← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 134

Sashe 79

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya É—ora da cewa "Mahaifiyarka ta fara tutsu, a kan ba ta san lamarin, idan har da gaske kana son yarinyar kana son tainakonta, ka tsaya a kan hakan, ka cigaba da addu'a, ni dai yarinyar ta yi mini, ban ga aibunta ba, wani muni wani waye hotonta da ka nuna mini ban gani ba, ban sani ba ko dan kana sonta ba ka ga munin bane ya sanya nima ban gani ba.

Ka je ka cigaba da shirye shiryen ka, a duba fili É—aya ka gina abun ka yadda ka ke so, ba wata matsala in sha Allah"

Cikin girmamawa raihan ya ce "Na gode sosai Alhaji, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana"

"Amin babban mutum"

Hajiya ta yi sallama hannunta É—auke da tray, da kayan shayi a kai.

Tana ganin raihan ta ce "In fara guÉ—a tun yanzu ne, ko in É—an jira?"

Murmushi raihan ya yi yana sosa ƙeya.

Hajiya ta zauna tare da faɗin "To kai raihan daga ganin ummi, har ce maka fa na yi wa ina yi wa yayanka kamu, kawai sai ka lallaɓa"

Ya ce "Wallaahi hajiya tausayi take bani a lokacin, na din ga damunta har muka fara sabawa. Hajiya ummi na da matuƙar kirki da tarbiyya"

Hajiya ta ce "Sosai kam, ina fatan Allah ya sanya alkhairi, na yi maka murna raihan, in dai mace ta gari ake nema, aka samu ummi to a gode Allah.
Sannan shekarun da ke tsakanin ku ba abun damuwa bane, shekaru lambobi ne kawai, ka riƙe ta ka kula da ita, ni dai ina son ta saboda Allah, tun tana zuwa gidan nan lokacin maryam tana nan, akwai ɗa'a da ladabi"

Raihan ya ce "Kuma wallahi ta iya girki sosai hajiya, ba ki ga yadda take bani abinci ba, ban taɓa cin abinci mai daɗin nata ba"

Alhaji ya dungure masa kai ya ce "Sannu ciki muka kawo duniya " suka yi dariya gaba É—aya, gaba É—aya sai ya manta da damuwar da yake ciki.

Ummi na zaune na tilawar litattafanta na addini, wayarta ta fara ringing, baƙuwar lamba ce, tayi zaton ko raihan ne, dan akwai canza lambobi.

Sai dai tana kai wayar kunneta, tayi niyyar sallama, ta gimtse sallamar jin uwar ashariyar da aka lailayo mata.

"Sannu asararriya ƴar wahala, baƙin kunurci, saboda asara da taɓewa kana da rashin kyakykyawar makoma, ummi ki rasa wa zaki ce zaki aura sai ƙanina ummi, na yi dana sanin saninki, saboda kin zama guzuma muni yayi miki katutu shi ne ki ka yi wa ƙanina asiri, saboda zalamar abun duniya, to wallahi ummi ki kuka da kanki, ko ki janye wannan maganar ta auren raihan, ko kuma in ƙasƙanta ki a idon duniya, in muzantaki kin san zan iya"

Jikin ummi yayi sanyi matuƙa, ta kasa magana, har maryam ta yi tijararta a waya ta gama, ta kashe wayar, kamar shashasha ummi ta bi wayar da kallo.

*Sweetheart, ki yi bacci cikin aminci da salama, zan so kiranki in ji muryar ki, amma na san wataƙila kin yi bacci, ki kula mini da kanki, ina son ki* message ɗin raihan ya shigo wayarta.

Ta miƙe ta tafi gaban mudubin ɗakinta, tana ƙarewa kanta kallo.

'to shi raihan ya aka yi baya ganin munina ne? A wajen ina munin nawa yake da yake ɓuya a idonsa baya gani?'.

Abu kamar wasa, mami ta sako raihan a gaba, ta daina amsa gaisuwar sa, ta daina shiga sabgarsa ta ce lallai sai ya je ya cewa Alhaji ya fasa auren nan.
Duk taurin kan É—a, fushin uwa masifa ne, hakan ya sake jefa shi cikin damuwa da wasi-wasi, idan ta ce ya rabu da ummi, sai ya ji kamar ta ce ya raba jikinsa da rai.
Gefe Hajiya da Alhaji suna ta ƙarafafa masa gwiwa a kan auren ummi.

Ga lokacin kai kuɗi na cigaba da kusantowa, ga pressure office, ga ummi gaba ɗaya ta canza ta koma masa kamar wata baƙuwa, taƙi sakin jiki da shi, kamar ma ƙara nesanta kanta da shi take yi.

Yanayin aiki ya ƙara takura raihan, dan haka ko wurin aikin bai fiye samun damar binta ba, ga yawan barin ƙasar da yake yi.

Gefe guda maryam ta saka ummi a gaba da cin mutunci da zagi na cin zarafi kala-kala, ban da saƙonni da kuma barazana da take yi mata, ummi ta rasa in da za ta saka kanta, daga kuka sai addu'a, dan ta rasa yadda za ta yi da al'amarin gaba ɗaya.

Duk da mami ba ta shiga harkarsa, hakan ba ya hana shi zuwa in da take, da la'asar bayan ya dawo daga aiki, yayi niyyar zuwa yau ya je ya ga ummi, ya nufi sashin mami ya je ya tarar da maryam ta zo gidan.

Sanin halinta ya sanya ya tsuke fuska, dan ya san ba wai zuwan Allah da annabi ba ne ta yi shi haka.

