← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 134

Sashe 49

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mami ta ce "Laaa ka amsa kuwa? Kema meyasa ki ka gaishe shi? Ƙaninku ne fa, ƙanin maryam ne Raihan ne.
Kai kuma ka amsa kamata yayi fa ka gaisheta" ya wani basar.

Ummi ta ce "Ƙyaleshi mami, ai dama su Allah ya bawa girman" tayi maganar tana ɗaga niƙabin fuskarta.

Sai yanzu shima ya ganeta, ranar saukarsu da maryam a makaranta.

Mami ta ce "Ya wani je ya tara gemu, yafi kowa girma kai ka ce wani babba ne, ni wannan gemun ina tantama idan ba mai ya shafa ya fito ba, dan ga gemun nan dai, amma hankali da saura".

Ummi ta yi murmushi ta ce "Girma ya riga hankali kenan" sai da ya É—an buÉ—e baki jin abun da ummin ta faÉ—a.

Mami ta ce "Eh mana, ya  makaranta ummi?".

Ummi ta ce "Mami makaranta muna jiran result"

"Masha Allah, lokaci ba wahala har kin gama ummi, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi, to ya batun aure kuma? Ko invitation ki ka kawo mini?".

Ummi ta sunkuyar da kai, tayi murmushin yaƙe ta ce "Tukuna dai mami"

Mami ta ce "Ya salam, Allah ya kawo nagari ummi, yanzu fa maryam kusan shekarar ta bakwai da aure, ke kuma shiru duk Æ´an islamiyyar ku sun yi aure, saura ke, amma kar ki damu komai lokaci ne"

Ummi ta ce "To mami, bari na yi alwala dan Allah"

Mami ta ce "To shikenan ba damuwa, je ki yi"

Ummi na tashi raihan ya kalli mami ya ce "Dan Allah mami fisabilillahi meye na tambayar invitation ta kawo miki? Da shi ta kawo miki ai ba sai kin tambaya ba, kin ce shekarar maryam bakwai da aure ita ba ta yi ba, kin dawo kin ce tayi haƙuri lokaci ne, kamar fa kin mari mutum ne kina sane sannan ki ce yayi haƙuri".

Mami ta ce "To uban tsari, ai da tausayi yakamata ace ita ma ta tashi haka, in da take tana shan wahala, matar yayan babanta ke wahalar da ita, shiyasa nake tambayarta ko auren ne ya zo, ta huta".

"Matsalarku kenan mata, kune maƙiyan kanku, ladan ake rubutawa mace idan ta azabtar da ɗan wani? Kuma duk tausaya matan da ki ke, tun da dai ba ki samo mata mijin nan ba, ai sai ki yi mata addu'a, is like an insult at times, ka tambayi mace maganar aure, ni idan mace ne faɗa za ayi da ni"

Mami ta ce "Kai,tashi ka je mini aike na uban tsari".

"To É—aukko kayan, ki haÉ—o da kuÉ—in shan mai".

"Duk kuÉ—in da babanka yake baka, sai ka damfareni dan zan aikeka, to ba zan bayar ba".

Ya kashingiÉ—a ya ce "Mami idan kina son aiken nan a kan lokaci, ki bayar da cin hanci " tashi mamin tayi tana hararsa.

Hakan yayi dai-dai da fitowar ummi, fuskarta a jiƙe da ruwa, gaban gashinta duk a kwance, gashin girarta ma tamkar za su haɗe.
Fararen idanuwanta suka bawa brown ɗin ƙwayar idonta fitowa sosai da sosai.
Ƙwayar idonta yake son kalla, domin tabattar da kalarta, sai dai bata bashi damar hakan ba, dan mayar da niƙabin ta rufe fuskarta, ta tayar da salla.

Mami ta dawo falon da ATM É—inta, tana yi wa Raihan kashedin ya je ya dawo da wuri.

Ya karɓi ATM ɗin yaƙi tashi, ummi ta idar da sallar, tayi Addu'a ta cewa mami za ta tafi, tashi yayi ya riga ummi fita.

Mami ta ce sai ta tsaya ta ci abinci, amma ummi ta ce sauri take yi.

Ta ajiye wa mami kyautar kwalbar turaren humra.

Kuɗin motar da ta bawa ummi ma, ƙin karɓa ta yi, kuma da ganinta ka san tana buƙata amma mursisi taƙi karɓa ta tafi.

A babban falo ta tarar da shi, yana taje sumar kansa.

Har zata fita ya ce "Ki tsaya mu tafi tare na ajiyeki ko a titi ne"

Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a na gode sosai, zan ƙarasa" bai kuma ce mata komai ba ta fito daga falon.

Ta fita harabar gidan, hakan yayi dai-dai da fitowar wata babbar mace, ta sha ado da lace blue, hannunta da wuyanta duk gold.

Wani matashi yana biye da ita, kai da ganinsa ka ga É—an shaye-shaye.

Da sauri ummi ta ƙarasa in da matar take, ta ɗaga niƙabinta ta durƙusa ta gaisheta.

