← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 134

Sashe 127

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Likitoci suka yi iya bakin ƙoƙarin su, aka sallamota a kan magunguna.

Bayan sun koma gida, aka kwantar da ita aka shiga jinya, saboda ba ta iya yi wa kanta komai, ita ma jinyar tun da aka yi mata ta marmari, aka fara ƙosawa.

Idris kuwa ya din ga bin ƙannen babansa yana roƙonsu a kira ummi, a bata haƙuri kar ta kai shi wurin ƴan sanda.

A ranar da ya koma gida daga asibiti, ya samu hindu ya din ga zaginta da ci mata mutunci, a kan maganganun da É—ahara ta ce ta faÉ—a a kan Iya.

Hindu ta ce "Duk tsohon dai bai ji kunyar hawa jaki ba, jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba, tun da ba uwata ba ce ta je ta mutu ba abun da yayi mini zafi, matar da ba ta da mutunci. Wai kai har ka na da bakin magana ma, tun kan ka dawo har gida aka zo aka bani labarin ka cinye kuÉ—in maganinta, kai ba ka ga laifinta ba sai nawa, sai ka fara yi wa kan ka masifar ai"

Kamar yadda suka saba, haka suka yi ta faÉ—a su na cece ku ce.

***
Anty rakiya kuwa, ta samu mami ta din ga surfa mata bala'i, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, wai ta biyewa tsoron dangin miji, za a raba musu zumunci.

Ta ɗauki gaba da ita, gaba ɗaya ta rasa abun da yake yi mata daɗi, ta na ji tana gani raihan yanzu ya koma mata kamar wani baƙo, sam ba ya sakewa da ita, saboda kar ta yi wata magana a kan ummi, kusan abun da take gudu shi yake shirin faruwa, ummi ta mallake mata ɗa.

Dan labari yana isheta cewar, kullum raihan status É—in sa, yabon ummi ne tare da koÉ—ata, dan ita ya riga ya rufeta daga gani.

Ta fuskanci sam fushinta da shi ba ya tasiri a kan sa yanzu, dan ya fi zuwa wurin hajiya ma yayi al'amuransa, ga wata irin muguwar shaƙuwa tsakaninsa da Salim yanzu har ma da Sagir.

Hakan ya ƙara mata tsananin tsanar ummi, da duk da abun da take yi wa ummin, ta kan kira waya ta gaisheta, tayi girki ko ta bayar da abu ta ce a bata, ta wulaƙanta amma tun da abun nan ya faru, ummi ba ta ƙara shishshigin raɓar in da take ba.

Aka gama gyaran gidan dr. Da idan sun dawo za su tare da mariya, daga can ƙasar ya turowa ummi kuɗi, a kan ta yi mata sayayya ta haɗa da kuɗaɗen hannunta, ta din ga yi mata sayayya.
Dan ba ƙarya hannun raihan a sake yake, kuma yana sakar mata yadda yakamata, kuma ita ma na ta hannun a sake yake.

Tun da aka yi scanic aka tabattar wa su ummi, yara biyu ne a cikinta, raihan yake murna, kuma ya gargaÉ—e ta a kan kar ta kuskura ta gaya wa kowa.
Suka yi ta shiri, tare da sayen kayan jarirai.

Sai dai cikin yana wata bakwai, kamar ummi za ta durƙusa ta haihu, saboda girma, kullum cikin lissafin kwanakin da suka rage take yi, saboda yadda nauyin cikin yake damunta, idan ta zauna sai an ɗagota saboda girman cikin.

Gefe guda kamar yadda ta yi alƙawari, tana tura wa yaya magaji kuɗi lokaci zuwa lokaci, saboda kula da Iya.

Farida ba ta haƙura ba, wurin bin bokaye da malamai, a kan lallai sai an raba auren dr. Da mariya, kuma a sake mallake mata shi ta juya shi fiye da yadda take yi a baya.

Sai dai abun da ba ta sani ba shi ne, duk da kallon mahaukaciya tuburan take yi wa mariya, a hakan ba ta wasa da addu'a, mace mai son addini sosai da sosai, dan yana ɗaya daga abun da ya sanya ta ƙara shiga ran dr. Sosai da sosai.

Hajiya ita ta maye wa ummi gurbin sirika, dan kusan har role ɗin uwa take yi mata playing, kusan kullum tana tafe zuwa duba ummi, ko yi mata aike take, tana tausayin ummi sosai da sosai, saboda abu ne na fari ba ta san ya yake ba, tana yawan cewa ummi "Anya ummi ba zaki likitoci su ƙara caje cikin nan ba, girmansa yayi yawa tubarkallah" sai dai tayi murmushi, ba tare da gaya mata haƙiƙanin abun da yake cikin ba.

Ummi ta daina fita ko ina, gashi ta ƙara zama mafaɗaciya, saboda damuwar ciki. Kasancewar Hajiya na gaya wa raihan sai yayi haƙuri da ummi, a wannan stage ɗin mata masu ciki na fuskantar saurin fushi, dan haka sam baya damunsa, shi tausayi ma take bashi.

Duk tsaftar ummi, sai da zamana dogon gashin nan sai ya kwana uku babu taza, kusan kullum sai dai ta saka kaya masu sauƙin nauyi yadda iska za ta wadace ta, takalmi kuma idan ba over size ba duk haushin takalman take ji.

Da safe ta fito, tana ta mita noor ba ta É—umamata shinkafa ba, wai ita ba ta cin abun da ta dafa.

