← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 134

Sashe 128

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kalli raihan zai yi mita, sai ya ga noor a bayansa, sai kuma ya saki fuska.

Raihan ya ce "Yaya ashe ka zo É—in ban sani ba".

"Eh da ka je ka haÉ—a ni da hajiyan Bauchi ko?"

Raihan ya sosa kai ya ce "Tuba nake babban yaya, with due respect kuma kai ne mataimaki na zan É—ebo sauran ayyukan da nake gabatarwa, na kawo maka zuwa next few months kuma, i will step down ka yi taking over"

Salim ya yi masa wani mugun kallo ya ce "Raihan ba ka da hankali ko? Tayaya makakke zai jagoranci wannan abun, kai da ka ke a nutse ma kana fama"

Noor ta ce "Ahh ba ka daina ba? Ka ce mini ka rage sosai ai" Raihan yana ja da baya yana dariya ya ce "Yauwwa noor gaya masa dai"

Kwanaki suka cigaba da tafiya, wasu rayuwarsu na daidaituwa, wasu kuma suna girbar abun da suka shuka.

Ummi ta shiga watan haihuwa, dr. Suka dawo ya kammala karatun da zai ba shi damar zama professor.

Duk wanda ya kalli mariya ya san ta samu kwanciyar hankali, shi kamaa dr. Ya canza.

Bai sauka a ko ina ba sai tsohon gidansa, in da za su zauna da mariya, gida yayi kyau ummi ta gyara komai.

Abdul ne ya É—aukko su daga airport ma, farida sam ba ta san ma sun dawo ba.

Ummi ta yi wa Allah godiya, ganin mama cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali.

Dr. Ya ce noor ta kwana tare da mariya, duk da jikinta yayi sauƙi sosai da sosai, shi kuma ya tafi can gidansa, sai dai ko kallon kirki bai samu daga farida ba, balle karɓa mai kyau.

Tana saka ran asirin da ta yi ya ci shi, ya biyo ta yana lallaɓata, amma ta ga ko ta kanta bai bi ba shi ma, yayi wanka ya shiga ɗakinsa ya hau bacci.

Tsananin takaici da baƙin ciki ya sanya ta je ta tashe shi da masifa, har da iƙirarin sai ta kashe mariya, bayan ta gama ci mata mutunci da kiranta mahaukaciya.

"Wallahi farida ban taɓa gaya miki ba, amma yau zan faɗa na yi dana sanin aurenki farida, baki da tarbiyya ko kaɗan. Suffar da ki ka mu'amalance ni daban kan na aureki, wadda ki ka nuna mini bayan auren daban. Wallahi na yi dana sanin rashin auren mahaukaciyar da ki ke faɗa tuntuni ta fiki sanin darajata.
Wallahi ki ka kuskura ki ka yi mata wani abu, a shirye nake da kowa ya kama gabansa da ni da ke, ba zaki kashe ni ba wallahi" ta dafe ƙirji tana zazzaro ido "Da can ba ka san bani da tarbiyya ba sai da ka auri mahaukaciya?"

"Na sani mana, kara nake yi miki ina yi miki kawaici, ke kuma ba kya gani, gara na fito miki a mutum, ina kuma jaddada miki, idan ki ka kuskura ki ka taɓa mariya kin taɓa igiyar aurenki, dan ba zaki cutar da abun da nake samun farinciki daga gare shi ba".

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku wallahi yahaya kai butulu ne, azzalumi ni ka ke gaya wa haka?"

Dr. Ya ce "Ke ki ka so, ai ni ban san tuntuni kamar a kurku nake ba, sai yanzu na yi ƴanci ai. Ke ki ka janyo duk abun da na yi miki, ke ma kin san na yi haƙuri da ke, kuma bani da niyyar cutar da ke, amma halinki ya fara kaini bango"

Gaba ɗaya farida ta ji duniyar tayi mata zafi, komai ne naman ƙwace mata.

Washegari dr. Ya shirya ya tafi gagarawa duba iya, babu yadda bai yi da mariya ba, ta ce masa ita fa ko rasuwa iya ta yi ba za ta je ba. Sam mariya ba ta da zafi, amma tun da ta faɗi haka ya san abubuwan da iya tayi mata suna cigaba da ƙona mata zuciya ne, dan haka ya ƙyaleta.

Ya je ya tarar an mayar da iya asibiti, babu wata kulawar kirki, babu jinya mai kyau tana iya magana amma ba sosai ba, sai ta yi zawo har ya fara bushewa a jikinta ba a É—agata an gyara ta ba.

A wannan karon mariya ta matsa sosai a kan lallai sai ta je sun gaisa da maman raihan.

Raihan ya sanar da Alhaji, Alhaji ya ja wa mami kunne sosai a kan kar ta kuskura ta wulaƙantawa ummi uwa.

Mai hali baya fasa halinsa, dan sai da tayi abun da mariya ta fuskanci akwai wani abu a ƙasa, Hajiya kuwa ta karramata sosai da sosai.

Sai dai mami ta yi mamakin ganin maman ummi, sam ba baƙa ba ce ba ga dogon hanci har baka.

Sati biyu da dawowar su dr., Ƴan maiduguri suka zo ganin gidan mariya, suka din ga murna ganin yadda ta yi ƙalau da ita.

Bayan ummi ta koma gida daga gidan mariya, cikin dare naƙuda ta tayar mata.

A cikin daren ita da raihan suka tafi asibiti, dan noor ta gudu wurin mariya, wia sai ummi ta haihu za ta dawo, yanzu ta zama masifaffiya.

