Sashe 37
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai azahar yayenta suka zo da ƙanwar babanta, suka tarar da ummi a akan aikin, suka din ga yi wa rahama da farida faɗa, wai dan me za su bar ummi ta yi aikin naman, sai ta sace ta cinye tukuna.
Abdul ne ya fusata ya ce "Yaya ummi ba ɓarauniya ba ce ba, ba ta taɓa ɗaukar abun da ba nata ba"
"Rufewa mutane baki kan in mareka, mara kunya fitsararren banza"
Ummi da jikinta yayi sanyi ta ƙyale musu aikinsu.
Suka gama aikin nama suka kwashe wanda za su kwashe, suka bar saura suka tafi, dr. Ya dawo ya tarar da farida da yaranta suna ta cin naman, ya leƙa ɗakin ummi tana zaune tana ta tilawar Alqur'ani ga gida ya buɗe da ƙamshi, ya shiga ɗakin farida ya ciko leda da nama, ya kai ya bata.
A gaban yara ta rufe shi da masifa, a kan ko dai ummin nan kishiyarta ce ba ta sani ba.
Ganin cin mutuncin da take yi masa a gabansu, ya sanya Abdul tashi ya bar wurin.
Cikin miyagun maganganun da take yi masa, har da gugar zanar ko wani abu ne tsakanin sa da ummi, da ya sanya shi bawa al'amarinta muhimmanci har haka.
Ta dire noor ta tashi ta bar masa falon.
Ummi kuwa da sauri ta wanke hannunta, ta hau naman nan da ci, dan tun ana suyarsa ƙamshin ya cika mata ciki, ranta ya biya.
Sai tayi aikin abinci da nama ba adadi, da ta gama rahama ta shiga ta raba abincin, ta kwashe naman ta hanata, koma ta bar da ɗan kaɗan sai dai ta haɗa da ƙanzo, dan haka nama tana kallo ba za a bata ba.
Ta fito falo, dan samun tsinken sakace, ta tarar da kawunta rungume da jaririya tana ta tsala uban ihu.
Da sauri ta ƙarasa in da yake ta ce "Kawu bani ita, ban taɓa ɗaukarta ba".
Ya miƙa wa ummi ita ya ce "Gata nan mai sunan mamanki, ina fatan ita ta so ki, kuma ta din ga ɗebe miki kewar mamanki"
Da sauri ta ce "Amin ya Allah, Allah yasa" ta karɓi yarinyar ta ce "Mamana ki daina kuka, mama tana da haƙuri, kawu ta zama kakarka kenan? Maman mama ko?"
Sai da ya É—an dara ya ce "Tsohuwa ce kenan?"
Ummi ta É—orata a kafaÉ—arta, tana jin soyayyar yarinyar a ranta, da aka saka mata sunan mamanta.
Haka ummi ta din ga zagaye da ita a falon, tun tana tsala ihun har tayi bacci.
Dr. Ya ce "Lallai ummana kin iya raino, tun da har gashi kakata tayi bacci, kawota ki je ki kwanta"
Ta bashi ita, tana kallon fuskar yarinyar, gashinta har goshi, jawur da ita.
Ya kalli ummi ya ce "Na ga ƙunarki da sauƙi, in sha Allah ranar monday zaki koma school gaba ɗaya"
Ta ce "To Allah ya kaimu"
"Amin, ki je ki kwanta sai da safe" ta juya ta nufi hanyar É—akinta, kamar ta ce ya bata Æ´ar su kwana tare.
Ranar Litinin ta koma ta cigaba da zuwa makaranta, ranar da ta je islamiyya, Maryam ce ta fara ganinta, da sauri ta tashi ta nufi ummi ta ce
"ya jiki?".
Ummi ta ce "Na ji sauƙi"
"Kin warke duka ƙonuwar ta warke?"
Ummi ta jinjina mata kai alamar eh.
