce "bari na kirawo ta" har noor ta bar falon kallonta yake yi yana dariya.

Hajiya ta ce "Wai ya aka yi har ku ka saba haka ne?"

Ya gyara zamansa ya ce "Ina ganinta a nan gidan, sai kuma lokacin da aka samu matsalar nan na su raihan, da na je gidansu ita ta gaya mini. Ta wurinta na din ga samun information É—in da na samu ummi a can garinsu. She's very funny ne kawai tana bani dariya.

Hajiya ma ta yi murmushi, noor ta dawo falon amma ta laɓe ta bayan labule ta ce "Na duba bacci take yi"

Ta gudu ta koma kitchen, ta haɗa musu ruwa da fruit, amma ta kasa fitowa tana jin kunya, sai a yanzu ta fuskanci hajiya mahaifiyar Salim ce dan suna kama sosai, saɓanin da ya ce mata ƴar uwarsu ce.

Da ƙyar ta dawo falon tana sunkuyar da kai.

Hajiya ta ce "Ya sunanki ne?"

"Mariya, amma ana ce mini noor, maman ummi aka yi wa takwara aka saka mini sunanta"

Hajiya ta ce "Masha Allah noor, kar ki damu da abun da ya faɗa rabu da shi, bari mu tafi ga abinci muka zo wa da ummi, na zo na ƙara duba jikinta"

Noor ta ce "Dan Allah kar ku tafi, bari na tashe ta"

Hajiya ta ce  "A'a ba sai kin taso ta ba"

Muryar ummi suka ji tana cewa "Hajiya sannunku da zuwa, wallahi bacci ne ya kwashe ni"

Hajiya suna can suna hira da ummi, Salim ya fita, noor ta bi bayansa.

Yana tsaye yana waya ya ji muryarta ta ce "Allah ya kama ka"

Ya waiwayo ya ce "Da na yi me?"

"Ashe mamanku ce"

Ya ce "A'a ƙanwar Alhaji ce"

Noor ta ce "To wallahi mamanku ce, shi ne ka gaya mata abun da na ce, duk na ji kunya".

Salim ya yi dariya ya ce "Last born"

Ta ce "Ba wata last born, wallahi ka bani kunya sosai"

Yayi dariya yana kallonta, ƴar ƙarama da ita sai baki.

"Ka san me? Babanmu yayi aure fa, ya auri babar su yaya ummi, mamanmu sai fitina take yi a gida, ni kuwa na yi tahowata nan"

Ya ce "Kin kyauta, ba kyau kallon manya idan sun samu saɓani"

Kawai ta saka hannu a aljihun rigarsa, sai ga kwalin sigari.

Ta ce "Ba ka daina ba ko? Ka ce mini fa ka daina"

Ya haÉ—e rai ya ce "Meyasa ba ki da kunya ne? Dan kin ga ina yi miki dariya har ki ka saka hannu a aljihuna?"

Noor ta ce "To ai ba kuÉ—i na É—aukko ba, kuma ka ce mini ka daina"

Hannu ya kai ya karɓa, ya mayar da kayarsa cikin aljihunsa, ya juya ya tafi.

3 MONTHS BACK

Salim ya je gidan raihan, amma maigadi ya sanar masa raihan ya ce duk wanda ya zo ace masa baya nan.

Ya tambayi maigadin dalili, ya ce bai sani ba, amma tun da hajiya bilki ta je, ummi ta tafi tana kuka da kayanta a hannu, amma bai san meyafaru ba.

Tun daga nan jikinsa ya bashi akwai wani abu, da safe neehal za ta fita suka haÉ—u, ya tambayeta meyafaru a gidan raihan da mami ta je, ta ce masa ba komai, sai da ya zageta sannan ta gaya masa abun da ya faru.

Da azahar ya wuce gidan su ummi  dan jin meyafaru, ya haɗu da noor a hanya za ta je makarantar islmaiyya .
"Ke!" Yayi maganar yana sauke glass.

Ta tsaya ta ce "Sunana mariya wato noor" tsyaawa yayi yana kallon ta ya ce "Kin gane ni?"

