← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 134

Sashe 130

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba aurenki zai yi ba yanzu? Dole yayi miki izza. Ke fa miji ba abun wasa bane ba" ta din ga yi mata faÉ—a.

Ummi ta ƙara ɗaura aniyar, raba noor da Farida har zuwa lokacin da za a saka auren noor ɗin, saboda kar ta ɗorata a kan mummunar ɗabi'arta na raina miji da yin asiri.

Ummi ta kira Alhaji a waya, ta din ga yi masa godiya, tare da yi masa adduo'i masu daÉ—i.

Ummi ta tara kuÉ—i da suturu, da sauran abubuwa.

Farida kuwa tayi watsi da dr., Shi ma yayi watsi da ita ya daina shiga sabgarta kausar ma ta biye mata ba sa kula shi.

Yau yana gidanta, tana ta cika tana batsewa, ta same shi a fall ta tsaya a kansa ta ce "Malam yaushe za ka dawo mini da Æ´a ta ne?"

Ya É—aga kai ya kalleta ya ce "Ke da noor, sai lokacin aurenta, ta bar gidan nan kenan na bawa mariya ita"

"Wallahi ba ka isa ba, ai ba ita ta haifa mini ita ba, da zaka bayar mini da Æ´a"

"Ni ban isa na ƙwace miki ƴa ba, halinki da ki ke nuna mata ne, ya sanya ta guje ki ita ma" za ta yi magana wayarta ta fara ringing.

Ta É—aga wayar ta yi sallama.

"Farida kina ina, ki yi maza ki zo asibitin murtala emergency, Rahama mijinta ya ƙonata da ruwan zafi da ita da ƴar da take goyo"

Farida ta dafe ƙirji ta ce "Ruwan zafi me tayi masa?"

"Wai faÉ—a suka yi, ta tafi tsakar gida tana girki, ya zageta ta rama, ya fito yayi balla da kurfotin gabanta da tafasasshen ruwa a kai, da garwashin duk ya watse musu a jiki ita da Æ´ar"

"Innalillahi na shiga uku" tayi jifa da wayar tayi É—aki tana salati.

Kiran sallar la'asar ake yi dama, dr. Ya fice sallar isha'i, dan bai san me aka ce mata a wayar ba.

Daga sallar isha'i, ya tafi gidan mariya.

Ya tarar ta idar da salla tana zaune ta yi shiru.

"Ya dai, na ganki sai a hankali, ina noor ne?"

"Tana gidan ummi, ai noor ta gujeni saboda sun yi jarirai"

Yayi murmushi ya ce "Noor an kusa girma, Alhaji Tahir ne yayi mini magana, wai su na riƙo Salim yana so, na ce zai sha shiririta"

Mariya ta ce "A'a kar ka ce haka, abu namu Æ´a ta wa É—a na wa, za ta yi hankali in sha Allah kan lokacin"

"Wane lokaci kuma, shekara É—aya ne kawai fa, tana gama secondary school ne suke so"

Mariya ta yi dariya ta ce "Allah ya sa zamu gani"

Ya É—an kalleta ya ce "Kamar akwai magana ko?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

"To ya aka yi?"

"Dr. Tun muna waccan ƙasar kamar ban kuma al'ada ba fa"

Yayi dariya ya ce "To me ki ke so in ce?"

"Koma meye ka ce mana"

Dr. Yayi dariya ya ce "Maman ummi rigima, kin fi ni sanin meyake faruwa ai"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai ciki ne da ni?"

Dr. Ya kashingiÉ—a yana dariya, gaba É—aya ta ruÉ—e "Haba dr. Ummi na jego nima a ganni da ciki, na shige su"

"To laifina ne? Ni dai ina so ina murna Allah ya raba lafiya, kowa ya kalle ki fa zai gane kin ƙara haske sosai" gaba ɗaya ta rikice, wai abun kunya ne, shi kuma ya din ga yi mata dariya. Gaba ɗaya ya manta da a gidan farida.