Ta ce "Alhamdilillah, dan Allah ki yi haƙuri, tun ranar da abun ya faru na kasa mantawa, kuma ban san gidanku ba, na gaya wa mamanmu ta din ga yi mini faɗa, ba ina sane na tureki ba ta ce in nemi yafiyarki".
Ummi ta yi murmushi ta ce "Ai bakomai, na samu sauƙi".
"Amma ya aka yi ki ka ƙone a ciki da ruwan zafi?".
Ummi ta ce "Zubo mini yayi".
"To Allah ya ƙara afuwa"
Ummi ta amsa da "Amin".
Maryam ta liƙewa ummi, sai dai ummi sai ɗari-ɗari take yi da ita, saboda ba ta son wani abu ya haɗa su tayi mata tijara da tashin hankali, saboda ita bata iya faɗa ba, maryam kuwa dage ce, akwai masifa.
Ga maryam da azabar kashe-kashen kuÉ—i, banda kayan ciye-ciye da take zuwa da su.
Komai za ta ci sai ta bawa ummi, ummi kuma ta ce ba zata ci ba.
Tun tana É—an É—ari-É—ari da ita, har ta É—an fara sabawa da ita kaÉ—an.
Can gida kuwa kawu yahaya ya sanar musu matarsa an yi mata aiki, an ciro Æ´a mace, sai dai likitoci sun ce sai matar ta huta sosai za azo dubiya. Saboda yana gudun su zo barka, Iya ta faÉ—i wani abun, da zai yi wa ummi mummunan tabo a nan. Dama kuma gashi ba shiri suke yi da farida ba, dan ita da Iya kar ta san kar ne, iyan za ta iya zuwa ta bar ta a falo ta cigaba da sabgoginta ba tare da ta bata ko ruwa ba.
Ummi ta É—auki soyayyar duniya ta É—orawa jaririya noor, idan uwar ta yasar da ita, sai ta É—auke ta ta goyata, tayi ta jijjigata tana aikin gidan da ita a bayanta, dan ko da yarinyar ta fara dariya ummi ta fara yi wa.
Duk wannan soyayyar da ummi ke nunawa ƴar farida, bai sanya ta sassauta mata daga baƙar azaba da mugunta ba, da ita da ƴaƴanta da ƙanwarta, dan ummi ba sabon abu bane a wurinta, kaiwa ƙarfe ɗaya na dare ba ta kwanta ba, saboda azabar aiki.
Ga wani sabon salon zalunci, har maƙwabta sai su aiko ummi ta je, a sakata aiki, har wankin labulaye da carfet, sai a sakata, gyaran kaji da fige su, sai a saka ummi.
Makaranta kuma maryam na ta sake shishshigewa ummi, sai dai ummi ta fuskanci maryam ɗin na ƙoƙarin mayar da ita ƙarƙashin ta ta din ga mulkata ta zama kamar ƴar korenta, ummi ta cigaba da janye jikinta, maryam ta kasa samun damar hakan, saboda ummin na da mugun gudun abun hannunta.
Wasu lokutan haka ummi za ta zo ba ta ci abinci ba, maryam ta zo da abinci na alfarma amma fafur taƙi ci.
Kusan wata uku da haihuwar noor, kawu yahaya ya ce idan suka tashi suka koma sabon gida, sai su iya su zo, su ga noor, kuma su ga sabon gida.
Dan yana tsoron Iya ta zo ta saki baki ta faɗi wani abu da zata ɓata ummi, dan ya ƙudurce a ransa sai ya je yayi mata kashedi a kan ummi kan su zo, kuma gashi ba jituwa suke yi da iyalinsa ba, duk zuwa sai Iya ta ce an yi mata laifi, duk zalamar iya da son abun duniyarta ba ta ƙaunar zuwa gidan yahaya, wannan karon ma shi kawun ne ya takura su zo, kar abun ya zama surutu, an yi mata aiki ba su zo ba, ga kuma tariya a sabon gida.
