← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 134

Sashe 101

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Raihan ya jinjina kai, suka ƙarasa gidan sa, tun da raihan ya kirata ya ce mata tare za su zo da Alhaji, ta gama girki, amma ta shiga ƙoƙarin ƙara wasu abubuwan.

Tun da ya zo kanta a ƙasa yake, saboda tsananin kunya, ko sau ɗaya ba ta yadda sun haɗa ido ba, shi duk yadda ake zuzuta muninta shi bai gani ba, sai tsantsar tarbiyya da nutsuwa, kuma tubarkallah shi bai ga wani muni ba.

Yayi musu nasiha sosai da sosai, ya ce raihan ya mayar da shi gida.

Ummi ta ce "Baba na gama abinci, bari na kawo maka"

Alhaji ya ce "Kar ki damu ƴar albarka ta, sauri nake kuma a ƙoshe nake, Allah ya yi muku albarka, ayi ta haƙuri kun san irin auren nan naku, society ɗinmu sun ɗauke shi, kamar wani zunubi, amma tun da bai saɓawa addini ba shikenan.

Da ƙyar ya sha lemo ya tashi, sai dai lemon yayi masa daɗi sosai da sosai, lemon cucumber ne da lemon tsami.

Da ƙyar wannan tarzoma ta lafa, sai dai aka saka ƴan islamiyyar su ummi ba ta haƙuri, kuma suka rubuta takardar ban haƙuri, suka yi signing ba ruwansu da ita ya taho da ita gida.

Bayan ya nuna mata takardar ta jujjuyata ta ce "You go far MD, da duk ba ka yi musu haka ba"

Ya ce "No, abun da na yi dai-dai ne, ba zai yiwu su É—arsa miki wani abu mara kyau game da aurenmu ba, alhalin halataccen aure muka yi ba, kuma gaba ba za su sake yi wa wani hakan ba".

Ta ce "To Allah ya kyauta. Alhaji bai ci abincina ba" tayi maganar a shagwaɓe.

"Bani in haÉ—a da nawa da nasa na cinye"

"Wai ba ka gajiya da cin abinci ne, ka daina zuwa gym ɗin ma, idan ba ka yi wasa ba, sai ka kasa wucewa ta ƙofar falo"

"Eh na ji bakomai, hakan ma normal ne"

Ummi ta ce "Sai na saita maka cin abincin ka, ba zan je da kai unguwa ka bani kunya ba, ace ba ka ƙoshi" ya kwashe da dariya, ya ce "Yanzu ba zan gane wannan ba, sai cikina ya cika tukuna".

Ranar litinin kuwa, ummi ta sha fama da raihan kan ya tashi ya tafi aiki, aikuwa da ya je ya sha aiki sosai da sosai.

Tun da raihan ya koma aiki, sai gidan ya yi wa ummi girma, ba ta aikin komai, duk sai kaÉ—aici ya dameta.

Gashi baƙin da sukan shigo, duk sun daina zuwa.

***
Anty Rakiya ce a zaune tana kallon fuskar mami me É—auke da zunzurutun damuwa.

"Ke yanzu Bilki har matar nan ta samu bakin yi miki rashin mutunci, yaushe ta waye?"

"Anty Rakiya ni ba wannan ne ya dame ni ba, kar bakinta ya tabatta yarinyar nan ta ƙwace raihan na shiga uku, ta ji daɗin yi mini dariya, shi ne babbar damuwata da tashin hankali"

"To wai kin bi shawararin da na baki kuwa?"

"Wallahi na bi, kin san raihan da taurin kai, ban gaya miki ranar da na kirshe shi ba, daga shiga ɗaki ya gudu ba. Ya ce mini ya koma aiki ashe duk ƙarya yake yi, yarinyar nan sumi-sumi, kar in je ta ƙwace shi, tun da sa'arsa ce kuma bazawara wayo za ta yi masa na shiga uku Anty rakiya".

"Ba ki shiga uku ba, ai wanda ya rigaka kwana sai ya rigaka tashi, dole ki samu hanyoyin muzgunawa yarinyar nan, kuma ki fara matsa masa a kan auren safiyya"

Mami ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, in sha Allah zan cigaba da ƙoƙari".

Ranar asabar raihan yana ta murna zai wuni a gida tare da ummi, tana kitchen tana shirya musu breakfast, yana É—aki yana bacci mami ta kira shi a waya wai ya je.

Tamkar ya fashe da kuka, haka ya ji, ya ajiye wayar, yana tunanin meyasa mami take yi masa haka, lallai sai ta shiga rayuwar aurensa da ummi.

Ya lumshe idonsa, ransa babu daÉ—i, ummi ta shigo ta kunna turaren wuta a É—akin.

Ta shiga banÉ—aki ta haÉ—a masa ruwan wanka, ta je kan gadon tana É—an dukan filonsa ta ce "MD, ka tashi ka yi wanka mu karya" juya mata baya ya yi, ya ce "Wake me up in romantic way"

Ta ce "Like how? Ba gashi yanzu ka tashi ba"

Ya juyo ya kalleta ya janyota jikinsa, yayi kissing É—in ta a goshi ya ce "Wake up sweetheart" irin haka nake so.

Ta ce "Ashe ba zaka tashi ba idan haka zan yi maka, yadda nake fama da kai ka tashi, da ƙyar ka ke tashi fa"

Ya ce "A'a idan ki ka yi mini haka sai na fi saurin tashi ai" ya ƙare mata kallo ya ce "Ni gaskiya a daina tashina da irin wannan kayan, ni dressing zaki din ga yi mini yadda ba za ace ki na jin hausa ba ma"

Ummi ta ce "Innalillahi, wai dama haka ka ke, mutum sai tsaurin ido, duk a ina ka san wannan ne?"

