Sashe 39
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kasancewar fitar sassafe yayi, yana gama abun da zai yi ya dawo kano, a falo ya yada zango, ummi tuni ta gama girki tayi shirin tafiya islamiyya, ya tsareta a falon yana bata labarin saƙon ƴan gidan na gaisuwa a gareta.
Ganin yadda ummi ta É—an sake da kawu yahaya, har tana tambayarsa wasu daga mutanen gidan, ya sanya farida yi mata tsawa, ta ce ta tashi ta tafi makaranta.
Abdul ya shigo da noor a hannunsa, ummi tayi saurin karɓarta, ta ɗan ɗagata sama ta ce "Mamana tafi ta kowa" noor kuwa ta buɗe baki tana dariya.
Wata irin zabura farida tayi, tun da ummi take kiran noor da maman wasu lokutan, ba ta taɓa kawo sunan mahaifiyar ummi bane ba sai yanzu, tayi wata irin zabura ta ce "Dr. Sunan matar ƙaninka ka saka wa noor? Babar ummi?".
Kai tsaye ya ce "Yes"
"Saboda me? Meye alaƙata da ita? Ita tayi mini cikin? Ko ita ta haufa mini, wai tsaya meye alaƙarka da ita?".
"Alaƙar da ki ka faɗa mana, na kawo miki amanar yarinya kina ta wulaƙanta ta, gashi tana ta yi miki bauta kamar baiwar da ki ka sayo da kuɗinki, dan haka na saka mata sunan mahaifiyarta, atleast ta samu ƴar uwa, kuma wadda zata din ga kallo tana jin daɗi".
"Yahaya gaba ɗaya na kasa gane kanka, na rasa in da ka dosa a kan yarinyar nan yanzu saboda tsabar wulaƙanci da rashin mutunci, matar da ban sani ba kawai ka saka wa ƴa ta sunanta? Ni wai wace irin alaƙa ce tsakanin ka da ummin nan, ko zagata ka ke yi ne ban sani ba, da a duniya kullum abun da zai faranta mata kawai ka saka a gaba?".
A fusace ya ce "Wace irin maganar banza ce haka farida"
"Ba wani maganar banza, maganar gaskiya dai, to ga noor É—in nan na bar mata, ta je ta raine ta na bar mata, tun da sunan uwarta ne ba na uwata ba".
Duk da ummi a tsaorace take rungume da noor, jin kawu yahaya suna faɗa, sai dai jin abun da farida ta faɗa, ya sanya cikin wauta da ƙuruciya, ta risuna ta ce "Anty na gode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya jiƙan magabata na gode in sha Allah zan kula da ita, a bani kayanta da abincinta na gode" a zaton ta da gaske ta bar mata noor.
Kawu yahaya duk da a fusace yake, sai da yayi dariya, aikuwa cikin ɓacin rai farida tayi kan ummi, ta fizge noor ta ce "Ai ba uwarki ce tayi mini naƙudar ba"
Kawu yahaya ya ce "Ummana, jeki makarantar ki kin ji" ta É—auki jakarta, ta fita cikin damuwa.
Ummi ba ta cika makara ba, dan haka da wuri ta je makarantar islamiyya.
Zama tayi ita kaÉ—ai, tayi shiru tana tunani, tana son sake yi wa kawu yahaya maganar ya gano in da mamanta take? Sai dai ta kasa tana jin nauyinsa, shi ya ce mata ta bashi lokaci, dan haka ba ta son cigaba da takura masa.
"Ummi" maryam ta kira sunanta.
"Na'am" ta amsa a taƙaice.
"Taso ga mami can ta zo, ita ta kawo mu, ta ce yau dai tana son ta ganki"
Jin mahaifiyar maryam ce ke son ganinta, ya sanya ta tashi da sauri, dan duk in da aka ce wannan babba ne mussaman sha'anin uwa, ummi na bashi girma sosai da sosai.
