Sashe 88
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Raihan ya gyara zamansa ya ce "Wallahi ko dan saboda Alhaji ban so na taho ba, mami ce taƙi tsayawa ta fuskance ni, na rasa yadda zan yi da ita wallahi, taƙi fahimta ta kuma anty rakiya ce take zigata"
"Kai dalla can, na kirata mun yi magana da ita, ba abun da za ta sake yi a kan maganar, ita ba a auren aka aureta? Mu ba auren zumunci ake a danginmu ba, babanka shi ya fara karya mana wannan ta'adar, ya aurota daga nan kowa ya samu Æ´ancin yin hakan, sai yanzu ita kuma ta ce ba za a auro wata ba?"
Raihan ya ce "Abun kuma har da gori?"
"Eh an yi mata gorin, da ai ba ayi ba, siyama na nemanka wai ka je ta girka maka menene oho mata"
Yayi murmushi ya ce "Nifa yanzu abincin kowa ya daina yi mini daÉ—i sai na matata"
"Ka ga fitsararre, amma dai da namun ka ke ci ko? Wai wani matarka ka ga idan ba ka rage rawar kan nan ba a kak yarinyar nan, haka zaku yi ta faÉ—a da babarka"
Raihan ya miƙe ya ce "Ni kaina na sani, ina ƙoƙarin ragewa wallahi, amma hannun ummi akwai maggi ta iya girki sosai"
Hajiya Aisha kawai ta yi murmushi ta girgiza kai, tana sake jinjina wautar mami, a irin wannan stage ɗin, ba a saka pressure wurin cewa lallai sai an tanƙwara namiji, sai nasiha da rarrashi idan ma so take ta soke auren.
Da daddare mariya da kanta, ta gyara katifarta, ummi ta kwanta, ta kawo abun rufa ta lulluɓe ummin, sannan ta rungumeta.
Sai da ta tabattar da mariya tayi bacci, sannan ta tashi zaune ta kira wayar raihan.
Aikuwa a take ya É—aga ya ce "Ina ki ka shiga ne? Tun safe nake kiran wayarki amma shiru"
Ummi ta ce "Albishirinka"
"Goro fari ƙal"
"Na haÉ—u da mama"
Yana kwance ya tashi tsaye, ya ce "Wace maman?"
"Mamana mahaifiya, ashe kawuna ya san in da take, wai dan kar in gudu in ƙi zama na yi karatu ya sanya ya ɓoye mini"
Adduoi na nuna godiya ga Allah ya din ga jerowa, yana hamdala can kuma ya ce "Congratulations to both of us ummi, dan wallahi da al'amarin nake kwana nake tashi, ina tunanin ta ina zamu fara nemanta, Alhamdilillah Ala mun gode wa Allah"
Tare suka din ga murna da raihan a waya, suka gama ta ajiye wayar, ta rungume maman tsam a jikinta, tana tuno irin rabuwa da suka yi, da irin so da ƙaunar da maman nata ta nuna mata.
Bacci suka yi sosai da sosai, babban abun da ya burge ummi, ya ƙara sanyata nutsuwa, duk da rashin lafiyar da maman take fama, tana yin salla, sai dai wasu lokutan akwai kura-kurai sosai a sallar ta ta, amma duk da haka tana kamantawa.
A washegari kawu ya ce zai koma Kano, nan da sati biyu zai dawo ya tafi da ummi.
Yaya maryam ta ce "Dr. Ka tafi da ita kuma, kusan shekara goma sha takwas, ba sa tare kuma ace nan da sati biyu za a zo a É—auketa a tausaya mana dan Allah"
Dr. Ya ce "Eh ai ban gama maganar bane ba, abu na farko ummi tana aiki, in da take aikin kuma sun jin daÉ—in zama da ita, abu na gaba kuma an saka mata rana watanni huÉ—u, kun ga za ta yi shirye-shirye ita da mijinta, daga kano ace ya din ga zuwa maiduguri yayi masa nisa, duk da dole zai zo ya gaisheku"
Anty maryam ta yashe baki tana faÉ—in "Masha Allah, Alhamdilillah"
Malam ma ya din ga murmushi yana sanya albarka.
"To amma, akwai É—an shirye-shiryenmu da muke yi wa yaranmu na aure, ai da an bar mana ita mun yi mata"
Dr. Ya ce "Nan da watanni biyu zuwa uku sai ta dawo nan, ku yi duk shirye-shiryen ku a tsanake"
Yaya ɗan lami ya ce "Amma ba za a ƙara mana ko wata ɗaya ko biyu ya zama nan da wata shida ba, mu gama shirinmu mu ma"
"A'a kar ka damu, in sha Allah babu wani abu da zai gagara, manyan mutane ne, idan muka ce a ƙara zasu ga bamu kyauta ba, hakan ma in sha Allah babu abun da zai gagara"
Suka kammala tattaunawa, suna ta yi wa kawu godiya, ya kama hanya ya koma kano.
Ummi taga gata da ƙauna, babu kyara, babu hantara babu cin zarafi, duk ba a rasa wanda sukan yi maganar cewa ummi ba ta kama da mariya, mariya ta fita kyau da haske, maryam ce ma a tsaye take faɗan kar wanda ya sake yi musu wannan zancen.
Ummi murmushi kawai tayi, dan da ta san abun da tayi going through, da wannan bai É—aga mata hankali ba.
***
A ka yi bikon raihan da ƙyar ya koma kano, Alhaji sai tsokanarsa yake "ni zaka yi wa yaji ko? Zamu gauraya da kai ne".
