Sashe 117
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
PAID ADVERT
*Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Ɗan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir ɗin da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin sheƙin fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sanƙo, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ƙarfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuɓe su a kan lambar wayar su dan ƙarin bayani 07045971194 ko 08140450950*
45
Raihan ya rasa ta ina zai fara kare kansa ma, haka yayi shiru Alhaji ya gama faÉ—an ya kashe wayarsa.
Kamar wanda aka gayawa saƙon mutuwa, haka ya ƙarasa cikin asibitin, ya taimakawa ummi ta wanke baki, ya haɗa mata tea da dankali yana bata. Cikin ɗari-ɗari take ci, dan ta san ƙarshen abun ta amayar da abun da ta ci, ga yunwa tana ji sosai.
"MD ka ga wancan cikin ban san ma da shi ba, ban yi laulayi ba wannan kuwa sai wahala nake sha"
Yayi murmushi da ƙyar ya ce "Wancan kin ci bonus"
"Wai ya na ganka duk wani iri ne? Na san zaman asibiti da gajiya, ba daÉ—i shiyasa gara ka mayar da ni maiduguri"
Raihan ya ce "No, ba gajiya na yi ba, da ke da babyna kuna buƙatar kulawata. Ai gazawa ce in ce ki koma gida dan baki da lafiya, ni zan yi abun da ya dace na kula da ku"
Tayi murmushi ta ce "To aikin fa?"
"Shima duk zan iya"
"ÆŠan Aljannana, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, ya barmu tare har aljanna"
Ya amsa mata da Amin, ƙasan zuciyarsa yana fargabar hukuncin Alhaji, dan daga ji ya ɗau zafi sosai.
Yadda ta gama cin dankalin nan, sai da ta amayar da shi gaba É—aya, abun har tsoro yake bawa raihan, duk ta rame saboda laulayi.
Yana nan zaune tare da ita, har ta samu bacci, bayan wasu awanni ta din ga jin hayaniya kamar a mafarki. Ta buÉ—e idonta, ta ga Alhaji a É—akin tare da Salim, ga raihan a gefe ransa a haÉ—e sai kuma likita a tsaye da file.
A hankali ta tashi zaune, tana mamakin zuwansu ta ce "Alhaji sannu da zuwa"
Ya dubi Ummi ya ce "Sannu ya jikin? Dan Allah kalli yadda duk ta bi ta ƙare ta rame, meke damunta ne? Ko kuma duk tsiyataku da rashin mutuncinka ne ya sanya ta rame" Yayi maganar yana kallon raihan.
Likita ya ce "Ahh ba wani abun damuwa bane, laulayi ne na mata, ba ta iya cin komai shiyasa muka ajiyeta mu ke ta saka mata ruwa"
Alhaji ya ce "Ka rubuta mata sallama, gida kano zamu tafi, za a cigaba da kula da ita a can"
Ya mayar da idonsa kan ummi ya ce "Banda abunki ummi, gani menene amfanina? Ko dr. Ba ya nan wani abu ya haɗaku sai ki zo ki gaya mini, ni ƴa ta ce ke ba sirika ba, kawai sai ki biye masa ki tafi wani wurin ace ba a san ma in da ki ke ba? Kuma dan baka da kunya ka lallaɓa ka mayar da ita ka taho da ita nan ba wanda ya sani, hankalin mahaifinta na can a tashe bai san ina take ba, ka bani kunya" daga ummi har raihan aka rasa mai magana, ummi ba ta taɓa zaton Alhaji ya iya faɗa haka ba, saboda kullum fuskarsa cikin murmushi yake.
Haka aka sallami ummi, suka nufo kano, raihan ya sha faÉ—a a wurin Alhaji,kuma yayi shiru bai ce komai ba ummi gaba É—aya ta ji babu daÉ—i.
Asibiti suka zarce da ummi, aka cigaba da ba ta kulawa ta musamman, saboda suna tafe a hanya ma tana amai.
Alhaji ya kira dr. A waya ya sanar masa ya gano ummi, tana tare da raihan a maiduguri.
Dr. Ya ce ya haÉ—a shi da ummin a waya, Alhaji ya ce masa ba ta da lafiya, ba za ta iya amsa waya ba.
Dr. Ya ce a cikin satin zai shigo Nigeria, dan hakan yayi dai-dai da lokacin zuwansa hutu. Ya karɓi kwatancen asibitin, ya kira Abdul a waya, ya ce su je asibiti da shi da noor, su duba masa jikin ummi.
Ko da suka je, sai da Abdul ya yi wa raihan ƙorafin, meyasa bai gaya masa ba ya ga ummi.
Babban abun da ya bawa ummi mamaki, bai wuce yadda Salim da noor suke yi wa juna murmushi ba, kamar sun saba. Kuma a iya sanin ummi ba shi da fara'a ko kaÉ—an.
Noor ta ƙarasa gaban gadon ummi ta na yi mata sannu.
"Yaya ummi shi ne ki ka tafi aka neme ki aka rasa ko? To ƴan gagarawa ne suka samo wani abokin Abba, suka saka ya kira musu shi, aka gaya masa abun da ki ka yi, ya bi ba'asi ban san dai me suka ce masa ba, ya kira waya yana faɗa ya cewa yaya Abdul ya je gidanki ya duba masa ke dama ba ya samunki a waya, aikuwa dai ya gaya masa gaskiya, amma fa mun sha faɗa saura ke idan ya dawo dan ransa ya ɓaci"
Salim ya ce "Ba ki ga bata da lafiya bane?"
