Sashe 48
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yaya É—anlami ya ce "Babu lafiya, wasu lokutan dai hankakin yana dawowa, wasu lokutan kuma sai ciwon ya dawo tayi ta shirme. Amma a hakan nan da take, za ta yi wanka, tayi shara tayi kwalliya ga shirin dutse nan ma gashi ka ganta tana yi, likita ne ya ce a samo mata abun da zai din ga É—ebe mata kewa.
Ka ga yanzu tafi sati ba ta yi magana ba, ba ta duka ba ta zagi, kaga daga mutuwar mijinta, ga rabata da ummi, ta zo ta haihu É—an ba rai, tayi jijjiga depression yakamata sai kuma dai ta samu matsala gaba É—aya.
Ban taɓa tunanin wani daga dangin baban ummi zai biyomu ba, dan mun yi alƙawarin ba zamu sake zuwa ba, irin jafa'i da mugun bakin da mahaifiyar ku tayi wa ƴar uwarmu, ya sanya muka ce gara mu yanke alaƙa da ku kawai".
Dr. Yayi ajiyar zuciya ya ce "Tun da na É—auki yarinyar nan, nake fafutukar neman ina ku ke, ni ban san garin nan ba, ainihin in da kuka zauna aka aureta, mun je aka ce ba kwa nan, abubuwa dai duk ba su yi daÉ—i ba, sai fatan Allah ya kyauta".
Mama da yaya maryam da suke gefe suka amsa da amin, dan maryam ta zo gida yau, babu tsammani suka ga kawu yahaya.
Maryam ta ce "To ya ummin take? Ba ka zo mana da ita ba?"
Ya girgiza kai ya ce "Ba yanzu ba, ummi na nan a jami'a".
Yaya maryam ta ce "Dan girman Allah, ummin?"
Yayi murmushi ya tashi ya ƙarasa gaban ta ya zauna yana kallonta, ba tare da ta ɗago ba tayi murmushi ta ce "Baban ummi"
Ya ce "Na'am".
"Jigidata da ka tsinka mini nake gyarawa"
Sunkuyar da kai suka yi cike da jin kunyar abun da ta faÉ—a, dan tafi sati ma ba magana.
Yayi murmushi ya É—ebi dutsen da take ta shiryawa ya ce "Gaskiya ban kyauta ba, ki haÉ—a wata maza".
Ta sake yin murmushi ta ce "Da na san zaka dawo, ai da na yi kitso, an yi mini lalle, kaina ba kitso, bana son kitso tun da ka tafi bana son kitso" tayi maganar tana cire hular kanta, gashin kanta baƙi wuluk ya bayyana.
Yaya maryam zata yi magana, ya É—aga mata hannu tare da girgiza mata kai, ya ce "To tun da na dawo yanzu sai ayi ko?".
"Ba zan yi ba, tun da ka tafi ka bar ni, ka ƙi ka dawo, Iya ta ƙwace mini ummi, ɗa na ya mutu ka ƙi ka zo ka ganni kuma bani da lafiya" tayi maganar tana kuka wiwi.
Ya ce "To ki yi haƙuri, ki yi haƙuri ba zan sake tafiya naƙi dawowa ba"
Ta riƙo hannunsa ta na cigaba da kuka ta kwantar da kanta a hannunsa ta ce "Baban ummi"
Ya amsa mata da "Na'am"
Ta ɗaga kanta ta kalleshi ta ce "Ka je ka karɓo mini ummina, Iya ba zata din ga yi mata wanka ba, ko idan yamma ta yi ta saka mata kayan sanyi, ba ta son ummi, dan Allah baban ummi ka karɓo mini ummi, kaga katifata ta ishemu ni da ita, idan ka sai mana gida sai in dawo gagarawa ko?"
Ƙura mata ido yayi, cike da matsanancin tausayinta, lallai yana daga horon da za ka yi wa uwa, ka rabata da ɗan ta, duk da tana cikin hauka, amma ba ta manta da ƴar ta ba.
