Sashe 72
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kasancewar yau babu coustomers, ummi ta bar reception ta koma in da take zuwa ta yi salla ta ci abinci ta kwanta, tana cigaba da duba chat's É—in su da raihan.
Ƙamshin turaren raihan ne ya fara yi mata sallama, ta zaci hallucinating kawai take yi, sai dai ba ta gama tunanin ba, ta ganshi a tsaye a kanta.
A zabure ta tashi zaune, tana bin sa da kallo.
Wani irin kwarjini ta gani a tare da shi, wanda ba ta taɓa gani a tare da shi ba, fuskarsa a matuƙar haɗe, kamar ba ya dariya.
"Raihan" ta kira sunansa a hankali.
Ya nemi wuri ya zauna, ya ƙura mata ido sannan ya ce "Salma wannan shi ne tukuicina daga gareki ko? Ko rabuwa ki ke son mu yi, yanke alaƙa da ni kai tsaye ba tare da wani dalili ba kina ganin shi ne mafita? Bafa a rana ɗaya muka gina alaƙar nan ba, ummi dama zaki iya wulaƙanta ɗan Adam har haka kamar yadda ki ka yi mini?"
Cikin rauni ta ce "A'a raihan, ba haka bane ba, dan Allah ka fahimce ni" nan ta gaya masa bayan dawowarta gida abun da ya faru, yadda farida tayi mata bincike ta nuna wa dr.
"Raihan wulaƙanci ba halina bane ba, ina ma naga ƙarfin gwiwar da zan iya wulaƙanta wani? Raihan ba kowa zan yi wa bayanin alaƙarmu ya kalli abun da idon basira alaƙar ta yi masa ma'ana ba, bana son zargi ya shiga ran dr. Duk da ya goya mini baya, amma ban san ta yaya zan wanke kaina ba, kafi ƙarfin wulaƙanci a wurina raihan, ban yi haka dan wulaƙanta ka ba"
Ya girgiza kai ya ce "Ban yadda ba ummi, duk a ƙoƙarinki na guje mini, ki ke shirin kai kan ki ga halaka, zaki auri shugaban makarantar ku ko? Malam isa"
A zabure ta kalli raihan, ya aka yi ya san wannan maganar?
"Mamaki ki ke yi ma? Ni zaki juya baya rana tsaka ummi, har ki yi shirin aure ban sani ba? Ina bibiyar rahuwarki fiye da yadda ki ke tunani, gani nake ko yaya na kawar da kai a kanki wani abu zai faru da ke, rabuwa da ni ba mafita bane"
"Raihan haka ne kawai mafita a wurina, matar gidanmu ta matsa mini da yawa, ƙalubale ko ta ko ina, ba zaka gane a mawuyacin halin da nake ba...
Ya katseta da cewa "Kuma sai ki kai kan ki ga halaka, mutumin da ya saki mata sun kai biyar, ya saki wata ke ma zai aureki ya biya buƙatar sa ya sake ki, ba irin wannan mijin nake roƙa miki ba"
Ta ce "Raihan alkhairi nake fata"
"Yi mini shiru" yayi maganar a hasale, galala take bin sa da kallo.
"Yakamata mu daina yaudarar junanmu, daga ni har ke, idan saboda ki rabu da ni ne, ki ke ƙoƙarin yin wannan auren, kin riga kin makara, ba za ayi shi ba. Ban damu da koma me wani zai yi zargi ba, ba zaki iya rabuwa da ni ba, kin riga kin makara. Ke banda rashin lissafi ma me zaki yi da wannan dattijon, shekarunsa nawa ke naki nawa? Me zai tsinana miki, ko ke ba kya wannan lissafin, ko an ce miki ci da sha ne kawai aure? Kodayeke ai kin san me nake nufi" kai ka ce gunki haka ummi ta koma, yau raihan ya zama wani abu na daban.
"Salma, ki yi haƙuri ba zan iya barin wani ya aureki ba, saboda ni nake sonki"
Tamkar ya jona mata shocking ta zabura ta ja da baya tana kallon fuskar raihan, yadda farar fatarsa ta koma ja, da irin kallon da yake yi mata, ya sanya ta tabattar da ba ƙarya yake yi ba.
"Ummi ki yi tunani, wace irin alaƙa ce a tsakani na da ke?"
Kamar zata fashe da kuka ta ce "Raihan, ni fa ƙanina na ɗauke ka, ƙanin ƙawata ce kai, mutum ne kai mai muhimmanci ne a gareni, amma ba irin wannan alaƙar ba".
Tashi yayi ya taka, ya je gabanta ya durƙusa, ya ɗan tsura mata ido ya ce "Bamu haɗa alaƙa da ke ba, ta uwa ko ta uba ba, kuma tarayyar mu da muka yi da ke ta wuce yadda ki ke tunani, ta kuma wuce gurbin da ki ka ajiyeta. Salma son juna muke yi. Lokacin nan da muka ɗauka ba ma tare, ki ka yanke alaƙarmu, kin sani a mummunan yanayin da yakamata ki ce na yafe miki, na shiga matsananciyar damuwa"
Da sauri ta girgiza kai ta ce "A'a Raihan, ina ganin mutuncinka, babu wannan maganar a tsakanin mu dan Allah a barta, kar ka sake yin ta bana so"
Ya shafi gefen fuskarsa, yana jin zafi a zuciyarsa, ya kalli ummi ya ce "Na gode Salma" ya tashi ya fice daga wurin.
