← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 134

Sashe 5

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mariya ta ƙara tsananta kula da jan ummi a jiki, babanta ya kaita makaranta, ita kuma ta je ta ɗaukkota, ta daina barin kowa ya raɓi ummi.

Mariya na zaune na ƙoƙarin koyawa ummi assignment a tsakar gida, kasancewar tana aji na uku a sakandare aka yi mata aure, ta iya karatu da rubutu. Iya na zaune suna hira da babarsu magaji da idris.

Ummi taƙi mayar da hankali a kan karatun da mariya take koya mata, sai soshe-soshe take yi, tana ɓata fuska.

"Mamana, wai ba zaki mayar da hankali ba, so ki ke anty ta zane ki?"

"Mama ni bana son makarantar" tayi maganar hawaye na taruwa a idonta.

Cikin damuwa haÉ—i da kulawa ta ce "Saboda me ummina"

Cike da ƙuriciya ummi ta ce "Tsokanata ake yi, mama dan Allah ki mayar da ni fara, kuma ki rage mini ƙibata"

Mariya ta É—an yi shiru sannan ta ce "Ummina, ke fa kyakywar yarinya ce, ai kin san sahabban manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, da nake yi miki tarihi ko?" Ummi ta jinjina kai ta ce "Eh, Ina son tarihi"

"Yauwwa ummina, mai kiran salla a zamanin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, sayyiduna Bilal radiyallahu an hu, baƙi ne, kuma Annabi bai taɓa ƙyamarsa ba, haka sahabbai ma"

Ummi ta yi shiru ta ce "To mama kin ce in din ga son annabi, to masu tsokanata ba sa son annabi ko?"

Shiru mariya ta yi, tana tunanin wane bayani za ta yi wa ummi, dan duk da rashin sakewarta da mutane, idan tana tare da mamanta, akwai surutu.

Iya ta ce "Kin ga kar ki sakawa yarinya wani tunani daban, ki gaya mata gaskiya kawai, mummuna ce ko ki so ko ki ƙi"

Babar su magaji ta kwashe da dariya ta ce "Iya wannan jika taki, ai tun yanzu yakamata a fara nema mata maganin farin jini, dan za ayi gwagwarmaya kan a samu mai so, dan ina jin Alhassan ranar yana cewa; da zai samu igiya da ya zargawa ummi, ya tafi tashe da ita a matsayin ɗan biri" tayi maganar tana ɓaɓɓaka dariya ita da iya, ba tare da tunanin, ya mariya zata ji a zuciyarta ba ko ita yarinyar, ummi tayi ƙuri tana kallonsu, duk da yarinya ce, ta san cin mutunci.

Mariya ta ce "Biri kuma, ummin za a yi wasan biri da ita, kuma ki ke dariya, shikenan bakomai" tayi maganar cikin ƙunar rai, ta kama hannun ummi suka tafi ɗaki.

"Mama, da gaske ni biri ce? M, for monkey na bayan littafina?"

Mariya ta goge hawaye, ta ce "Ummina ke mutum ce, mai kyau sosai da sosai, kar ki sake haÉ—a kanki da biri kin ji ko? Kina da kyau sosai, kalli gashinki fa, duk garin nan kin ga mai irin gashinki?"

Ummi ta girgiza kai alamar a'a.

"Yauwwa ummi, idonki ma mai kyau ne, ina son idonki, duk garin nan babu mai irin idonki".

Ummi ta taɓa idonta ta ce "Sai akuya ko?"

"Akuya kuma?"

"Eh, malamarmu ce ta faÉ—a, ta ce ni da akuya irin idonmu É—aya, eyes sunan ido da turanci in ji anty"

Mariya ta yi shiru tana kallon ummi, yarinyar na cikin taskun ƙalubale, daban-daban, har a kai ga malamarta na kamanta ta da akuya.

Iya kuwa ta cigaba da hurawa balarabe wuta, da shi da mariya, cin kashin yau daban na gobe daban, har Æ´an uwansa ma, ware shi suke a wasu abubuwan saboda ba shi da kuÉ—i, haka zalika mariya ta cigaba da yi wa iyalan gidan bauta, idan anjima su yi mata rashin mutunci, ko a ci zarafin Æ´ar ta a gabanta ba.

Kusan kullum sai ummi ta ce ba ta son makaranta, dan kuwa abun da mariya ta fuskanta, ba iya É—aliban ne ke tsokanarta ba har da malamansu a ciki.

Dan idan ummi ta zo da aikin gida, tayi a gida, sai ta ce ba zata nuna wa malamarsu ba, idan ta tambayeta dalili sai ta ce "Malamarmu cewa take yi in fito gaban Allo, a tafawa ƴar baƙa saran daddawa, ayi mini dariya, ni kuma in yi ta kuka sosai, bana son ana tsokanata"

Ba ƙaramin ɓaci ran mariya yayi ba, Dan haka da kanta ta je makarantar, ta roƙi headmaster, a kan ya taimaka ya tsawatar a kan abun da ake yi wa yarinyar, kar son karatun ya fita daga kanta gaba ɗaya.

Yayi mata alƙawarin yin hakan, sai dai ba ta canza zani ba.

Ummi na ta kaiwa tana komowa a tsakiyar ɗakinsu da safe, kasancewar yau ba makaranta, sai fama take da uban gashinta, taƙi tsayawa a gyara, mariya sai fama take da ita ta nemi wuri ta zauna.

Ta kalli babanta da yake cin abinci ta ce "Baba kafi mama loma" tayi maganar tana dariya.

"Eh mana, baki ga na fita girma ba?"