Yayi ajiyar zuciya ya ce "To shikenan, ki daina kukan ya isa haka, mayar da hularki, kiyi haƙuri" ta ɗauki hularta ta saka.
Ta ja bakinta ta sake yin shiru.
"Zan kawo miki ummi in sha Allah, amma ba yanzu ba".
Yaya maryam ta ce "Saboda me? Abun da ta daÉ—e tana jira kenan, ka taimaka".
Ya ce "Ina da dalilina, kuyi haƙuri dan Allah"
"To amma mu ai ka bari muje in da take".
Kawu yahaya ya ce "Da ina da ƙudurin rabaku da ummi, da ba zan neme ku ba, ina da hujja mai ƙarfi sosai.
Zan cigaba da shiga lamarin nemawa mariya magani in sha Allah, komai zai daidaita kuma zai wuce".
Ba haka suka so ba, amma ba su san takamaimai menene dalilinsa na ƙin haɗa su da ummi ba.
***
Hangen dala ba shiga birni ba, domin kuwa inteesar tayi zaton soyayyar da suka sha da sagir a waje, ita za aje a cigaba da yi a gidan, sai abun da take so shi zai din ga yi mata, amma ina.
Ya nuna mata shi namiji ne, mage mai kwanciyar É—aukar rai, a gida ta saba ba abun da take yi, ummi ce take komai. Yanzu kuma ya ce shi ba zai É—auki Æ´ar aiki ba.
Dan haka sai komai ya din ga bata wahala, asubar fari zata tashi ta haÉ—a masa breakfast, gashi su yi ta faÉ—a dan abincin nata ba daÉ—i, ga almubazzaranci kamar ba mace ba.
Ga rashin kunya da rashin iya magana, gashi ɗan uwan mata, yana da tarin yayye da ƙanne mata, ga uwarsa mai shegen sanya ido. Sai ƙannensa su zo gidan su fi sati, gasu manya duk sun girmeta, su yi ta yi mata rashin mutunci, idan tayi magana su ce za su yi mata dukan tsiya.
Abun duniya ya damu inteesar, ta dawo gida tana kuka, ta gayawa mamanta.
Farida a zatonta zata iya maganin abun, ta kira Sagir tana masifar dan me ba zai tsawatarwa ƙannensa ba?
Ya ce mata ba zai iya ba, baya son ya saɓawa mahaifiyarsa.
Abu kamar wasa aka fara jamb, kawu yahaya ya turawa inteesar kuÉ—i, ya ce taje tayi jamb, a nema mata admission.
Amma sagir ya ce ba yanzu ba, sai ta haihu, domin kuwa a lokacin ma laulayi take yi.
Kawu yahaya bai matsa ba, farida ta din ga masifar dan me ba zai dage sai inteesar ta fara makarantar yanzu ba?
Ya bata amsa da "Yanzu ya fi ni iko da ita, shiyasa tun tana ƙarƙashin ikona, na so ta fara makarantar, yadda bai isa ya hana ba, amma ku ka dage, dan haka ni ba abun da zan ce".
***
BAYAN WANI LOKACI!.
Kasancewar tsakiyar damuna ne, an ɗan kwana biyu ba a yi ruwan sama ba, dan haka ana tafka zafi, ga uwar rana da ake ƙwalawa.
Tamkar ba ita ranar ke duka ba, haka take tafiya sannu a hankali, tana ratsa layukan unguwar, sannu a hankali take tafiyar, tamkar tana tausayin ƙasa, kamar mai rangji haka take tafiyar kamar tana tausayin ƙasa.
Ta cikin niƙabinta take kallon dogon layin, tare da lissafa sauran tafiyar da ta rage mata, ta isa in take fatan zuwan.
Layin shiru, sai lokaci lokaci, ababen hawa ke giftawa, manyan gidajen layin ko ina a rufe.
