← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 134

Sashe 8

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai yayi mamakin yadda iya ke ta hantarar mariya, tana cikin alhinin mutuwar mijinta, ga Æ´an uwanta a gida, amma iya na ta masifa da nanata ta kashe mata É—a.

Ya dubi Iya ya ce "Haba iya, haba iya da wanne za ta ji? Ya za ayi ta yi sanadiyyar mutuwar mijinta, mijin da suka yi auren soyayya, shekara bakwai tare, ko sulhu ba a taɓa yi musu ba, ki ce ita ta kashe shi, ga ƴan uwanta a gida ai babu daɗi"

"Yahaya, ni fa nake zaune da yarinyar nan, ni na san abubuwan da take aikatawa, azabar son zuciyarta ya sanya ta hura masa wuta ya tafi neman kuɗi, gashi nan ya mutu a banza, yaron nan haƙurin zama yake yi da ita"

Yahaya ya ce "A'a iya, idan na zo fa muna hira da bashir, a bar kaza cikin gashinta kawai banda tone-tone, amma batun ace mariya ce ta kashe mijinta bai taso ba, dan Allah ki bari ta ji da alhinin da take ciki"

Kasancewar yana da abun duniya, domin kuwa lecturer ne shi a kano, kuma albashinsa da tsoka, dan haka yana yi wa iya sha tara ta arziki, a dole ta ja bakinta ta yi shiru.

Wasa² magana har waje wurin maza, iya ta tubure tana cin mutuncin sirikarta, wai ita ta kashe mata ɗa.

Yayan mariya har cikin gidan ya shiga, ya yi wa mariya wankin babban bargo.
"Irin tarbiyyar da aka baki kenan dama mariya? Irin zaman da ki ka yi da mijinki kenan, ki kasa zama da shi a yadda yake, ki hura masa wuta ya tafi ajali ya riske shi, kuma gashi an ɗora miki, an ce ke ce sila. Mariya kin ɓata wayonki, wannan ba tarbiyyar gidanmu ba ce ba, kuma ahalinsa ba zasu taɓa mantawa da abun da ki ka yi ba". Kasancewar yana cikin manyan yayyenta, kuma tana bala'in tsoronsa, dan haka ba ta iya kare kanta ba sai kuka, ga shi a gaban mutane ya din ga yi mata faɗa, mariya ta rasa da wanne za ta ji.

Iya kuwa ta samu damar cigaba da ƙullawa mariya sharri a wurin yayanta.

Yahaya ya tsawatar, saboda shi É—an boko ne, ya ce ba zai yiwu a saka mariya a gaba ace ita take aikata duk wannan laifukan ba. Idan ma haka ne tana matsa masa kan ya rasu yanzu yana ina? Kuma ai mijinta ne, tana da right na ya yi mata abun da take so.

ÆŠakinta ta shiga ta zauna, tayi kuka, tayi kuka, har zuciyarta ta fara raya mata ko kashe kanta zata yi ta huta da wannan azabar.

Ummi ta zo tana kuka ita ma, dan tun ana yi mata faɗan nan ummi take tayata kukan, ta din ga share mata hawayen tana cewa "Mama ki yi haƙuri, ki daina kuka" ita kanta yayar mariya, ta san mariya ba za ta aikata haka ba, yadda iya ke yi wa mariya a gaban su, ba ƙaramin ƙular da ita yayi ba. Sai dai su al'adar gidan su, muddin ak kawo ƙararka daga waje, ba a taɓa goya maka baya, balle kuma a gidan aure, idan miji gutsurar namanki yake yana ci, sai ace ki je ki cigaba da haƙuri, wataran sai labari, kowa haƙuri yake yi.

Maryam ta tambayeta ina samirunya, ta ga duk babu? Mariya taƙi gaya mata, ta shashantar da zancen.

Bayan kwanaki uku da share zaman makoki, Æ´an nesa suka watse, sai masu shigowa jefi-jefi gaisuwa, yayar ta ta zauna da ita, ta É—an din ga É—ebe mata kewa, zuwa kwana arba'in, aga meye abun yi.

Gaba É—aya mariya ta gama fita daga hayyacinta, kai daka ganta ka san tana cikin alhini, ko abincin kirki ba ta iya ci. Salla kawai take iya yi, wanka kansa sai ta yi da gaske take iya yi.
Daga kwanciya sai kuka, amma hakan bai sanya ta tsira daga tashin hankalin Iya ba, ga kyarar ummi da take yi kamar ba jininta ba, wanda hakan ya fara tunzura yayar mariya maryam.

Kwanan bashir goma sha huÉ—u da rasuwa, rabi'u ya zo yayi sallama, suka amsa ya sake yi musu gaisuwa.

Ya ce wa iya "Ina mariya, ina son zan yi magana da ku ne"

Iya ta ce "Dole ne sai ta nan? In dai abun da ya shafi É—a na ne, gaya mini kawai ina jinka"

"Wane irin a gaya miki kawai? Ai tana da hakkin sanin menene ita ma, tun da mijinta ne" yaya maryam tayi maganar a zuciye kamar ta kife iya da mari, saboda a zamanta ɗin nan ta gane lallai mariya tayi zaman haƙuri.

"Rashin kunya zaki yi mini?"

"Ba wani rashin kunya, maganar gaskiya ce ai. Ke mariya fito za ayi magana"

Jiki a sanyaye mariya ta fito cikin hijjabi, ta zo ta samu wuri ta zauna.

Suka sake gaisawa da mariya, yayi mata gaisuwa, Sagir yayi sallama ya shigo suka amsa masa, shima ya samu wuri ya zauna.