Matar ta faÉ—aÉ—aÉ—a murmushinta ta ce "Ummi yau kece a gidan, ba dan Allah yasa na fito ba tafiya zaki yi bamu gaisa ba?"

"Ba haka bane hajiya, a gurguje na shigo ne, kusan kullum ta hanyar nan nake bi, shiyasa na ce yau dai bari na shigo"

"Eh amma zaki tafi bamu gaisa ba ummi, ya gida ya makaranta?"

Ummi ta amsa da Alhamdilillah.

Hajiya ita ce uwar gidan mami, tun lokacin maryam na nan, tana son mu'amala da ummi saboda nutsuwarta, amma ummi ta janye jikinta ta daina zuwa gidan ma, saboda ba a ga maciji, tsakanin mami da Hajiya.

Ummi ta gaida Salim da suke tare da hajiya, ya amsa mata sama-sama.

Hajiya ta ce "Ummi kin yi aure ne?" Ummi ta girgiza mata kai.

"Ai da kin yi aure ban sani ba, sai mun yi faÉ—a".

Kamar an jefo shi, ya dafo kafaɗar hajiya yayi ƙasa da murya ya ce "Ku daina yi wa mutum irin wannan tambayar babu daɗi"

Hajiya ta yi murmushi ta ce "To babban mutum".

"Biki zaki je kenan?"

Ta ce "Eh, Æ´ar set É—inmu ke auran É—a"

Raihan ya ce "Shiyasa ki ka sha kwalliya, kamar ƙawar amarya mu ga jakar" ya karɓi jakar hajiya ya zuge.

Ya girgiza kai ya ce "Allah sarki Alhaji, an ɗebi kuɗinsa za aje ayi liƙi, to nima bari na ɗebi rabona" ya zura hannunsa ya ɗebo kuɗi ya zura a aljihunsa.

"Raihan abun har da gori, sai ka gayawa duniya kuÉ—in babanka ne"

Yayi dariya, ya ce "A dawo lafiya"

Ummi ma ta ce "Hajiya bari na tafi, a dawo lafiya "

Hajiya ta ce "A'a ummi, shigo mu fara aniyeki, sai mu ƙarasa wurin bikin"

Ummi ba za ta iya jayayya da hajiya ba, dan haka ta ce "To na gode"

Har ummi ta juya zata bi su ya ce "Eh ba shakka, ba zaki hau babur ba sai mota shikenan ai".

Lokacin suna Islamiyya, Maryam bata da aiki sai bayar da labarin Muhammad Raihan, barkwancinsa da kuma tsokana, tsokanar ma irin mai cika cikin nan.
Dan haka ummi ba ta waiwayo ba, tayi murmushi ta bi bayan su Hajiya.

Ayshercool
08081012143
Whats app only please 🙏
    *CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P22

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books É—ina, da free pages duk akwai a kan watpad account É—ina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

22

Raihan ya nufi in da babur É—in sa yake, ya É—auka ya fita daga gidan.

Suna tafe suna taɓa hira da ita da Hajiya, duk da ta kasa sakin jiki da hajiyar sosai, saboda yadda take matuƙar jin nauyinta.

Har kan layinsu suka kai ta, ummi ta yi ta musu godiya, sannan ta sauka ta nufi gida.

A harabar gidan ta tarar da Abdul hannunsa riƙe da waya. Yana ganinta ya tsaya yana jiran ƙarasowarta.

"Yaya ummi ina ki ka shiga ne?".

"Na É—an biya wani wuri ne, meyafaru?"

Maama sai faɗa take yi, intee ce aka dawo da ita,  wai ta kuma yin ɓari, zasu tafi asibiti zata bar miki sallahu baki dawo ba.

Ummi a ranta ta ce 'Ga kausar a gidan, ita ba za a bar mata sallahun ba'

A zahiri ta ce "Subhanallah, ubangiji Allah ya bata lafiya".

Ya amsa da "Amin, Allah ya taimake ki sun tafi, yanzu na dawo daga kaisu, kafin su dawo na san ta huce ba za ta yi miki faÉ—a ba".

Ummi ta ce "Haka ne, bari na yi sauri na shiga ciki"

Ta ƙarasa ɗakinta, ta yi wanka a gurguje, ta canza kaya ta saka hijjabinta na zaman gida, ta nufi kitchen.

Ta tarar da noor tana wanke-wanke a kitchen.

"Mama aiki ki ke yi haka?"

Noor ta ce "Eh, rage miki aikin nake yi, na san a gajiye zaki dawo, na ɓoye miki abincinki a ƙarƙashin dining, kar a cinye ba ki ci ba" tayi maganar cikin iyayi.

Ummi ta yi murmushi ta ce "Na gode sosai mama, bari na je na ci abincin, in zo mu É—ora abincin dare"

Noor ta ce "Kije ki yi bacci ma ki huta, zan yi miki greating kayan miya, na yi miki mopping"
Chapter 49 · 0% Book details