A ƙofar makaranta suka tarar da mamin a wata zuƙeƙiyar mota, suka ƙarasa gaban motar, ta buɗe ƙofar motar tana murmushi.
Ummi ta durƙusa ƙasa ta ce "Mami ina wuni"
Matar ta ƙarewa ummi kallo, sannan ta yi murmushi dariya na neman suɓuce mata ta ce "Lafiya lau ummi, ya gida ya makaranta?"
"Lafiya ƙalau, Alhamdilillah"
"Yau Allah yayi na ga ummi, kusan kullum sai tayi zancenki a gida"
Ummi tayi murmushi tare da sunkuyar da kanta ƙasa.
"To Ubangiji Allah yayi muku albarka baki É—aya, ina fatan wataran kuma zaki kawo mini ziyara gida"
Ummi ta ce "To, zan tambaya idan aka bar ni zan zo in sake gaishe ki"
Tayi murmushi ta ce "Masha Allah, ku koma aji to, Allah ya yi albarka"
Ummi ta amsa da "Amin ya Allah na gode, Allah ya tsare hanya"
Maryam ta ce "Bye bye mami, drive well"
Ta amsa mata da "Thank you dear"
A haƙiƙanin gaskiya maryam bata da aiki sai bayar da labarin baƙin ummi, da gidadancinta da rashin wayo, da yadda take kullum cikin kuka, abu kaɗan sai ta hau kuka, da irin yadda malamai kan yi mata ba'a, ko yadda su kan su ɗaliban ke attacking ɗin ta, amma ba ta iya cewa komai.
Babban abun da ya burge mamin da ummi, shi ne nutsuwarta, da kuma gudun duniya da ta gani yau da wanda take jin labari a wurin Maryam.
****
Yau babban burin Idris ya cika, dan kuwa ya hilato hindu shagon wani abokinsa, ya aiwatar da abun da yake muradi a kanta.
Hindu tayi kuka kamar ranta zai fita, sai dai ya zuba mata ido, a tunainsa yanzu hankalinsa zai kwanta, sai dai ina, kasancewa da ummi kawai yake burin yi.
Duk da babu abun da ya shiga tsakaninsa da ummi, yana jin kamar akwai wani abu na musamman da ummi ke da shi, da baya tunanin ya samu a tattare da hindu.
Iya taushin fatar ummi ya isa saka mutum annashuwa, ya daÉ—e yana jin haushin kansa, da har suka rabu da ummi, bai amfana da ita ba.
Kukan hindu ne ya dawo da shi hayyacin sa, ya din ga lallaɓata yana bata haƙuri, tare da yi mata alƙawarurruka kashi-kashi irin na yaudara.
Tun da farida ta san sunan babar ummi, aka saka mata, ya sanya ta ƙara tsananta ƙiyayyarta ga ummi, azabtarwa iri-iri.
Rayuwa ta cigaba da garawa, sai dai al'amura sun tsananta ga ummi, lokacin da dr. Ya samu canjin wurin aiki, daga Kano zuwa kaduna, wasu lokutan sai yayi wata guda bai zo gida ba, wasu lokutan kuma ya kan zo weekends.
Idan ummi ta karaya ta ji kamar ta mutu ta bar duniya ta huta, sai kuma taga wahalarta ta tashi a banza kenan, ba ta yi acheiving komai a rayuwa ba.
Ko ina babu daÉ—i, gida azaba da wahala, makarantar boko, ba'a, cin zarafi daga É—alibai har ma da malamai wasu lokutan, sukan aibata ta ko su muzantata da halittarta.
Sai da ta kai ta kawo, kuÉ—in makaranta idan dr. Ba ya gari, idan ya turowa farida, ba zata bawa ummi nata ba, har korota ake yi daga makaranta.
A ci mata mutunci, Saboda rashin biyan school fees, sai da ta kai Maryam ta saka babansu biya wa ummi kuÉ—in makaranta.
