Sashe 58
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Tahir dariya kawai yake yi wa raihan, so yake dole sai ya zame, kuma ya san dalilin sa na yin haka, dan raihan akwai biyayya in dai abu zai faranta masa rai zai yi, da mamansa ne ma suke faÉ—a wasu lokutan ba su fiye shiri ba, idan ta zo da abu na son zuciya, ya ce ba zai yi ba.
Duk da ummi ta É—an girmewa Raihan, sannu a hankali ya nuna mata shi namiji ne, domin kuwa yafi ummi wayo nesa ba kusa ba, dan bata ankara ba, suka yi wani irin mugun sabo da ita da shi, duk É—ari-É—arinta da shi, ta sake jiki da shi, dan barkwancinsa kawai nishaÉ—i yake saka ta.
Kullum a wurinta yake karyawa, da safe sai ta tafi masa da abinci, kuma cikin ikon Allah babu wanda ya sanya mata ido ya lura da shige da ficenta.
Shi kansa raihan a tarayyarsa da ummi, ya san tana da baki dan tana magana tana tsoron yi ne, saboda yanayi na yadda al'umma suke karɓar ta.
Idan suna hira, wasu lokutan manager sai ya kalleta ya ce "Wai ummi dama kina da baki haka?" Sai ta yi shiru ta daina maganar cikin jin kunya.
Gaba ɗaya ta daina jin nauyin raihan, haka kurum sai ya zame daga office, ya taho wurin aikinta, manager har tambayarsa yake "Wai kai Raihan baka sana'a ne? Kullum kana liƙe a wurin ummi?".
Kasancewar manager matashi ne, da kaɗan zai girmewa ummi, ƙanin mai shagon ne, dan haka Raihan ya ce "Eh ni bani da sana'a, zaman banza nake a yanzu, shiyasa kullum muke tare da ita".
"Ta ce Abdul yayanta ne, kai kuma ƙaninta, anya ba ka girmeta ba kuwa? Ka yi ta mata wayo, ta zo da ɗan abincinta, ta ajiye maka ka zo ka cinye, ka hanata sakat da surutu, ka zo in baka aiki kaima".
Raihan ya ce "Allah ya kiyaye in yi aiki ku biyani dubu sha biyar, dan wayo, dan kun ganta saliha, ai ta kusa daina aikin nan".
Manager ya ce "Ai tawakalli ta fika, shiyasa take aikin, kai ka raina sana'a, kullum kana liƙe da ita, ka cinye mata abinci, kuma kana jiran a biyata ka karɓe mata kuɗi".
Raihan ya ce "Wai manager abincin nan daga gidanka ake kawo wa ne? Ina ruwanka ne ka dameni fa"
Idan suna abun su shi da manager, sai dai tayi ta dariya, kamar sako da sako manager komai sai yayi magana, shikuma raihan baƙar magana da neman tsokana.
Ummi na jin daɗin aikinta a wurin nan, ko albashin farko ba a bata ba, amma manager yana daga cikin mutanen da suke mutuntata, bai taɓa nuna mata ƙyama ba, kuma tana iya ƙoƙarin ta wurin kula da coustomers ɗin su, idan ta je da wuri ba ruwanta, har share-share yi take yi tayi mopping gaba ɗaya ba ta da damuwa.
Zamanta a wurin yana rage mata damuwoyi da yawa.
Yanzu ma tana ta bawa raihan labarin rigimar noor, ba ta da wata hira sai ta noor.
Cikin nishaɗi take hirar, Raihan yana kallonta, ya ce "Ya aka yi haƙorinki ɗaya ya ɓalle ne? Ko dai da kina yarinya kin yi rashin ji ne?"
Ta yi murmushi tana dariyar yaƙe, da tuna yadda aka yi haƙorin ya ɓalle ranar salla ta ce "A ƙaddara bana jin magana ne, na taho da gudu ranar salla, na faɗa cikin kwanuka na buge baki da tukunya, haƙorin ya ɓalle" tayi maganar tana tuna yadda idiris yayi ball da ita ranar.
Raihan yayi dariya ya ce "Ai da alama, kuma fa da ya ɓalle ɗin yafi kyau, amma dai mijinki sai ya rage sadaki, saboda ɓallewar haƙorin nan, duk da ta wani fannin sai ya ƙara, tun da kina cikin matan da malaman fiƙhu suka ce a ƙarawa sadaki".
Basar da zancen tayi, saboda jin zai ɗaukko wani babban karatu mai nauyin gaske, ita ina ta ga ko saurayi balle ayi zancen ƙari ko ragin sadaki, ita da tun da take, ba wanda ya taɓa cewa yana sonta?.
Raihan yayi mugun sabo da abincin ummi, kusan kullum a wurinta yake karyawa, ba tare da ya san abincinta take sadaukarwa ta bashi ba.
Suna tafe a hanya ta ce "Raihan, manager ya ce a satin nan fa za a biya salary"
"Dubu sha biyar É—in ki ke wa wannan washe bakin?"
"Eh mana, idan Allah ya saka mata albarka zaka sha mamaki".
Ya ce "Oho dai, amma dubu sha biyar ya fi kuÉ—in mayukan da zaki shafa a sata" ta ware ido ta ce "Ni É—in? To wallahi vaselin nake shafawa ko man kaÉ—anya"
Yayi murmushi ya ce "Amma zaki kai ƙaninki shopping ko? Muje ki yi mini sayayya"
"Me ka ke so in saya maka?"