Noor ta ce "Ke fa ki ka ce ba kya son warin shinkafa"

Kamar tayi kuka ta ce "Haba noor, amma tun jiya na ce miki zan ci, yunwa nake ji, ina magana kina kallo kin yi mini banza"

Noor ta ce "Ai Yaya ummi ban san yaya zan yi miki na burgeki ba, MD ne kawai yake iya miki, ni ba ni na É—ora miki nauyin cikin nan ba, amma ki yi ta yi mini faÉ—a. Kuma sai na koma gida tun da faÉ—a ki ke yi mini"

Ummi ta marairaice ta ce "Haba noor, to ki yi haƙuri dan Allah kar ki tafi, wai ni ya ku ke so in yi?"

Raihan da yake bayanta ba ta sani ba, ya kama dariya, ba wuya ta bayar da haƙuri, ba wuya kuma ta fara kuka.

Ciki duk ya mayar da ita wata iri, sai dai bai sanya ta daina kyau a idonsa ba.

Yayi gyaran murya ya ce "Ya aka yi ne yau ke da noor É—in taki ku ke faÉ—a"

A shagwaɓe ta ce "Wai tafiya za ta yi"

Ya ce "Haba nooriya, uwa guda ki tafi ki bar Æ´ar ta ki?"

Noor ta tura baki ta ce "FaÉ—a take yi mini, kai ma fa shaida ne ta ce ba ta son shinkafa, wai yau kuma shinkafa za ta ci, wai ta gaya mini jiya da daddare, ni ina na ganta jiya da daddaren?"

Ummi ta ce "Ni duk kun tsane ni, baku san me nake ji ba, ko tausayina ba kwa ji"

Raihan ya ce "Mu mun isa, mu kuwa muke ƙaunar ki, jeki ki yi wanka ki shirya, har noor tare zamu tafi office yau, kya ji daɗin jikinki"

Ta juya tana hararar noor, noor ta kama dariya ta ce "Na fasa tafiyar yaya ummi"

"Ki yi ta tafiyar ma, ina ruwana" suna lallaɓata suna yi mata dariya.
Aka ba ta É—unamen shinkafa ta ci hankalinta ya kwanta.

Tare suka tafi wurin aiki, fitowar ta yi mata daÉ—i tana kallon titi.

A can wurin aikin, suna zuwa a parking space noor ta ga motar Salim.

Sun shiga take tuna masa wulaƙancin da ya yi mata, ta zo ganinsa.

Yau bai biye mata ba, ya ce "Allah ya baki haƙuri, kar na tanka cibi ya zama ƙari"

Ma'aikata na ta gaishe shi, yana amsa musu cikin mutuntawa.

Wani mutum ya taso, ya tare su ya durƙusa a gaban raihan yana dan Allah maigida ka taimaka mini da aikin sharar nan ko masinja, nafi wata ina zuwa an hana ni ganinka, ina cikin mummunan yanayi na babu da fama da rayuwa, dan Allah ka taimaka mini.

Ummi ta zubawa mutumin ido, raihan ya kalli ummi ya ce "ya dai? Kin san shi ne?"

"Ishaq Abdulkarim magashi" ta faÉ—a jiki a sanyaye, mutumin ya É—aga kai yana kallonta.

A rikice cikin tashin hankali mutumin ya ce "Salma Muhammad Bashir, ke ce da ma ke ce? Kina nan dama" ya fara maganar cikin kame-kame.

"A ina ki ka san shi?"

Ummi ta ce "ÆŠan ajinmu ne a University"

Raihan ya ce "ÆŠan ajinku? Amma yake neman shara?"

"Wallahi yallaɓai korata aka yi daga makaranta, dan Allah ka taimaka mini"

Raihan ya ƙare masa kallo ya ce "Kana cikin wanda ku ka din ga muzanta mini mata kuna makaranta ko?"

"Dan Allah ka yi mini rai yallaɓai, lamarin Allah kenan, gashi yau ina neman alfarma a wurinta, na yi nadama dan Allah ki yi haƙuri ki yafe mini"

Gwiwoyi a ƙasa yake yi musu magiya, ummi ta ce "Kar ka damu, ba ni nake ɗaukar aiki ba, ni abun da ya faru ya wuce a wurina, wannan wurin kuma ba ni da hurumin ɗaukar ka aiki, idan  ya baka haka nake fata, idan bai ba ka ba ka yi masa uzuri wataƙila babu vacancy ne" daga haka ta ja jikinta ta yi gaba zuwa office ɗin raihan.

Ba ta san yadda suka ƙare ba, shima da ya zo office ɗin bai gaya mata yadda suka yi ba, noor ta ce "MD a ina yaya Abdul yake?"

Raihan ya ce "Ai ba a nan branch É—in yake ba, yana sharaÉ—a shi".

"To ina first born?"

Ya kalleta ya ce "Wa kenan?"

"Yaya Salim mana, ba ka san last born yake ce mini ba, shi kuma first born?"

Raihan ya yi dariya ya ce "Ni ina zan sani, baya nan"

Noor ta ce "Na ga motarsa fa"

Ummi ta ce "Kai noor, me zaki yi masa an ce miki baya nan"

Raihan ya ce "Da gaske kin ga motarsa?"

"Wallahi na ganta"

Raihan yayi murmushi ya ce "Yaya hukuma sai da rarrashi, office fa na bashi, nake ta bin sa ina yi masa magiya, ofishin kula da ma'aikata da ladabtar da au na bashi, ya ce ba ya so ba zai yi ba wai wata sana'ar zai yi. Na ce Alhaji ya saka baki, amma ya ƙi shi ne yau ya zo ban sani ba, ko ma ya neme ni, bari na je office ɗin nasa na duba"

Noor ta bi raihan har office É—in da Salim yake, sai haÉ—e rai yake yi.
Chapter 127 · 0% Book details