Hajiya ta ce "Raihan ba a fushi da iyaye, nan gaba kar sake aikata abu makamancin haka"
Raihan ya ce "Hajiya ba fushi na yi ba, na tafi ne dan na je na samu nutsuwar zuciya, amma in sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba"
Cikin tsananin fargaba ya tashi ya nufi sashin mami, ba addu'ar da bai karanta ba, saboda ya san dole ne zuwansa ya tarar da sabon ɓacin rai.
A bedroom ɗin ta ya tarar da ita a zaune, cikin ladabi ya durƙusa ya ce "Mami barka da gida"
Maimakon ta amsa sai ta ƙure shi da ido, da har sai da ya fara tsarguwa.
"Ai gara in ƙare maka kallo, in tabattar da ni na haifeka kuwa? Ba matar ubanka ce kuwa ta haifeka ba ko har ubanka? In haifi ɗa a cikina ya janyo mini zagi da cin mutunci, raihan kana son gamawa da duniya lafiya kuwa? Ka sani sarai matar nan ba ƙaunata take yi ba, ka je ka sameta ka kai ƙara ta ta kira ni ta ci mini mutunci"
"Wallahi mami ba ƙararki na kai ba"
"Yi mini shiru tun kan na fasa maka baki, ka kyauta ba dai wannan mummunar yarinyar ba ce ba, ka je gaka nan gata, amma ka sani babu yawuna babu saka hannuna a aurenka raihan, kuma bayan ka aireta sai ka auri safiyya. Kuma ban lamunci ka yi mata kayan lefe ba, tun da bazawara ce, dubu É—ari biyar É—in ta isa komai da komai"
Cikin damuwa raihan ke ƙoƙarin yin magana, amma ta dakatar da shi, tare da bashi umarnin ya bar mata ɗaki.
Kansa har wani sarawa yake yi, wai ita safiyyan nan dole sai ya aureta kamar wahayi? Baya son ta ba ya ƙaunarta amma an dage sai ya aureta, ga kuma wata magana, wai ba zai yi wa ummi kayan lefe ba, to iyayenta ne zasu saya mata sutura da kayan kwalliyar da za ta yi masa a gidansa? Kuma a wannan marrar nawa dubu ɗari biyar take, da har za ta isa ayi wa ummi kayan lefe, nauyin ai sai ya yi wa iyayenta yawa, shi abun kunya ne ma a gare shi ace bai yi wa ummi kayan lefe ba. Haka yayi ta wasi-wasi yana nazarin abun a ransa.
Farida ba ta damu da in da ummi take ba, sai dai tana tambayar dr. Tana fatan ummi ta tafi kenan, amma yayi mata banza ya ƙyale ta.
Noor kuwa sai bin sa take tana tambayar sa, wai yaushe ummi za ta dawo, ita fa gidan babu daÉ—i idan ummi ba ta nan, ya ce mata zata dawo nan ba da daÉ—ewa ba.
Ummi a gabanta aka fara haɗa kayan turarukan wutanta, wai akwai turarukan da sun fi shekara a binne a ƙasa ana tsuma su.
Yaya maryam ta kasa zama, kullum tana yawon kasuwa ita da mama, matar malam wurin yi wa ummi sayayyar kayan aure.
Ita babban abun da yafi faranta mata, bai wuce kasancewar ta da babarta ba.
Mami ta ƙara matsanta wa raihan, ga gefe guda kuma, Safiyya sai ta wani kira shi wai za ta gaishe shi, duk rashin son wulaƙanta ɗan Adam irin na raihan, ƙarshe sai da yayi blocking ɗin ta, dan ta daina damunsa da kira.
Ya cewa ummi zai zo Maiduguri ya ganta, ya kuma gaida mama, amma gudun matsala ya sanya ta ce masa ya bari ta kusa dawowa.
***
Sai da ummi tayi sati uku cif, sannan dr. Ya koma ɗaukar ta, kamar ta ce masa dan Allah ya barta a nan, amma sai ta ji nauyin hakan ta kasa, kayanta ƙwaya biyu da ta je da su, sai da aka ɗinka mata kusan kala goma a can, kuma tuni suka haɗa kayan gyaran jiki masu haɗe da turarrruka, ummi ta fara amfani da shi.
Yaya maryam sai jaddada mata take yi, kar ta yi wasa da kayan gyaran da aka ba ta ta yi, da sabulan da aka haÉ—a mata.
Mariya ta kalli dr. Ta ce "Ka yi mini alƙawarin ba wurin Iya zaka mayar da ita ba?"
Yayi murmushi ya ce "Ai aronta na ce ki bani, ba zan kai miki ita wurin Iya ba"
"To ai zaka dawo da ita ko?"
"In sha Allah"
"To dan Allah ka kula mini da ita sosai da sosai, kar ka bari ta yi kuka"
"In sha Allah zan kula da ita sosai da sosai"
Ta kalli ummi ta ce "Kar ki yi musu kuka kin ji ummi, ban da ƙyuya da kuka, ba ruwanki da yara, kar ki je su din ga dukanki kin ji ko?"
Ummi ta riƙe hannunta ta ce "To mamana, me ki ke so na taho miki da shi idan zan dawo?"
Ta É—an yi jimm sannan ta ce "Bakomai, ni dai kawai ki dawo, ba dan ina jin kunyar kawu yahaya ba, ba zan bashi ke ba"
Ummi ta cigaba da kallon mariya tana jin daÉ—i.
Da ƙyar suka rabu suka nufo hanyar Kano.
Duk rashin surutun ummi, haka ta sake ta din ga yi wa kawu hira tana bawa kawun labarin mamanta.
Bayan azahar suka sauka a kano, noor kamar ta mayar da ummi cikin ta, dan murnar ta dawo.