← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 134

Sashe 26

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dafaffen rogo ne, da ƙuli-ƙuli, ko wanke hannu ba ta yi ba, ta hau rogon nan da ci, saboda yunwar da take ji.

Ta gode wa Allah bayan ta kammala, duk da ba ƙoshi tayi ba, saboda ɗan kaɗan ne aka zubo shi a kwano.

Ta fito da kwanon tsakar gida, ta saka ruwa tana girgijewa, dan ba ta da ko omo.

Kamar wanda aka cillo, ta ga idiris ya shigo, babu ko sallama, hannunsa riƙe da jakar kayansa, wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta yi, saboda faɗuwar gaba da tsorata.

Babansa da yake bayan sa yayi sallama, ummi ta amsa ta tsuguna ƙasa ta ce "Baba ina wuni?"

"Lafiya ƙalau, ya gidan?"

Kai a ƙasa ta amsa masa da "Lafiya lau".

"Gashi nan, duk ranar da bai kwana a gidan nan ba, da safe ki je gida ki sanar da ni, zaka ga yadda zan yi da kai, mutumin banza wanda bai san abun da yake yi masa ciwo ba, an lallaɓa abun nan a rufawa juna asiri, ka daina ɗaukko mana magana, amma kana ƙoƙarin tona mana asiri" mahaifinsa yayi masa kaca-kaca, sannan ya tafi.

Ummi ji ta yi kamar tabi bayan sa, dan ta wani fannin zamanta ita kaÉ—ai babu Idris shi ne rufin asirin ta.

Ta ajiye kwanon da take É—aurayewa, ta nemi wuri can a tsakar gida ta zauna, tana ta addu'a a zuciyarta.

Idris kuwa ya cika yayi fam! Kamar ya fashe saboda tsabar baƙin ciki da takaici, fuskar ummi kawai idan ya kalla, ji yake kamar ya shaƙeta ta mutu, me zai yi da wata ummi, mummuna kamar ba bil'adama ba, aba kamar bayan garwa.

Tsaki yayi ya fito zai sake fita, aikuwa ta sake razana, kai tsaye inda take ya nufa, ta fara ƙoƙarin miƙewa tsaye, ya sanya ƙafarsa ya tankaɗata ta faɗi ƙasa.

"Shine ki ke je ki ka gaya musu bana kwana a gidan nan ko? Idan na kwana a gidan uwar me zan yi miki?"

Da sauri ta girgiza kai ta ce "A..aA'a iya ce ya aiko nemanka, wallahi ba faÉ—a na yi ba" tayi maganar cikin rawar murya.

"Rufe mini baki"  yayi maganar yana dukanta a ka da hannunsa.

Ta saka hannu bibbiyu ta dafe kanta, saboda jin zafin dukan da tayi, dan ma Allah ya taimaketa, tudun gashinta bai bari ta ji zafin sosai ba.

"Idan ki ka kuskura ko da wasa, ki kai ƙarata, sai na yanka ki, kuma azabar da zan gana miki, sai kin gudu da ƙafarki, ke baki san yadda na tsaneki ba ko? Zaki gani yanzu ai, banza mai kama da dabbobi"

Kame jikinta take sake yi, saboda gudun kar ya kuma dukanta, aikuwa sai da ya sake takata da ƙafarsa, sannan ya fita.

Sai da ta tabattar ya fita, sannan ta iya É—agowa a hankali, ta bi hanyar da ya fita da kallo.

Ta kalli jikinta, da ya ɓata mata da ƙasar takalminsa, tun da tazo gidan sau ɗaya tayi wanka, shi ma ba soso babu sabulu. Kayan jikinta tun wanda ta zo da su ranar da aka kawota, Iya ta ce za a aiko mata da kaya, amma shiru.

A hankali ta saka hannu ta karkaɗe ƙasar, tana takaicin yadda ya ƙasƙantar da ita ta hanyar takata da takalminsa mai datti da taɓo.

Tayi shiru tana ta saƙe-saƙe a zuciyarta, ta haɗe gwiwoyinta, ta kifa kanta, ta nemi hawayen ma ta rasa, sai zafi da ƙunar zuciya.