Wata irin dariya ta bashi, ya ce "Ai tsaurin ido ya riga ya ƙare tsakaninmu, tun da ni da ke yanzu kin san waye boss, fita fa zan yi"

Ta ɗan ɓata fuska ta ce "Cewa fa ka yi a gida zaka wuni"

"To ya zan yi fita ta kamani, ki yi haƙuri kin ji baby"

Ummi ta kalli fuskar sa ta ce "Yaushe zaka kai ni gida na gaida su mami ne? Kuma ban je na yi wa Kawu da su anty bangajiya ba".

Ya É—an sosa kai ya ce "Haka ne, amma for now ban ji zan iya bari ki fita ba"

Ta marairaice ta ce "Dan Allah"

"Na ji amma da sharaÉ—i"

Da sauri ta ce "Menene sharaÉ—in?"

"Sai kin ce mini baby"  tayi turus tana kallon sa.

Ya ce "Yauwwa ai na san lagonki, and ki roƙe ni in a romantic way, a guje zan barki".

"Dan Allah baby ka bar ni na je na gaida su mami, na je gida na yi wa kawu bangajiya"

Ya girgiza kai ya ce "Ba haka ba, idan kin koyo sai ki tambaye ni, yanzu dai tashi mu je ki tayani wanka" sai da ta É—an matsa daga kusa da shi ta ce "Wanka kuma?" Ya É—aga mata gira.

"A'a zance maka babyn dai" sauka yayi daga kan gadon ya ce "Kina da sauran aiki Salma, ina son soyayya sosai ban sani ba ko dan ban taɓa yi ba sai a kanki, amma ina son gidana ya fi ko ina samar mini farinciki, kar ki saka na fara leƙe-leƙe" ya ƙarasa maganar yana shigewa toilet, a daidai lokacin da ƙirjin ummi ya buga da maganar sa ta ƙarshe.

Shi ya ma manta da ya faÉ—i maganar, ummi kuwa duk ta shiga damuwa, ya gama cin abincin sa ya fice.

Ummi ta zauna ta yi shiru tana tunani, abun duniya ya isheta, tana son yin abun da za ta faranta wa raihan rai, sai dai haryanzu tana tsananin jin kunyarsa. Ta buÉ—e wayarta ta shiga YouTube, tamkar sun san halin da take ciki, ta ci karo da wani video, malamar tana ta bayani a kan kula da miji.
Malamar take cewa "Ƴan mata nawa ya tsallake bai aure su ba, ke ya auro ki ya kai ki gidansa, ko da ya kasance mai kule-kule ke ɗin dai ke ya zaɓa, dan me zai kai ki gidansa ki din ga yi masa gidadanci, ba ko yaushe kunya take da muhalli a aure ba" ummi ta shagala tana kallo, malamar har da demonstration na yadda za a yi wa miji kissa.

Ji ta yi ana danna bell ɗin ƙofar falon, ta ajiye wayar ta tashi ta buɗe.

Ta faÉ—aÉ—a murmushinta, ganin wata babbar mace da wata.

Tayi musu maraba zuwa cikin falon, tana ta jera musu sannu da zuwa.

Matar ta kalleta ta ce "Kin gane ni ne?"

Ummi ta yi murmushi ta ce "Na gane ki, maman bauchi ce, ai ya nuna mini a hoto"

Hajiya Aisha tayi murmushi ta ce "Lallai kin yi kyan kai, ina can ya aike ni bana ƙasar, ban samu zuwa bikinku ba, na je umara daga nan na tafi aiken raihan"

Ummi ta yi murmushi ta kawo musu ruwa, da lemo.

Ta ce "Daga baucin ku ka taho?"

Hajiya Aisha ta ce "Daga can muke, tun safe muka taho ai"

Ummi ta ce "Be gaya mini ba, ai da na ɗora muku girki tun kan ku ƙaraso"

"Be san zamu zo ba shi ma, amma yana gida ai ko?"

Ummi ta ce "A'a ya fita tun É—azu"

Ta kawo musu kayan tea, ta shiga kitchen ta É—ora tukunya.

Siyama ta kalli Hajiya Aisha ta ce "Mummy, ga fa kairun nisa'i in ji raihan, ki ga rashin mutuncin da yake yi mini a kan matar nan, wai duk matan ƙarshen zamani ita suka rako"

Hajiya Aisha ta yi dariya ta ce "Raihan ne fa, haka nima yake ce mini duk ranar da na zo gidansa na ci girkin ummi, wai sai na koma bauci ba yatsu saboda daÉ—i, hannunta akwai maggi"

Suka yi ta dariya, nan da nan ummi ta din ga yi musu hidima, ta kawo wannan ta kawo wancan.

Duk rashin son sakewa da mutane irin na ummi, ta É—an sake da hajiya Aisha, suna ta hirar duniya.

Hajiya Aisha ta kira raihan a waya tana faÉ—an ina ya tafi weekends, ta zo baya nan.

Ya ce mata yana gida, ta ce ita ba zata kwana a kano ba, ya dawo za ta tafi.

Dama duk a takure yake, kiransa kawai ta yi ta zaunar da shi, Safiyya na ta kaiwa tana komowa tayi kwalliya, sai dai ko kallo ba ta ishe shi ba, hankalinsa yana kan wayarsa yana kallon hotunan ummi.

Idan ya kalli safiyya sai ya ganta wani iri, shi dai a wurinsa ya fi ganin kyan ummi nesa ba kusa ba, ita baƙinta ke hana a ga kyawunta, kuma yanzu ta washe ta ƙara kyau.
Chapter 101 · 0% Book details