Sashe 116
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ban gayawa kawu abun da ya faru ba, ban sani ba ko ya sani, ina ga dai wurin mama zan koma na zauna dole"
Raihan ya ce "Ke a tunaninki zan bari ki sake kufce mini ne? Gobe in Allah ya kaimu da sassafe zamu tafi Abuja"
"Amma mami fa? Kuma ga aure zaka yi, kar ka kuma samun saɓani da ita"
"Ke ina ruwanki da aurena ne? Kin san wani abu?"
Ta ce "A'a"
"Har cewa su Alhaji na yi, bani da lafiya ba zan iya ƙara aure ba, kema haƙuri ki ke yi da ni" A zabure ummi ta kalleshi ta ce "Amma da wasa ka ke yi ko?"
"Wallahi da gaske nake"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai kai ba ka jin kunya ne?"
"In dai a kan ki ne bana jin kunya, a wurinki ne kawai nake da lafiya" haka suka manta da damuwa da matsalolin da suke ciki.
Washegari da sassafe, suka shirya suka tafi Abuja da shi da ummi.
Ya danƙawa ummi takardun gidan gagarawa ba tare da ya cigaba da takura mata a kan me za ta yi da gidan ba. Sai dai ta ce masa ya ajiye mata.
Raihan É—in da sai da Alhaji yayi ta fama da shi a kan tafiya Abuja, amma daga baya ya ji raihan shiru, ya tafi babu ko sallama.
Ummi har mamakin irin son da raihan yake yi mata take yi, kullum fatanta da Addu'arta Allah ya sa kar ya daina sonta.
Ummi ji take za ta iya ɗaukar kowace kasada dan ta cigaba da rayuwa da mijinta, dan sai dai ta bar gidansa ta ƙara tabattar da ɗakinta shi ne rufin asirin ta, dan sai da ta yi wa maryam Allah ya isa.
A gidan su wani abokin raihan suka sauka, gidan babu kowa a ciki, kuma kafin su je an gyara gidan komai akwai a cikin gidan.
Cikin dare suna bacci, raihan ya farka ummi na jikinsa, sai dai jikinta ya É—au zafi sosai.
Ya haskata ya ga baccinta take yi hankali kwance, washegari da safe da ta tashi, idonta ya É—an yi wani iri.
Ta dube shi ta ce "Good morning"
"Sweetheart, wai ba ki da lafiya ne? Jiya da daddare na ji jikinki ya yi zafi?"
Tayi murmushi ta ce "Duk cikin murnar ganinka ne, amma lafiyata ƙalau"
Ya rungumeta a jikinsa ya ce "Anya kuwa, idonki kamar wadda ba ta da lafiya" wayarsa ce ta fara ringing, ya kai hannu ya É—aga yayi sallama.
Muryar Safiyya ya ji ta ce "Yaya ina kwana?"
"Lafiya lau"
"Dama mami ce ta ce na kiraka, maganar kuÉ—in party, sannan kuma kayan da zan yi fitar biki".
Raihan ya ce "Ai dama auren na mami ne, dan haka ita zaki tambaya bani ba"
Ya katse kiran, ya kalli ummi da take ta sauke numfashi.
"Salma ya dai?" Ƙoƙarin tashi take yi daga jikinsa, ya riƙe ta ya ce "Meyafaru ne?".
"Dan Allah idan kana sonta, kar ka yi pretending dan ka kwantar mini hankali, dan Allah ka yi aurenka".
"Haba ummi tun yanzu? Kin fara karaya ni ya zan yi to? Dan Allah kar ki ce zaki daina kulawa da ni, wallahi banda tursasawar mami, ni babu agender ƙara aure a gabana, wannan ɗin ma da yaya aka yi ana cewa na yi ƙanƙanta?" Ummi ta yi masa shiru, dan wani irin zafi ƙirjinta yake yi mata.
Ya tashi zaune ya ce "Me zan yi mana order mu karya, zan fita da wuri ne"
Ta juya masa baya ta yi shiru.
Sai a lokacin ta ji ashe ƙarya take yi, da take cewa ba zata ɗaga masa hankali idan zai ƙara aure ba.
Ya leƙa fuskarta ya ga yadda ta haɗe rai.
Bai ce mata komai ba, ya tashi ya shiga banɗaki, har ya gama shirinsa ya fita ba ta sake kula shi ba. Sai dai fitarsa ke da wuya ta fashe da kuka, yayi wuri ace za ayi mata kishiya tana tsaka da karɓar kulawa da soyayya daga wurin mijinta, an hanata samun cikakkiyar nutsuwa tare da shi.
Ya dawo da takeaway, nan ma ta ce ya ci nasa ba yanzu za ta karya ba.
Haka Æ´an kwanakin yayi ta fama da ummi, ita kanta ba ta san tana da azabar kishi har haka ba, sai yanzu dan ta fara zancen ita maiduguri za ta koma.
Ta addabi kanta da zuciyarta ko abincin kirki ba ta iya ci, idan baya nan sai ta zauna ta sha kuka kamar ƙaramar yarinya, idan ya dawo babu ruwanta da shi, ko shimfiɗarsu ya je, sai ransa ya ɓaci. Ga kiran waya da mami take babu ƙaƙƙautawa a kan maganar auren sa.