Ummi na ɗaki tana ta yi wa noor nasiha, a kan maganar salim, ta ce mata ita tana son sa amma tsoron auren take yi, ummi tana ta lallaɓata, dan sun yi magana da dr. Kuma ta san zai kira noor ɗin ya tambaye ta.

Anty Maryam ta shigo ɗakin ta ce "Ummi, kin yi baƙuwa, sai wani harare-harare take yi, ban san me aka yi mata ba, amma da alama ƴar uwar mai gidan ce, suna kama da shi"

Ummi ta yi murmushi ta ce "Anty ki ce ta shigo".

Mintuna kaÉ—an sai ga Maryam ta shigo.

Ummi ta ce "Sannu da zuwa, yanzu ki ke tafe?"

Ta ja tsaki ta zauna.

Noor ta ce "To, ikon Allah"

"Noor kawo mata ruwa da yaran ta gansu"

"Ai fa, an samu abun da ake so, an samu daular da ake kwaÉ—ayi tashin farko an zubo yara biyu, yaran da aka ce babu kalarsu a danginmu"

Ummi ta yi dariya ta ce "Ai abun alfaharinku ne, kun samu iri a dangi. Kuma ƴaƴa biyu sai matar so ba kwaɗayayyi ba, abun alfaharinku ne, ƙaninki akwai himma, ko kuma maybe daga ni ce"

"Ummi ni ki ke gaya wa haka?"

"Ke fa ki ka fara, wai kwaÉ—ayi? Ke in kwaÉ—ayi ne kawai ya kawo ni gidan nan, da ban kai haka a cikinsa ba"

Noor tayi sallama, ummi ta amsa, ta miƙawa maryam yaran, maimakon ta karɓa ta ce "Ba shakka, dole mami ta ce akwai lauje cikin naɗi a wannan yaran, ba zata taɓa karɓar su a matsayin jikokinta ba"

Ummi ta ce "Noor mayar mini da ƴaƴana wurin Anty"Noor na fita ummi ta ce "Kar Allah ya sa ku karɓe su a matsayin jikokin, ku mayar da su in da suka fito, tun da ubansu ya san nasa ne shikenan.
Dama ni ban ce ta ƙaunace ni dole ba, tun da ba ku ku ka halicce ni ba. Ni yanzu a duniyar nan da a so ni da a ƙi ni duk uwar ubansu ɗaya.
Babu yadda ban yi ba wurin yi wa mami biyayya, da girmamata amma ba ta gani, a gaban uwata saboda rashin ta ido, take cewa wai yara ba na ɗan ta bane, da yake uwata ba zuciya ce a ƙirjinta ba ko? Maryam da zan baki shawara da kun daina jayayya da ikon Allah, ni da raihan ajiyar Allah ne mutu ka raba. Idan ku ka cigaba da takurawa aurena ko kun raba aurena da raihan, zan cigbaa da rayuwar aure da shi ina haihuwa ko da aure ko babu, dan a yanzu ba wani ƙalubale ko abun kunya da ba zan iya fuskanta ba.
Zaman gidan raihan, da zazzago Æ´aÆ´a yanzu na fara, idan kin ga dama daga nan ki je wurin mami ki yi mini wani sharrin ke ta shafa da ke da ita"

Maryam ta miƙe ta ce "Ummi, mamin ki ke gaya wa haka?"

"Idan tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba, jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba. Na yi iya yi na, na gaji, ba zan cigaba da cusa kaina in da ba a ganin kima ta ba. Kuma wallahi idan kuka cigaba da uzzura mini, hakkina zai fara bibiyarku ai ke ma mace ce, kuma a gidan wani ki ke aure, a sannu kema zaki haÉ—u da dai-dai ke".

Ta fice ta bar ta a É—akin a tsaye.