Æangaren ummi kuwa sumul ta samu lafiya, kamar ba ta taÉ“a yin larurar sanyi ba, kuma lokaci zuwa lokaci, kawu yahaya ko bai sayi abu ya bata ba saboda matarsa, ya kan É—an bata kuÉ—i ta sai abun da take buÆ™ata.
Suka fara shirin tashi daga gidan, dama ƴan kayan ummi ba su da yawa tuni ta tattare su ta ƙulle.
Hatta su intee ummi ce ta haɗa musu kayansu, sannan ta koma ta haɗa na rahama, ga yau noor sai koke-koke take yi zazzaɓi na damunta, kai ka ce ummi ce ta haifeta, ta bata magani ta haɗa madara ta bata, sannan ta cigaba da aikin da ita a bayanta.
Suka gama haÉ—a kaya cif, washegari tun safe mota ta zo ta kwashi kayan su, zuwa sabon gida.
Gidan da suka koma, ƙato ne yafi wancan girma da kyau, a ɗan gaban unguwar da suke da yake, ƴan uwan su farida suka cika gidan, ummi na ganinsu suna ta binne-binne.
An canza furnitures, duk ta rabawa Æ´an uwanta tsofaffin, ummi kuwa da tsohuwar katifarta ta dawo gidan, sai dai hakan ko a jikinta, É—akinta shi ne na farko, baya cikin ainihin falon da zai sadaka da sashen kowa, Abdul sashinsa daban ba a cikin falon ba, da kitchen É—in sa da banÉ—aki, a can gefe É—aya.
Gidan ya ƙawatu yayi kyau matuƙa, ko ina ya sha flowers, sai ƙamshin sabunta yake yi.
Hatta ɗakin su intee kamar ɗakin wata amaryar, dr. Yayi ƙoƙari sosai da sosai, dama mutum ne mai hidimtawa iyalinsa sosai da sosai.
Bayan magariba ummi ta gaji matuƙa, har wani jiri take ji, ga ciwo da mararta take yi, wanda tun da take bata taɓa jin irin ciwon ba.
Tana ta ƙoƙarin gyara nata ɗakin, dan kuwa ba ta gyara komai ba, tana ta fama da aiki, da rigimar noor.
Ƴan uwan farida suna ta cewa ta karɓe ƴar ta daga hannun ummi, kar ta shafa mata baƙi da muni.
"Ke!"
Ummi ta waiwayo ta kalli rahama da ke tsaye.
Ta ce "Bani kuÉ—in nan da zobena"
Ummi tayi saroro ta ce "Wane kuÉ—in?"
"Ba ke kika haÉ—a mini kayana ba?"
"Eh nice" ummi ta amsa.
"KuÉ—in da suke cikin wardrobe É—ina, kuÉ—in anty farida ne"
Ummi cikin faÉ—uwar gaba ta ce "A'a anty rahama, ban ga kuÉ—i ba wallahi, kayanki kawai na haÉ—a miki a cikin akwatin da sauran kayanki a cikin jakunkunan da ki ka bani, dubu biyun nan ce kawai kuma kin É—auketa, amma ban ga kuÉ—inki ba".
"Ke rufe mini baki ko na dalla miki mari, kuÉ—in anty farida ne dubu hamsin"
"Wallahi wallahi anty rahama ban gani ba, ki cajeni ki caje kayana, wallahi ban É—auka ba" ummi tayi maganar jikinta yana rawa tana tuna irin tozarcin da aka yi mata lokacin da iya ta ce ta yi mata sata.
"Rahama ina kuÉ—in ne? Ta baki?"
"A'a fa sai kin zo da kanki, ta ce ita ba ta É—auka ba".
Farida ta ce "Ke, ina kuÉ—ina?"
"Anty ban ɗauka ba" ta faɗa kamar numfashin ta zai ƙwace, saboda fargaba da tashin hankali.
Ashar É—in da farida ta yi mata cikin tsawa ya sake gigita ta, ta ma rasa me za ta ce.
Shaƙeta rahama ta yi tana zazzaro mata ido ta ce "Zaki faɗa ko sai na kashe ki" girgiza kai kawai ummi take yi.