Raihan ya ce "Sai mun je sai in zaɓi abun da nake so"
Ta ce "To shikenan, in sha Allah idan aka biya sai mu je, nima na je shopping ban taɓa zuwa ba fa, to ina zamu je?"
"Ki yi tunanin in da ki ke so mu je" ta jinjina masa kai tana ta murmushi, wai duk saboda dubu sha biyar take wannan farincikin.
"Yauwwa, ya ake ciki da aikin Alhaji kuwa?"
Ya ce "Hmm kin san ya kuma haÉ—a ni da wani, alhakin fitar da zakka, da mutanen da zai biyawa umara da aikin hajji"
Ummi ta ɗan yi shiru ta ce "Masha Allah, sai ka tsaya ka ji tsoron Allah, kar ka bari son rai ya shiga lamarin, wataƙila ya yi hakan ne dan ya gwadaka, ka bawa wanda suke buƙata kayi adalci"
"Haka ne ya sayyada, shiyasa ban so ya sakani ba, kin san ina da yayye, kamar ba zasu ji daÉ—i ba tun da su ne manya, tunda ki ka ce ina ma zaki sake ganin baba ya saki aiki, zaki yi farinciki, sai na sha jinin jikina, komai lokaci ne, wataran da kuÉ—i nima zan nemi na ganshi ya sakani aiki, ba zan ganshi ba"
Ummi ta ce "Wannan haka yake, Allah ya ƙara masa lafiya da nisan kwana, ya yalwata arzikinsa"
"Amin ya Allah sayyada"
***
Kamar kullum sai da ya mayar da ita gida, sannan ya koma office ya cigaba da ayyukan sa, bayan la'asar ya koma gida.
Mami na ganinsa ta hau murmushi, wanda har hakan ya bashi mamaki, ya ce "Mami na ga kina ta fara'a"
Ta ce "Ashe kai Alhaji ya saka duba mutanen da za a bawa zakka, da wanda za a kai umara bana, har da aikin hajji mutum uku?"
Ya kalli mami ya ce "In ji wa?".
"In ji ubanka, da baka gaya mini ba, ai ni mijina ne ya gaya mini"
Ya ɗan yi miƙa ya ce "To shikenan tun da ya gaya miki"
Mami ta ce "Ohh, Allah dai ya cika mini burina, to su wa ka zaɓa? Dan ina da vacancies".
Ya dubi mami ya ce "Vacancies kuma, na me?"
"Ahh wanda za a bawa zakka mana da wanda za a kai umara har ma da aikin hajji".
Raihan ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Amma ni mami, duk a gidanku su Anty Saude, ba wanda ba a kai aikin hajji ba wasu umara, ƙawayenki kuma duk suna da rufin asiri, to wa kuma za a baki? Ai gara a kai waje wasu ma su amfana"
Ta ce "Kai dalla yi mini shiru, nima na san waɗanda suke da buƙata, ka bani vacancies, da kuma kuɗin da zan bayar nima, duk shekara Alhaji yana bani, maganar ma na yi masa ya ce kai ya bawa wannan damar".
Raihan ya ɗan ɓata fuska ya ce "Haba mami, dan Allah me zaki yi da kuɗi? Zan baku vacancies huɗu, ke biyu Hajiya biyu shikenan, kuɗin zakka kuma gaskiya ba zan iya baki ba, an ware percentage ɗin share ku fa, a ribar da aka fitar ta shekara za a baku"
Mami ta shiga tafa hannu, ta ce "Raihan, wai tsaya ni da hajiyar nan muka yi naƙudarka, da komai sai ka daidaitani da ita, kuɗin mijina ka ce ba zaka bani ba Raihan, shikenan ba zan kyauta ko sadaka ba nima?"
Ya miƙe yana zumɓura baki ya ce "Dan Allah mami kiyi haƙuri, nifa ba haka muka yi da Alhaji ba, what if gwadani yake yi, wallahi kin fi Hajiya yawan ci masa kuɗi ma, haba mami dan Allah" sai ta kasa magana ta bi shi da kallo, gashi dai ita ta haife shi, amma idan ya botsare, wasu lokutan kasa magana take yi, dan bata san dalilin da ya sa yake yi mata kwarjini ba wasu lokutan, idan ta yi ba dai-dai ba ɓaro-ɓaro yake gaya mata.
Manager ya kira ummi a waya, ya ce ta turo account number zai tura mata kuÉ—inta na albashi.
Bata da account number, dan haka ta kira raihan jikinta yana rawa dan farinciki ta ce "Raihan, manager ya ce na tura account number, zai turo mini salaryna, amma bani da account, ka bani naka na bashi"
Yayi dariya ya ce "Gaskiya banki za su rufe mini account É—ina idan aka saka dubu sha biyar, ni kuÉ—i idan bai kai dubu É—ari ba, basa shiga account É—ina".
Ta ce "To ko kawai in bari sai da safe idan Allah ya kaimu, idan na je sai ya bani a hannu kawai ko?".
"Ina da lambarsa zan tura masa, amma dan Allah kar ki kasa bacci saboda dubu goma sha biyar, kuma kar ki manta kin yi mini alƙawarin zaki kai ni shopping".
Ayshercool
08081012143
What's app only please ðŸ™
    *CUTARWA!*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
P25
FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
Masu neman free books É—ina, da free pages duk akwai a kan watpad account É—ina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya
Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.
And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ayshercool.
PAID ADVERT!.