Ƙarar babur ta ji, kasancewar gefen hanya take bi, ya sanya ko a jikinta, dan ko waiwaya wa ba ta yi ba, ashe layin da yake gabanta yake ƙoƙarin shiga.
A É—an fusace ya ce "Ke, kurma ce ne? Sai mutum ya tureku, ace bai kyauta ba, ba ki ji ina horn bane?"
Ta tsaya cak, ta ɗan ja wasu seconds, sannan ta juyo ta kalleshi ta cikin niƙab, sai dai ba ta ce komai ba.
Maimakon ya wuce ya tsaya ya ji me za ta ce, idan rashin kunya za ta yi masa, ya ƙare mata ta tas.
A hankali ta ce "Sorry, ga hanya wuce" tayi maganar tana É—an ja baya ta bashi hanya.
Fuskar ta a rufe da niƙabi, amma muryarta ce ta saka shi ƙara kallonta.
"Malama idan zaki ware murya ki ware, da na bugeki ai ba zaki maƙale murya ba".
Ta ce "Ikon Allah, me muryata kuma tayi maka, ai na ce ka yi haƙuri ka wuce"
Tsaki yayi ya ja babur ɗin sa ƙirar lifan, ya yi gaba.
Ita kuma ta yi ajiyar zuciya, ta cigaba da tafiya.
A ƙofar ƙaton gate ɗin gidan ta tsaya, mutum biyu ta tarar sanye da uniform na security, suka dubeta suka ce "Gurin wa zaki je?"
Ta ce "Habu baka gane ni ba?"
Jin muryarta ya sanya shi cewa "Ahha wata sabon gani, ke dama kina duniyar nan?"
Ta ce "Ina nan mana, ya aiki ya kwana biyu?".
"Alhamdilillah, gaba ɗaya tun da ƙawarki ta bar gidan nan muka daina ganinki"
"To ai gashi na zo wanke laifina yau, ina fatan mami na nan?".
Ya ce "Eh tana ciki"
Ta ce "Yauwwa na gode" ya buɗe mata ƙaramar ƙofar gate ɗin, ta shiga ciki.
Ɗayan ya kalleshi ya ce "Ka barta ta shiga? Baka kira hajiya bilkin ba, kuma ba ta ɗaga niƙabinta ba".
Habu ya ce "Ai ƴar gida ce, ƙawar maryam ce, tun da tayi aure ne ta daina zuwa".
Ya ce "Ok, na so ta ɗaga niƙabin naga fuskarta, muryarta tayi mini daɗi".
"Ji É—an wahala, ka sani ko yanzu tayi aure, ka shiga hankalinka".
Ummi kuwa sashin mami ta nufa, fasalin gidan yana nan yadda yake, amma yanayin fentin da aka sassauya masa da wasu abubuwan zaka san arziki ya fi na da.
A falo ta tarar da mai aiki, duk da Æ´ar bata san Æ´ar aikin ba, suka gaisa sannan ta tanbayeta ko mami tana nan.
Mai aikin ta ce "Eh, tana falon sama"
"Ki ce mata ummi ce ta zo" mai aikin ta jinjina kai ta nufi ƙafar benen ummi kuma ta zauna.
Bai kai mintuna biyar ba, mai aikin ta saukko, ta ce wa ummi ta shiga.
Ummi ta tashi ta bi bayan Æ´ar aikin.
Da sallama ummi ta shiga, mami ta waiwayo tana cewa "muryar wa nake ji ne haka? Gaskiya koma nayi fushi"
"Tuba nake mami"
Sai dai tana zagayowa, ta tarar da na kan babur da ya kusa tureta da lifan, yana zaune ya barbaje ƙafa a kan centre table, sai yanzu ta gane a in da san shi.
Sai da ya É—an sake É—aga kai ya kalleta shi ma.
Nan suka gaisa da mami, mami nata mitar ummi ta ɗauke ƙafa ta daina zuwa tunda maryam ta bar gidan.
Ummi ta kalleshi ta ce "Ina wuni?"
Ya basar ya ce "Lafiya ƙalau"