Yau da ya kai ƙarshen ƙulewa da halinta, ya hau zazzaga mata bala'i. Tayi masa shiru abun da ya fi komai ɓata masa rai.
"Ai gara na yi auren, tun da kin gaji dani kin daina tausayi na, ina ta taki kina wahalar da ni".
Kai tsaye ta ce "Da ka huta dama kana son abun ka a ranka"
Sai da ya sake É—aga kai dan ganin ko ba ummi ce ta yi maganar ba.
Janyota yayi da ƙarfi yana fuskantar ta, zai sake balbale ta da faɗa, ya ji tana sheshsheƙar kuka, sai kuma jikinsa yayi sanyi.
"Ummi wai meye haka? Gaba É—aya kin canza".
"Dan Allah ka bari na koma maiduguri na zauna, ka je ka yi aurenka"
"Ummi ni É—in ne ba kya so kuma yanzu?"
Cikin kuka ta girgiza kai ta ce "Ba fa abu ne mai sauƙi ba, wallahi ba zan iya jurewa ba, kishi zai kashe ni, ba zan iya pretending ba ɗan aljannata, i so much love you sweetheart, ba zan iya pretending ba, kullum zuciyata da sauri take bugawa idan na tuna zaka zama namu ni da wata, ka yi haƙuri ba dan in ɓata maka rai nake yi ba, ban san haka kishin yake ba, na ɗauka ba shi da wahala" ta ƙarasa tana ƙanƙame hannunsa tana kuka mai ratsa zuciya.
Tausasan kalamanta sai suka sanya tausayinta ƙara shigarsa.
"Na san babu sauƙi, amma ki jure dan Allah na samu na yi wa mami biyayya ko na gama da duniya lafiya, idan ina ganinki a haka zan iya bujirewa, ki daure Salmana ki yi haƙuri na san da ciwo" ya din ga rarrashinta tana wata irin ajiyar zuciya, da sai da ta din ga bashi tsoro kar wani abu ya sameta.
Cikin dare jikinta yaƙi daɗi, dama tana zazzaɓinta a tsatstsaye, idan ta ci abinci tayi ta amai, ba abun da yake zama a cikin ta, sai dai na yau ya tsananta, da har sai da raihan ya gane, tun tana iya zuwa banɗaki yin aman har ta kasa.
Ranga-ranga ya tafi da ita asibiti, a karon farko gwaje-gwaje suka tabattar da ciki ne da ita. Raihan kamar yayi tsalle dan murna. Tun da tayi ɓarin nan ba ta ƙara yin period ba.
Aka din ga saka mata ruwa, sai dai zazzaɓi ba ya sauka, kuma ko ta ci abinci ko ba ta ci ba sai tayi amai.
Tausayinta ya cika raihan, ga zafin laulayi ga kishi, sai da likita ya zo dubata ne ma take gaya masa ta fi wata tana zazzaɓi a kaɗan-kaɗan.
Raihan yana saka ran a sallame su, amma likita ya ce sai sun riƙe ta, saboda low bp, ga jininta ma yayi ƙasa, sai an ba ta kulawa ta musamman.
Kwananta biyu a asibiti, da sassafe ya dafa tea zai kai mata, ya fito daga motar sa, sai ga kiran wayar Alhaji.
Ya É—aga yana gaida Alhaji sai dai yanayin muryarsa ya tabattar masa ba lafiya ba.
"Kana ina?"
"Ina Abuja Alhaji lafiya?"
"Ban sani ba, ina ummi take?"
Gaban raihan ya faÉ—i ya ce "Tana gida?"
"Ni zaka yi wa ƙarya? Ashe baka da hankali ba ka da mutunci raihan? Jiya da daddare babanta ya kirani cikin damuwa ashe sakar masa ƴa ka yi, kuma an nemi in da take an rasa, ga wani case can a familynsu ma ana ta nemanta, ka gaya mini ka sakar masa ƴa? A baka yarinya cikin girma da mutunci amma ka wulaƙanta ta, yarinya mai tarbiyya da nutsuwa, bilki ce ta saka ka saketa ko?"
Raihan ya girgiza kai ya ce "A'a ba ita ba ce ba".
"Koma waye ya saka ka, ka cuci kanka, kana ina? Kuma ina Æ´ar mutane"
Raihan ya ce "Muna tare a nan Abuja"
"Uban me ka É—auketa ka yi mata a abujan bayan ka saketa?"
"Alhaji ba sakinta na yi ba, rashin fahimta ne"
A fusace ya ce "Kai ka sani, baka ma da kunya, in anjima zan shigo garin Abujan, ka bani ƴar mutane da takardarta na danƙawa mahaifinta ita, kai kuma tun da mutumin banza ne ka je ka ƙarata, am so disappointed on you!.
08081012143
PAID ADVERT!.
Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku
Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshiÂ
Man garan gashiÂ
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702Â Â 08025453921
*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUÆE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUÆŠI GIDA*
CUTARWA!
AYSHERCOOL
(BRIGHT PENS)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
45