Rabi'u ya ce "Yauwwa, dama ni na yi masa magana tun da yana gida na ce masa ya shigo, Iya kamar yadda ki ka roƙi na tafi da bashir lagos, ya nemo arziki, to mun sauka Lagos lafiya".

Maryam ta ce "Amma ki ka ce mariya ce ta ce lallai sai ya tafi neman kuÉ—i"

Iya a fusace ta ce "Wai wace irin mara tarbiyya ce, ƙarya nake yi kenan, matsin da take yi masa ya sanya na yi masa magana, ya tafi da shi"

Maryam ta ce "Amma ai ba haka ki faÉ—a ba, ki ka saka yayanmu ya din ga ci mata mutunci a gaban mutane, wallahi ki ji tsoron Allah"

Rabi'u ya ce "Dan Allah ku yi haƙuri, ku saurare ni ku ji, bayan zuwanmu Lagos, mun fara sana'ar fawa da balarabe, kasancewar ba shi da account, yake tarawa a account ɗina, ya ce mini mariya ta sayar da kayanta, ta bashi kuɗin, amma shi a bashi ya karɓa, zai mayar mata da kuɗinta, dan haka ba laifi ya tara kuɗi, riba kawai kusan dubu sittin, uwar kuɗin sa da ribarsa da komai, kusan dubu ɗari biyu, basussuka da sauran su, duk na biya masa dubu ɗari da arba'in ne suka rage, mun taho gida da niyyar idan mun zo na cire kuɗin na bashi.

A hanya ƴan fashi suka tare mu, suka ƙwace mana kaya, da kayan tsarabar sa, har sun yi gaba ya tashi kan su ƙarasa barin wurin, shi ne suka harbe shi a ƙirjin sa, kan ya rasu ya ce: kar a raba gado, sai an biya mariya kuɗinta na kayanta, da sauran kuɗin da take bin sa" Ya kalli ummi da ke zaune tana bin su da kallo, sannan ya kalli mariya ya ce "Ya ce; ki kula masa da ummi, sannan ki yafe masa" yana faɗar haka mariya ta sanya tafukan hannunta ta sake fashewa da kuka.

"Ni bai ce maka komai a kai na ba?" Iya tayi maganar tana kallon rabi'u.

"Yana cikin maganar yayi kalmar shahada, ummin dai ya fi nanatawa"

Ta share hawayen da ke shirin zubo mata sannan ta ce "Ba wani zancen tana bin sa kuÉ—i, ni ban yi wannan maganar da shi ba, dan haka ka je ka É—ebo kuÉ—i ka kawo mini"

Maryam ta ce "A kawo miki kuÉ—i kiyi me da su? Ai kuÉ—i na magada ne, kuma sai mariya ta gama idda za a raba gado, saboda a tabattar da babu ciki".

"Ba dai ciki ba, shekara nawa rabonta da haihuwa, tun daga wannan mummunar yarinyar fuska kamar turotso, ba ta sake haihuwa ba, ba haihuwa take ba, dan haka ba ta da wani ciki. Wa ya sani ma ko balaraben baya haihuwa"

"To me ki ke nufi, ummin ba Æ´ar ku ba ce ba? Wai ke matar nan anya musulma ce ke? Kin yi imani da Allah kuwa?"

Sagir ya ce "Ke malama kar ki sake ki zagar mana uwa, na gaya miki" miƙewa maryam ta yi ta ce "Na zageta ɗin, ka yi abun da zaka yi. Azzalumar tsohuwa mara imani da tausayi, ashe ke ki ka ingiza ɗanki ya tafi neman kuɗi, amma kin saka yarinya a gaba, kina ta yi mata sharri, to wallahi dan kanki, ummi kuma idan ba ƴar ku ba ce, sai ki fita neman ubanta" nan da nan hayaniya ta ɓarke.

Mariya ta tashi ta ce "Dan Allah yaya maryam ki yi haƙuri, in dai kuɗi ne, ni babu bashi tsakanina da baban ummi, na rasa mijina balle abun duniya? Tumunin takabar ma na yafe, a bawa ummi hakkinta, in ɗau ƴa ta in koma in da na fito dan Allah" tayi maganar cikin matsanancin kuka, tare da jan hannun ummi ta tafi ɗaki.

Shi kansa rabi'u yayi mamakin rashin arzikin Iya, kawai ta É—orawa mariya karan tsana.
Ta sake jaddawa rabi'u ya kwaso kuÉ—i ya kawo mata, me balaraben ya mutu ya bari, da za a tsaya wani rabe-raben gado.

Maryam kuwa da kanta ta tafi tasha, ya bayar da saƙo zuwa gida, a kan lallai a cewa yayansu ya zo, akwai matsala.

Ko abinci ba a basu, maryam ita ta din ga cefane tana ciyar su.

Yayan su mariya ya dira a garin, Iya sai da ta yi mamakin ganinsa, maryam ta ja shi, ta ce masa akwai matsala cigaba da zaman mariya a gidan nan, tana kallon irin zaman da mariya take yi a gidan, nan ta kwashe komai ta gaya masa.
Abun ba ƙaramin ɓata masa rai yayi ba, wani irin tausayin mariya ya kama shi, karon farko da ya ji zai goyi bayan ƙanwarsa, dan haka ya yanke cewa kawai zasu ɗauki mariya da ummi su tafi.

Dan haka ya je ya samu iya ya ce mata, washegari da safe zasu yi sammako su tafi Maiduguri, yaso su zauna su cigaba da gaisuwa, tayi takaba a É—akin mijinta, amma wasu dalilai ya sanya sun yanke shawarar su tafi da ita gida kawai.

Iya ta ce "Shikenan babu laifi"
Chapter 8 · 0% Book details