"Mami barka da yamma" banza ta yi masa, daga baya kuma ta ce "Kar ka sake zuwa gaishe ni, muddin ba ka aiwatar da umarnin da na baka ba, bana buƙatar ganinka a sashina ma gaba ɗaya"

Maryam ta kalleshi ta ce "Wallaahi ka bayar da maza raihan, me aka yi aka yi ummi? Meye da ita meye abun burgewa a tare da ita? Sannan menene aibun Safiyya, amma na lura kamar ba a hayyacinka ka ke ba, wannan annakiyar baƙin zaka ɗaukko ka kawo mana mugun iri cikin family, wannan yarinyar da mujiya.....

"Dalla malama dakata!" Ya yi wa maryam tsawa.

"Islamiyyar da ki ka yi ba ta amfane ki da komai ba, da baki san daraja karramawar da Ubangiji ya yi wa ɗan Adam ba, ki tsaya iya matsayinki, idan mami tayi matsayinta ne, ke kuwa ko kusa ko a nesa ba ki da alaƙa da aurena, dan haka ki zuba ido idan zaki iya idan ba zaki iya ba ba zan juri cin zarafin matata ba, idan kin yi mata a baya ba ta da bakin ramawa, ni dai-dai nake da ke"

A tare suke shiga karanto "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"

Mami ta ce "Au raihan har ta zama matarka ma ashe? Yanzu a gabana ka ke gaya wa Æ´ar uwarka haka saboda yarinyar da ba ka aureta ba ma? A wayance kana nuna mini babu gudu ba ja da baya kenan sai ka aureta" raihan ya yi shiru yana huci.

Maryam ta ce "Taɓɗijan, akwai ƙura mami, ita ma munafuka na kirata a waya ta ƙi magana, da yake ba ta da gaskiya, munafuka uwar son abun duniya, sumi-sumi da ita garin yayime-yayime na, na yayimo mana masifa"

Cewar ta kira ummi ya fi komai É—aga masa hankali, ya san dole sai ta yi wa ummi rashin mutunci.

Juyawa yayi da sauri ya fice, ya tafi É—akinsa ya sauya kaya, ya É—au babur É—in sa ya fita.

Gidansu ummi ya tafi, ya yi sa'a security yana nan, ya ce masa ya yi masa sallama da ummi.

Jin ana sallama da ita, ya sanya farida kallon ummi da take ta aiki a falo.

Farida ta kwaɓe baki, haka ma kausar, kausar ta ce "Ohh su mujiya an yi abun arziki, kowane mai tsautsayin ne? Na ga dai wancan tsohon ya ce ya fasa"

Farida ta ce "Oho dai, ni dai ayi a tattara a bar mini gida"

A gaggauce ummi ta gama, ta je É—akinta ta shirya, ta fito harabar gidan, ya mayar da hankali a kan wayarsa yana dannawa.

Ƙamshin turaren wurinsa da take yi, ya sanya shi ɗagowa, ya zuba mata ido.

Duk ta yi wani iri, alamu sun bayyana ƙarara a cikin damuwa take.

"Sannu da zuwa" ta faÉ—a a hankali.

"Yauwwa, ya ki ke ya gidan?"

"Lafiya ƙalau" ta amsa tana murza yatsunta.

"Kwana biyu ayyuka sun yi mini yawa sosai ban samu na zo na ganki ba, zuciyata duk a takure"

Ita dai ummi ta yi masa gumm, taƙi magana.

"Yaya ummi" ya kirata da sunan da ya saba a baya.

Ta É—ago ta kalleshi, ya ce "Meyafaru ne? Duk kin canza mini, kamae an canza mini ke, meyafaru ne?"

Kamar ya soso mata in da yake yi mata ƙaiƙayi, ta ce "Dan Allah, ka taimaki rayuwata ka fasa auren nan raihan, wani ƙalubalen ne yake tinkaro ni, kamar ba zan iya ɗauka ba, Astagfirullah idan ka aureni kamar sabon babin ƙaddara zan buɗe, da alama kai kaɗai ka ke so na, gidanku ba zasu karɓe ni a matsayin sirika ba"

Ya jinjina kai ya ce "Eh, thank God tun da ina son ki ni, na san akwai ƙalubale, maryam na san ta kira ki, haka zalika na san mami kin ji abun da ta ce ranar, amma duk ba matsala ba ne ba. Salma ki canza rayuwarki ki koyi tsayawa a kan ra'ayinki da abun da ki ke so duk tsanani duk ƙalubale. Ke kin san ko mata huɗu na ce ina so za a bani a garin nan, amma na tsaya kai da fata na ce sai ke, ni meyasa zaki watsa mini ƙasa a ido? Ummi ba wasa nake yi ba da nake nanata miki ina son ki, ni kaina fa a cikin ƙalubalen nake, amma na ji zan jure saboda ke. Dan Allah ummi kema ki koyi tsayuwa a kan ra'ayinki ba ra'ayin wani ba, ita maryam ɗin waye ya hanata auren wanda take so, sai ke?
Dan Allah ki manta da wani ƙalubale mu tsara rayuwar mu, jarrabawa ba ta ƙarewa a rayuwar mumini.
Ai ki na so na ko? Tayi shiru tare da haÉ—e rai.

"Ba kya so na saboda na yi miki yarinta ko? Headmaster ki ke so?"

Ta É—aga kai alamar eh.

"Ko gidan tsohon mijinki ki ke son komawa" yadda ya ga ta razana ne abun ya bashi mamaki.

Ya kawar da zancen ya ce "Ni a wani bugiren ki ka ajiye ni?"

Bai yi tsammanin za ta bashi amsa ba, ya ɗora da cewa "Ƙanin ki ko, wanda ki ka raina da aure?"

Zumɓura baki ta yi, tana juya ƙwayar idonta a hankali.

"Ummi wai meyake damunki ne? To mu yi hira ta yaya da ƙanwa kamar yadda muka saba"
Chapter 79 · 0% Book details