Ummi tayi dariya ta ce "To ni kuma gaba É—aya Æ´an gidan nan, na fi su loma"

Mariya ta ce "Ke É—in, sai ka ce abinci ki ke ci"

"Mama nafi duk Æ´an yara girma fa"

Babanta ya ce "Kin fi su lafiya ne, kuma kin fi su kyau shalelena"

Ta kama kumatunta ta ce "Iya ta ce bani da kyau ai"

"A'a ke kyakywa ce sosai" miƙewa ummi ta yi ta fita daga ɗakin, tana leƙa baƙon ɗan magen da yake wasa a tsakar gida.

Mariya ta yi ajiyar zuciya ta ce "Baban ummi, kana ganin ummi zata iya samun miji tayi aure?"

Ya kalle ta ya ce "Meyasa zaki faÉ—i haka? Kina mahaifiyar ta, kema kin fara biyewa surutun mutane na cewar Æ´armu ba ta da kyau mummuna ce?"

"Ba haka bane ba, abun yana taɓa ni sosai da sosai, har malaman su ummi su da zasu tsawatar wai har da su a cikin tsokanarta, babar su magaji wai har da cewa Alhassan ya na kiran ummi da biri, kuma ta faɗa suna dariya"

Jiki a sanyaye ya ce "Biri kuma? Cin mutuncin ya kai haka? Wallahi mariya ummi ba mummuna ba ce ba, tana dai da duhu ne, kuma ƙwayar idonta ce da ba irin tamu ba, amma ba mummuna ba ce ba"

Mariya ta numfasa ta ce "Ni ba wannan ba, duk wanda ya ci zarafin ummi, na san bani na halicceta ba, amma abun da yake damuna, a zamanin nan yarinya ta kai mutuncinta ɗakin aure, ya ta ƙare ina ga idan ummi ta samu miji, gaya masa zamu yi ga abun da ya same ta? Idan muna gaya masa waye shaida babu tabbacin a lokacin dukkaninmu da muka sani muna raye. Idan kuma muka rufa, zai yi mata kallon mutuniyar banza, ummi ta san abun da ya faru da ita mummunan abu ne.
Ina tausayawa yarinyar nan abubuwan da suka baibaye rayuwarta, ina tausayawa ƙalubalen da zata fuskanta wataƙila bana nan a lokacin balle na tayata kwasar raɗaɗin, amma ina tausayawa ummi, idan ba ta samu miji mai tawakalli ba, za ta fuskanci wulaƙanci, wa zai so mini ummi tsakani da Allah, ya karɓi ƙaddarar da ta same ta? Wallahi baban ummi ba zan yafe wa yaron nan ba, ya cuce ni ya cutar da rayuwar ummi, ko idan ta ƙara girma zata manta oho, haryanzu bata yadda na bar ta a ɗaki ita ɗaya, an cuce ni" tayi maganar kuka mai ƙarfi yana ƙwace mata.

Balarabe yayi ajiyar zuciya, yana jin ɗaci a zuciyarsa ya ce "Wallahi mariya ni kaina abun nan yana ci mini zuciya, ba yadda na iya, mahaifiyata ta riga ta yi mini kandagarki, ƙetare maganar ta na iya shafar mu baki ɗaya, amma in sha Allah, ina sanya ran Allah ba zai wulaƙanta ummi ba, dan Allah kiyi haƙuri mariya, wallahi idan kina kukan nan, sai na ji kamar na bijirewa umarnin iya, na ɗau matakin abun da aka yi wa ummi".

Ta share hawayen ta, ta ce "Kar ka yi haka, aikin gama ya riga ya gama, ko ka ɗau mataki, wannan wani miki ne a zukatanmu da ba zai taɓa warkewa ba".

Yayi shiru ya zubawa mariya ido, shi kansa ya san mariya ba ƙaramin haƙuri take yi ba, zama da shi. Tsakaninta da shi babu wata matsala, amma azabar wahalar da take a gidan, duk ta rame ta yi duhu, soyayar kirki ba sa samun sakewa su nunawa juna, saboda azabar iya.

Ihun Ummi suka ji, hakan ya sanya su yin rige-rigen fita tsakar gida da gudu.

Ummi suka tarar da Alhassan ɗan wurin saminu, ya tattara gashin ummi, ya murɗe shi a hannunsa, jijiyoyin kanta sun mimmiƙe, duk ta gigice.

A guje mariya ta ƙarasa, ta hankaɗe shi, ta ƙwace ummi da ke kuka.

"Alhassan me ummi tayi maka ka murÉ—e mata gashi haka?"

Cikin fitsara yaron ya ce "ÆŠan magenmu take mana wasa da shi"

A fusace mariya ta ce "Kuma saboda zalunci ka rasa me zaka yi mata, sai izaya da gashinta?"

"To waye ya ce ta taɓa mana magenmu, ana ta nemansa?"

Cikin zafin rai, mariya ta É—auke Alhassan da mari.

Sai da balarabe ya waro ido.

"Tura ta fara kaiwa bango, wane irin zalunci ne haka? Ummi fa Æ´a ce ba baiwa ba, wallahi duk wanda ya kuma dokar mini Æ´a sai na ci ubansa. Dama a ciki nake da kai, na samu labarin kana ce mata matashiyar buranya, uwarka ce mai kama da buranya ba ita ba"

"Wayyo Allahana iya, a taimake ni ta kashe mini ido" Alhassan ya wage baki yana kwarmato"

Bakomai ya hana balarabe taɓuka komai ba, face sanin idan iya ta fito ba ƙaramar tijara zata yi ba, kuma ƙarshe su zata ɗorawa laifin".

Buje a hannu iya ta fito daga banÉ—aki tana faÉ—in "Menene haka? Kashe yaron zaki yi me yayi miki?"

Alhassan ya kwashe ƙarya da gaskiya ya gaya mata.
Chapter 5 · 0% Book details