Farida kuwa hankalinta ya tashi, saboda yadda ta je ta tarar da rahama, a asibiti, jikin yarinyar duk ya saɓule, haka na rahama cikinta, fuskarta da ƙafafuwan ta duk sun ƙone ƴan sanda sun kama mijin nata.

Ta din ga kuka tamkar za ta zare.

Ummi kuwa duk da furucin da Maryam tayi mata, ko a jikinta ta miƙe ƙafa ta cigaba da sabgoginta a gidanta.

Hausawa suka ci idan kana da kyau, ka ƙara da wanka, ummi ta san in dai ɓangaren kula da mijinta ne, to tana da kyau ba a magana a ɓangaren kula da raihan.
Amma duk da haka, maganar hausawa gaskiya ce, dan haka ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, wurin lalubo lambar Amina Gachi, CEO beenad herbal center, mussaman ita da taɓa fama da ciwon sanyi, kuma galibi ciki ya kan tayar da ciwon, dan haka nemi Amina gachi, domin shiryawa koma wa ɗakin mijinta.

(Bari na baku bayani, beenad herbal center, ba iya maganin sanyi suka ƙware ba, suna bayar da magunguna daban-daban dai-dai da matsalolin ku, damun kawo daidaito a gidajen auren ku.
Suna da kaya kamar haka;
Shedaniyar gumba
Gumba mai saying
Garin mai kabbara
Mai dalalan miyau
Wayyo dadi
Zumar kwakwa
Zumar ridi
Zumar dabino
Zuma mai ma'ul ijaba
Farin jini
Gumba kalla kalla da dai sauran su
A BEENAD HERBAL suna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kuka zaba
Ga kuma maganin slimming
Gyaran nono
Maganin hips
Maganin Kara kiba
Da dai sauran su.
Kayan mu tested and trusted ne
Suna maraba da masu siyan Daya ko sari
Suna Nan cikin garin kaduna
Kuma suna tura Kaya duk inda kike da yardar Allah

AMINA GACHI
07034404975
CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE
KADUNA
Phone no 07034404975.

Da labarin abun da ya faru da rahama ya zo kunnen ummi, hankalinta ya yi mummunar tashi, dan sai da ta yi kuka, dan yadda Abdul ya gaya mata abun babu daÉ—in ji, ummi ta ce raihan ya bar ta je ta dubata, ya ce ba zata fita ba sai tayi arba'in.

Yaran raihan kamar ana hura su, dan baya wasa wurin kula da su, ummi na cin abinci mai gina jiki, da zai samar mata da ruwan nono, kunu masu kyau da kayan marmari, su kuma yaran ga isashshiyar madara yana saya, kan su yi arba'in suka cika ɓul-ɓul gwanin sha'awa.

Can gagarawa, aka samu wani irin maimakon ruwan sama, kamar da bakin ƙwarya, ga ƙarfi ga kuma iska hakan ya sanya rufin ɗakin iya kwashewa.

Dama dr. Ne ya bayar da kuɗi, a gyara mata ɗakin ta saka aka yi rufi ta karɓe sauran kuɗinta ta cinye, sai ledar ɗaki da ta saka.

Iska ta yaye kwanon, ruwa ya din ga zuba a kanta, ruwa ya jiƙa tsohuwar ƙasar da aka yi ginin ɗakin da ita, ita ma ta zube wani ya danneta, ban da katakon rufi da ya din ga ƙwalo mata a ka.

Gashi itakaÉ—ai take kwana babu kowa a wurinta, dan haka babu wanda ya san abun da ya faru sai washegari.

Babu wanda yayi zaton za a ciro iya da rai, haka aka kwashe ta aka yi asibiti da ita, tamkar an jiƙa kaza a ruwa, ga jikinta duk ƙazantar zawon wahala da tayi, kan nan kamar an suɗe ƙwallon giginya, duk ta zama abun tsoro.
Chapter 130 · 0% Book details