"Eh, na ganeka É—an uwan su yaya raihan"

"Yauwwa, ummi na gida ne?"

Ta ce "A'a tana gidanta"

Ya buÉ—e motar ya ce "Ba ta can ki gaya mini gaskiya "

Ta ce "Eh ta zo gida, mamanmu ta ce wai ba zata zauna ba, ba a san fa in da take ba, yaya raihan ya zo ana ta nemanta, sakinta fa yayi".

Salim ya ce "Ina ta tafi yanzu?"

"Gaskiya ba zan gaya maka ba, islamiyya fa zan tafi, kar na makara".

Salim ya ce "Shigo mu tafi na kai ki islamiyyar "

"A'a ni ba zan hau motar wanda ban sani ba"

Ya ce "A'a ai ni kin sanni, yayan raihan ne ni"

Ta ce "Bari na gaya maka dai, duk da ta ce kar na sake na gaya wa kowa, gagarwa ta tafi, can garinmu a jigawa, amma kar ka gayawa yaya raihan, ta ce kar na faÉ—a, jiya kan ta tafi ta gaya mini".

Salim ya ce "Na gode sosai da ki ka gaya mini, daga gagarwan ina za a yi aje gidan"

Ta wassafa masa komai, kwatancen gidan tun daga tasha, da yake ba ɓoyayye bane ba, ya yi wa noor godiya ya tafi.

A yammacin ya tafi gagarawa, bai jira sai washegari ba, yayi sa'a ya tarar da ummi, kuma ta sanar masa duk abun da ya faru, da shawarar da ta yanke, ta kuma roƙe shi a kan dan Allah kar ya gayawa kowa in da take.

Bayan wata guda, ya haÉ—u da noor ta je gidan yayar farida, a sharaÉ—a, shi kuma ya je wurin wani abokinsa.

Suka gaisa, yake bugun cikinta ko an ga ummi, ta ce masa ba a ganta ba, ta nuna masa yadda take cikin damuwa, rashin sanin in da ummi take.
Ta saki baki tayi ta bashi labarin zaman da ummi ta yi a gidansu, da yadda ake yi wa ummi gorin ta auri yaro ƙaninta.

Ta ce "Yauwwa ka ce kai yayan yaya raihan ne, amma ba mamanku É—aya ba ko?"

Ya ce "Eh"

"To wallahi in gaya maka mamansa ce ta saka ya saketa, ba ta sonta wai mummuna ce ta auri yaro, dan Allah ai auren yaro ba haramun bane ko? Kuma ai yaya raihan babba ne yana da gemu fa"

Ya ce "Eh gaskiya ba laifi ba ne, in dai mutum yayi gemu ba yaro bane"

Message ya shigo wayarsa, ta kalli lock screen É—in sa, da hoton hajiya ne a kai, ta ce "Laa ka san wannan matar?"

Ya amsa da "Eh, Æ´ar uwanmu ce"

"Innalillahi, ta burgeni lokacin bikinsu yaya ummi, ta iya wanka, gashi ta iya turanci"

Yayi dariya ya ce "Gaskiya ne"

Noor ta ce "Wallahi duk ƙarfin hali nake yi, rashin yaya ummi har kuka nake yi, rayuwarsu tayi ta bani sha'awa da MD ba sa faɗa, amma kawai ya saketa na zata auren saurayi ya fi daɗi, amma na fasa"

"Tsoho zaki aura kenan? Ai shi ma yana sonta ba laifinsa ba ne"

Ta ce "A'a ba tsoho nake so ba, me dai gemu kamar naka, wai dan Allah da ka je gagarawa ba ka ga yaya ummi ba?"

Abun da ta faÉ—a na farko ya bashi dariya, ya ce "Da na ganta ai da na gaya miki, amma me zaki bani na nemo miki ita?"

Noor ta ce "To ai bani da kuÉ—i"

Ya ce "Ba kuÉ—i zaki bani ba, zan gaya miki amma sai na nemo miki ita"

Tun daga ranar suka saba da Salim, lokaci-lokaci ya kan bi unguwarsu, dan ya ganta, saboda yana son surutunta.
Chapter 121 · 0% Book details