Yaya Hashim bai zo ya ganta ba, maman na'ima ba ta zo ba, tayi ta lissafin mutanen da take sanya ran su zo su ganta, amma basu zo ba.

***
A ɓangaren mariya kuwa, tuburan depression ya zame mata hauka, ga ta dai a nutse, sai dai babu cikekken hankali, wasu lokutan sai hankalin ya dawo, ta yi ta harkokinta, amma da abun ya juyo, sai daina cin abinci, ta daina magana. Duk wanda ya shigo da ƙaramin ɗa gidan, sai ta ce sai an bata umminta, ko ta ɗauki fulo tana yi masa wasa, ta ce ummi ce.
Idan Æ´an yara mata suka shigo gidan, suma sai tayi ta kiransu da sunan ummi. Ta ce "Yaya É—anlami, kalli yadda ummina tayi wayo ta girma".

Ya amsa mata da "Tubarkallah, ki yi ta yi mata addu'a, Allah ya ƙara rayata"

Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ba ummi ba ce, ummina baƙa ce mai kyau, bari in tashi in zuba ruwa in yi mata wanka, na goyata garin nan da sanyi"

Yayi saurin tashi, ganin da gaske tana ƙoƙarin kama ƴar mutane ta yi mata wanka, ya ce "Ki yi haƙuri in anjima sai ki yi mata wankan".

"To ai bana son babanta ya dawo ya tarar da mu, ba mu yi wanka mun yi kwalliya ba, kaga yana son turare da lallen da nake yi masa, baban ummina har kayan kasuwa yake sayo mana" haka tayi ta gwamutsa masa zantuka.

Yayi shiru yana kallonta, ba zai manta zuwan ƙarshe da yayi gidan Iya ba, da yaje da maganar neman alfarmar ɗaukar ummi, ko na ƴan kwanaki ne, dan hankalin mariya ya kwanta, ta fara samun matsala a ƙwaƙwalwa, amma ta kada baki ta ce Allah ya ƙara, hauka yanzu ta fara da yardar Allah sai ta din ga bi bola-bola hakkin ran ɗan ta ne.

Tun daga nan yayi alwashin ummi ko Æ´ar gwal ce ba zai kuma zuwa da niyyar a bashi ba.

Mama ta fito ta taya shi lallaɓa mariya, suka mayar da ita ɗaki, sai surutai take, tana basu labarin baban ummi da kuma ummi, sai dai ko da wasa ba ta zancen Iya, ko sauran mutanen gidan sai ummi da babanta.

Ummi ta sakankance idiris ba zai kwana a gidan ba, dan haka har ta hau kan tsurar katifar ta kwanta, sai dai ta kasa rufe idonta tayi bacci, saboda tana jin tsoro, ga gari hadari na ta haÉ—uwa, sai addu'a take Allah ya sa kar ayi ruwan sama.

Sai da hadarin ya haɗo gaba ɗaya tare da iska, kawai ta ga hasken tochlight a tsakar gida, inuwar Idris ta hango, ya tunkaro ɗakin. Ta runtse idanunta, tana fatan Allah yasa ba shi bane ba, sai dai ta ji ya mayar da ƙofa ya rufe, hakan ya tsananta bugun zuciyarta.

Ba ta san me yake yi ba, saboda ta rufe idonta, ƙafafuwanta ya taka ya ce "Ke dalla tashi" yayi maganar a matuƙar kausashe cikin rawar jiki ta motsa, ta tashi zaune, me zata gani Idris a tsaye a kanta tsirara kamar mahaukaci.

Ihu ta saki, ta runtse idanunta ta dafe kanta da hannayen ta.

"Dalla malama rufe mini baki, ki tashi na ce, uban meye baki sani ba? Munafukar banza da ta wofi, maƙaryaciya an cuceni an haɗani da saura, har da zuwa ki gaya musu bana kwana a gida, ai na san kin san komai kin saba".

Kyarma ta fara yi, taƙi motsawa, aka kece da wani irin ruwan sama mai ƙarfin gaske, ba ka jin komai, sai sautin zubarsa da ƙarfin gaske a kan kwano.