Ummi ta takure tana ajiyar zuciya.
"Salma, ki yi haƙuri ba zan iya barin wani ya aureki ba, saboda ni nake sonki" shi ne abun da ya din ga yi mata kai kawo a zuciyarta.
Manager ne ya biyota yana tambayarta me ta yi wa ƙaninsa ya ga ya fita rai a ɓace, ummi ta ce masa babu komai.
Kwanaki biyu a tsakani, headmaster ya daina kiranta a waya gaba É—aya, messages É—in ma da yake tura mata ya daina.
Sai dai ko a jikinta, tunanin ya raihan yake yafi tsaya mata a rai.
Gashi ya ce halin da ta saka shi a ciki, yakamata ta nemi yafiyarsa.
Ganin ba ta da mafita, ya sanya ta neme shi a waya, amma shiru ba ya É—agawa.
Tana cikin jimamin lamarin, dr. Yayi sallama a ƙofar ɗakinta, ta amsa sannan ya shiga.
Ya nemi wuri ya tsaya, sannan ya dube ta ya ce "Ummi, baya fa ta haihu, mutumin nan malam Isa ya kirani a waya, ya ce mini ya janye maganar aurenku, kuma hakan yayi mini dai-dai, dan kuwa ko bai janye ba, ba zan bashi aurenki ba, binciken da na yi a kansa bai yi mini daÉ—i ba, dan haka ki cigaba da addu'a, Allah ya kawo mafi alkhairi" har kawu yahaya ya fita, ummi na tunanin me raihan ya yi wa headmaster ya fasa aurenta, kenan da gaske yake yi sonta yake, ba zai bari kowa ya aureta ba!?
Gabanta ya faɗi tare da tabattarwa da kanta ba ta ga ta zama ba, idan ba raihan da rigima ba, ai ya san zaren ba kalar yadin bane ba, ina shi ina ita? Kyakkyawan matashi kamarsa me zai yi da ita, ga uwa uba ta girme shi, dole ta lallaɓa shi su rabu lafiya.
Sanin baya É—aga wayarta, ya sanya washegari da ta shirya, ta tafi office É—in su raihan.
Sai dai ba a bari ta shiga ba, sakataren shi yayi mata sannu da zuwa, tare da tambayarta raihan ya san da zuwanta?.
Ta ce "A'a, amma ace masa ummi ce"
Sakataren ya tashi ya shiga cikin office É—in raihan, ya dawo ya ce mata ta jira, zai neme ta.
A ƙalla ta shafe awanni biyu tana jira, bai fito ba, ba kuma dan yana abun da ya fi ganinta muhimmanci ba, sai dan ya sanya ta yarda da alaƙarsu soyayya ce.
Yana office É—in sa, ya kira waya ya saka aka kai mata ruwa da lemo da snacks.
Ya koma ta window ya tsaya yana kallonta in da take zaune, fuskarta duk ta faÉ—a, tana ta wasa da yatsun hannunta.
Ji yayi ya kasa jurewa, ya nufi ƙofa ya fita, tana hango shi ta tashi ta tsaye, sakataren ya fara yi masa bayanin ita ce baƙuwar da take son ganinsa, ta daɗe a wurin. Buɗar bakin raihan sai cewa ya yi ta rubuta a rubuce tana son ganinsa, idan yayi approving ya bata date da time ya fice ya bar ummi.
Ayshercool.
08081012143
[4/20, 7:21 PM] Authoresses: Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â *CUTARWA*
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
FOLLOW AND SHARE
AYSHERCOOL

31
Har raihan ya bar harabar gidan bayansa ummi take kallo, ko sau ɗaya bai waiwayo ba, ita kuma ba ta daina zubar da hawaye ba, gani take kamar kallon ƙarshe take yi masa, ba zai sake dawowa rayuwarta da sunan yana son ta ba.
Ta tashi jiki babu ƙwari, ta tafi ɗakinta, ta rufe ɗakin ta saka sakata, saboda kar noor ta zo ta isheta da surutu.
Ta zauna ta din ga kuka, ta ma rasa kukan me take yi.
Ta yi shiru tana tuno irin rayuwar auren da ta yi a gidan idiris, ta kasa manta irin wulaƙantar da ta yi a gidan idiris, irin tozarcin da ya yi mata, tamkar ya auri mushen dabba ba ɗan Adam ba, kuma ɗan Adam ɗin ma ƴar uwarsa.
Ta tuna yadda abokansa suke zunɗensa da angon ɗoɗɗoya, ba zata manta tonon asiri da wulaƙantarwar da Idiris yayi mata ba.
'To idan kuma haryanzu ban warke ba fa'?" Ta tambayi kanta.
Ta dafe ƙirjinta tana zancen zuci, ita dai tun da Allah ya sa kawu yahaya ɗaukkota, yayi ta ƙoƙarin saya mata magunguna, cikin ikon Allah ba ta sake jin wannan matsalar ba, ko maƙiyinta ba ta fatan Allah ya haɗa shi da bala'in da yake cikin larurar sanyi.
Tun da farida ta dawo daga gidan inteesar, tamkar ita za ayi wa kishiya, kamar za ta yi hauka, domin kuwa da ita da wasu daga ƙannenta suka dawo gidan, suna ta bata haƙuri, a kan sai ta daure ita ma, idan ba haka ba inteesar ba zata kwantar hankalinta ba.