Da safe raihan ya kira waya ya sanar suna asibiti, sai dai haihuwa ta gagari ummi, ga ciwo amma labor baya gaba, duk ta galabaita, likita ya ce sai dai ayi mata aiki.

Alhaji ya ce lallai sai mami ta je asibiti ita ma, ayi komai da ita ai matar É—anta ce.

Ummi ta tayat da hankalinta, ta din ga kuka tana cewa tsoro take ji, duk aka kewayeta ana rarrashinta.

Noor kuma tana gefen ta tana tayata kukan.

Ummi ta kalli mariya, ga mama matar kakanta, ga Anty maryam, ga hajiyar su raihan, ga Abdul ga raihan kansa har da Salim, ga Nihal ƙanwar raihan, ana rarrashinta. Duk da mami ita sai yatsuna fuska take yi.

A ranta ta ce "Allah sarki, haka family suke dama? Kowa ya damu da kai" wani irin farinciki ya cika mata zuciya.

Ta ce sai dai a shiga aikin har da raihan, idan mutuwa za ta yi ya riƙe hannunta.

Mami ta ja wani uban tsaki, raihan kuwa ya riƙe hannunta yana ta kwantar mata da hankali.

Raihan ya kasa zaune ya kasa tsaye, aka shiga da ummi, awa guda da wani abu, aka fara fito da jarirai, mace da namiji.

Sai dai hankalinsa ba a kansu yake ba, Ummi yake jira a fito da ita.

Yana nan tsaye aka turo ta a kan gado idonta a rufe, an rufeta da green É—in yadi.

"Salma" ya kira sunanta da ɗan ƙarfi.

Ta buɗe ido tare da riƙe hannunsa ta ce "Ka yi magana a hankali mana, ban mutu ba" yayi dariya ya durƙusa ya sumbaci goshinta ya ce "Thank you very much sweetheart, Allah ya baki lafiya"

Can waje kuwa ana ta murna an fito da jarirai, mami ta kallesu ta ce "Taɓ, wannan wane irin yara ne, mu kaf danginmu babu wannan kalar, meye wannan?"

Ayshercool
08081012143.

CUTARWA!

AYSHERCOOL

(BRIGHT PENS)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

49

PAID ADVERT

*Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Ɗan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir ɗin da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin sheƙin fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sanƙo, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ƙarfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuɓe su a kan lambar wayar su dan ƙarin bayani 07045971194 ko 08140450950*

49

Tsit kowa ya yi ya zuba wa mami ido, tana wani yatsune fuska.

Hajiya ta ce "Amma meyasa zaki ce haka? Wannan ai ba magana ba ce ba"

"Eh na faɗa, ko a dangina kin taɓa ganin irin wannan?, kalli kalar uwarsu ki kalli raihan ki kalli yaran".

Jajawur yaran, haskensu ya wuce ace hasken raihan kawai suka ɗaukko, gasu manya sosai, kuma kansu ƙwal babu gashi, kuma ba su da gashin gira ko kaɗan sai alamarta.

Mariya cikin jin kunya ta ce wa Hajiya "Bari na gansu"

Aka miƙa mata yaran, ta zuba musu ido tana murmushi sannan ta kalli mami ta ce "Hajiya, ai yaran nan da babansu su ke kama, haka na haifi ummi, Iya ta din ga ce mata aljana, sai dai kwana biyu kanta ya cika da gashi ko anty maryam, sai dai ummi tun tana jaririya baƙa ce".

Wani mugun kallo ta yi wa mariya ta ce "To ni danginmu babu irin wannan abubuwan, ni ban taɓa ganin jarirai a haka ba, danginmu dai kaf babu mai wannan farin"

Nan da nan Maryam ta harzuƙa ta ce "To mu namu akwai, duk tsiya dai ai na ɗanki ne ba wani ba"

"Ba ni da tabbas, ni É—a na ma ba shi da cikakkiyar lafiya"

Hajiya da ta fara fusata ta ce "Ke dai ya rainawa hankali, dan ya tsallake son zuciyarki"

Mariya ce ta din ga basu haƙuri.

Raihan kuwa yana can ɗakin da aka kai ummi, sai zuba yake yi yana yi mata kalamai masu kwantar da hankali da ƙwarin gwiwa.

Likitan da yake yi mata allura ya ce "Maman twins ai ba Kya buƙatar maganinmu, wannan kalaman sun ishe ki warkewa" suka din ga dariya, sai da bacci ya ɗauke ta sannan ya tafi ɗakin da su Hajiya suke.

Noor ji take kamar ta kwaÉ—awa mamin raihan mari, ko karar ganin idon mariya bai saka ta yi alkunya ba.

Abdul da yake ɗakin ya tashi ya fita, Salim ma surutun ya ishe shi, ransa ya fara ɓaci.

Mariya ta kalli Salim ta ce "Salim, dan Allah jariran nan ba da babansu suke kama ba, dan Allah kar ki saka zargi a kansu tun suna jarirai, su sha wahala kamar ummi, idan ta tashi ta ji, ba za ta ji daÉ—i ba".

Salim ya ce "Mama, muna murna muna fatan Allah ya bawa ummi lafiya, mun gode wa Allah kyautar da ya bamu" ya ƙarasa maganar yana yi wa mami mugun kallo.

Kamar daga sama raihan ya shigo ya ce "Hajiya ba ni su na gansu"
Chapter 128 · 0% Book details