Ganin za ta ɓata masa lokaci, ya sanya ya jefar da fitilar hannunsa yayi kanta, kamar zararre.

Ayshercool
08081012143
*CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

BRIGHT PENS
(FREE BATCH)

P12

Kamar mai shirin tarayya da dabba, haka yayi kan ummi, ya fara yage suturar jikinta, yana ja tana ja, tana ihu tana bashi haƙuri.

"Ba zaki rufe mini baki ba?" Yayi maganar cikin fusata.

Warin bakinsa ya daki hancin ummi, kai ka ce an buÉ—e masai.

Sai dai ba ta gama shaƙe warin bakinsa ba, warin gashin kanta ya daki hancinsa, gashi ne fal Allah ya bata shi, sai dai kasancewar babu gyara babu tsafta, ya sanya yake wani irin tsami mara daɗin shaƙa.

Sai da ya ware gashin ya sauka bayanta, warin ya ƙaru har wani gafi gashi gashin yake yi, saboda tururin warin dauɗa da ƙazanta.

Ƙyale gashin yayi, ya cigaba da ƙoƙarin rabata da suturar jikinta, sai dai nan ma jikin ummi, warin dauɗa yake yi, da tsamin gumi, saboda rashin wanka da kula.

Har ɗauke numfashin sa yake yi, ita kanta ummin warin hammatar idiris ɗin ya hanata sukuni, yafi ƙarfinta nesa ba kusa ba, amma ba ta gaza ba wurin ƙoƙarin kare kanta.

Duk da a duhu ne bai hana shi, kifa wa ummi mari ba da dukkan ƙarfinsa, Allah ya sa hannunta ya samu ba fuskar ba, amma sai da ta gigice.

Marin da yayi mata ya sanya ta saka kataɓus, har ya cimma in da yake burin zuwa, sai dai wari da ƙarni mai haɗe da zarni ya bugi hancinsa sai da yayi baya, take ya ji cikinsa ya yamutsa masa, kamar zai yi amai, nan da nan zuciyarsa ta fara tashi.

Duk yadda ya so ɗauke numfashin sa ya kasa, wani irin baƙin ciki da takaici ya ninku a zuciyarsa, ya laluba ya ɗaukko fitilarsa ya hasketa, ta kare jikinta sai kuka take yi.

Ya tashi ya rufeta da duka, abun da ta fi tsana, ya din ga takata da ƙafarsa, sannan ya janyota ya hankaɗata waje ana wannan ruwan saman, ba tare da imani ko tausayi ba. Kuka take iya ƙarfinta, tana danna ƙofar ɗakin, amma ya saka sakata ta ciki.

Tsakar gidan ya shaƙe da ruwa, saboda rashin magudanan ruwa a unguwar.

Jikinta duk ya yage mata sutura, kuma a haka tsirara ya hankaÉ—ota waje cikin ruwan sama.

Ga wani irin tsoro take ji, balle ta tafi ɗaya ɗakin, haka ruwa ya din ga dukanta tana kuka. Tun tana saka ran ruwan zai ɗauke, har ta zubawa sarautar Allah ido, ƙafafuwanta suka gaji saboda tsayuwa, ruwan saman nan ya ƙarasa zuba a kanta.
Ta din ga buga ƙofar ɗakin a hankali ta na cewa "Dan Allah yaya idiris ka buɗe mini na ɗauki kayana, sanyi nake ji dan Allah" tayi bugun har ta gaji, jikinta ya din ga wata irin karkarwa saboda sanyi.
Ruwan, bai gama ɗaukewa ba, ta fara takawa a hankali ta na ƙanƙame jikinta saboda ƙyanƙyamin ruwan da ya kwaso dagwalon unguwar ya shigo ya taru a gidan.

Ɗaya ɗakin ta nufa, sai dai kasancewar ba taga babu ƙofa, a buɗe yake, shima ta tarar ya malale da ruwa, babu in da za ta zauna, ta samu wuri ɗaya ta raɓe tana cigaba da kuka.
Chapter 26 · 0% Book details