Ta ce "Au, haka ne fa, zumuɗi nake na ganta, ba ka san yadda na shiga tashin hankali ba da aka ce ta ɓata".
Yayi murmushi ya ce "I see"
Alhaji ya ce "Ai daga ita har shi, sun yi laifi, kuma ba zan matsa da bincike ba, sai dr. Ya dawo, amma fushi dole ayi fushi da su"
shi dai raihan ya rasa menene yake yi masa daɗi, ga rashin lafiyar ummi, ga faɗan Alhaji da yaƙi saurarensa.
Salim ya ɗauki Alhaji suka tafi gida, tun da yaje gida yake cigaba da faɗa a kan abun da ya faru, hankalin mami yayi mugun tashi, dan yadda ransa ya yi mummunan ɓacin nan, zai iya aikata komai dan kamar ƴar cikinsa aka yi wa haka ɗauki lamarin da zafin gaske.
Ta din ga kiran raihan tana jaddada masa, kar ya kuskura ya gaya wa Alhaji ita ce ta saka ya saki ummi.
"Mami na ji, ni ba zan faÉ—a ba, amma ummi fa?"
"Au kai sai ka bari ta faÉ—a É—in?"
"Mami ya zan yi, tayaya? Zan yi mata dole ne, tana kwance muna fama ba ta da lafiya, ba zama ta fahimci me nake nufi ba" mursisi raihan ya nuna wa mami ba zai tursasa ummi ba. Bayan ya kashe wayar ya kalli wayar ya ce "Mami ina fatan zaki fahimci cewa, ɗan adam duk ƙin da ki ke yi masa wataran zai iya yi miki rana, ko ki nemi alfarma a wurinsa.
Kwana biyu ummi ta É—an warware, ranar dr. Ya dawo, Alhaji dai tare da Salim suke zuwa asibiti, haka Hajiya ma take sintiri.
Tun da raihan yayi aure, Alhaji da Salim suke É—asawa saboda Alhaji ya jinjinawa Salim yadda yayi playing role É—in sa na babban yaya ga raihan ba tare da wata adawa ba. Kuma a hankali ya lura da ya rage fitina sosai da sosai, dan ko fita baya son yi suna tare da Alhaji.
Alhaji ya kasa shiru, sai da ya tambaye shi, dalilin canzawarsa lokaci ɗaya yayi murmushi ya ce "Alhaji kenan, ai ko dabba idan kana mutunta uwata zata so ka, balle ɗan Adam ni dama wasu lokutan babarsa ke sanyawa nake ja baya da shi, duk abun da yake faruwa ina sane da yadda mutunta da girmama mahaifiyarmu. Da na raka shi maiduguri ma, yadda dangin matarsa suka din ga yaba kamalarmu na ji daɗin hakan sosai, na ƙara yadda da zama mutumin banza ba shi da wata fa'ida. kuma ƙanina zai yi aure very soon zai fara tara zuriya, kuma yaransa namu ne, abun kunya ne a garemu yaranmu su taso su ganmu a irin wannan yanayin. Ina ta addu'a kuma ina jan hankalin Sagir ma. Abu na gaba rayuwar raihan da matarsa ta burgeni, da har na ji nima ina son yin aure, amma na san za a iya hanani aure saboda halina, duk ruɗin abokai ne dama, amma yanzu Alhamdilillah ina ta ƙoƙarin gyara kuskure na na baya, a cigaba da yi mana addu'a".
Alhaji ya ji daÉ—in kalaman Salim ya din ga saka masa albarka, tare da alwashin duk yarinyar da yake so ya sanar masa, zai nema masa aurenta, tun da matar na tuba ba ta rasa miji.
Daga haka ya ƙara janyo shi a jikinsa, da cigaba da rarrashin sa da yi masa nasiha.
Murna ta saka sai da ya bawa Hajiya labari, Hajiya ta din ga murna ta ce "Aini auro ummi cikin familyn nan ya zame mini alkhairi mai tarin yawa, ba abun da zan cewa Allah sai godiya, Allah ya ƙara musu zaman lafiya da kwanciyar hankali, ya ƙara haɗa kan zuriyarmu".
Yadda ummi ke ƙara girmama shi, yaya sama yaya ƙasa, mutuntawa ta kowane fanni, ga yadda ita ma ta ɗora da kyautatwa mahaifiyarsu, dama can kuma kan a aurota, ya san yadda take mutunta kowa a gidan, hakan ya sanya shi ma yake girmamata da jin nauyinta.
Dan wasu lokutan ta kan tsokane shi, da shi ne ɗan uwanta da mama ta faɗa, lokacin da suka je maiduguri, babu wasan ƙanin miji tsakaninsu sai girmamawa da mutunta juna.
A falon gidan dr. Kuwa, ga raihan, ga ummi, ga dr. Da Alhaji, sai Abdul da Salim.
Alhaji ya kalli raihan ya ce "To ayi ta ƙeƙe da ƙeƙe a gaban mahaifinta ka faɗi saki nawa ka yi mata? Tun da dama abu kan ya faru ake magance shi, da ka sanar akwai matsala ne sai a sasanta ku, kan a kawo nan amma tun da aka zo nan, sai ayi ta ta ƙare.
Raihan ya yi shiru bai ce komai ba.
"Ba magana nake yi maka ba?"
Kamar zai yi kuka ya ce "Alhaji wallahi ban saki matata ba, idan ma na saketa a na mayar da ita"