Shugaban makarantar ya hana malamai korar ummi, a duk lokacin da ba ta biya kuÉ—in makaranta ba, sai ya yi wa kawu yahaya waya, sai a lokacin dr. ya san abun da yake faruwa game da kuÉ—in makarantar ummi da yake bawa farida ba ta bata, daga nan har makarantar boko, direct transfer yake yi musu.
Duk wani aiki ko aike da yakamata namiji yayi ga Abdul, ummi ce za ta yi shi, sayen fetur, cefane, refilling É—in gas, duk ummi ce ke yin sa, intee da kausar babu abun da suke tsinanawa a gidan nan, ko É—auke cokali kuwa a kan hanya, saboda azaba har tayar da inji sai da ummi ta iya.
ƙawayensu intee idan suka zo, su yi ta nuna musu ummi a matsayin ƴar aikin gidan su.
Allah ya taimaki ummi, aka sakawa rahama ranar aure, ta din ga murna ta san ko ba komai ta É—an samu rangwame.
Gefe guda soyayya da shaƙuwa mai ƙarfin gaske ta shiga tsakanin ta da noor, noor komai ummi, kai ka ce ummin ce ta haifeta ba farida ba, dan ita ce ta yaye noor ma.
Ummi na ta aiki a kicin da safe, ta je ɗakinta ta dawo, ta zo ta tarar da ƙwai guda biyu a kan drower kitchen, ita dai ba ta ajiye ƙwai ba, dan haka ta kai hannu ta ɗau ƙwan tana duddubawa, rubutu ne a jiki, an zana wani hatimi da sunan wanda rahama za ta aura, har da zanen kan ƙwarangwal.
"Ke!" Tsawar da farida ta daka mata, ya sanya ta zabura ta saki ƙwan ya faɗi ya fashe, maimakon ruwan ƙwai ya fito, sai jini da wani baƙin abu ya tsiyaye.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai wace irin karfa ce ke ne?"
Cikin magiya ummi ta din ga bata haƙuri, amma tsabar mugunta matar nan ta ɗauki muciya ta din ga bugawa ummi.
Abdul yana falo yana video game, ya shigo kitchen ɗin da sauri ya tarar da ita tana ta bugawa ummi muciya, tana ƙoƙarin karewa.
"Maama lafiya, meyasa ki ke dukanta da muciya"
"Dalla rabu da ni, na gaji da abubuwan da yarinyar nan take yi mini"
"Amma maama bai kamata ki dake ta da muciya ba, idan kuma ki ka ji mata ciwo fa?"
Cikin ko in kula ta ce "Na daki banza"
Tayi maganar tana sake kwaɗawa ummi muciyar iya ƙarfin ta.
"Maama dan Allah ki daina cin zalin anty ummi, wannan CUTARWA! ce, maybe tsautsayi ne ya sanya ta yi miki laifin"
A fusace ta ce "Ni ka ke gayawa ina cin zalinta?" Tayi maganar tana nufo shi.
Babu tsoro ko fargaba ya ce "Idan ba CUTARWA! ba ce dai-dai ne Allah ya sa a yi wa intee ko kausar abun da ki ke yi mata" sak tayi tana kallon Abdul, ba ta taɓa zaton wannan maganar daga bakinsa ba.
Ta ji jikin ta ya yi sanyi, ta jefar da muciyar ta fice.
Ya girgiza kai shi ma ya fita, dan kunyar ummi ma yake ji, bai san me zai ce mata ba, saboda abun da mahaifiyar su take mata.
BAYAN SHEKARU BIYU
***
Ummi na tsaye a gaban mudubin É—akinta, tana ta aikin taje gashin ta, ta nemi wuri ta zauna tana kallon kanta a mudubi, gashin duk ya rufeta, ta sunkuya tana cire gashin da yake jikin comb É—in, ta tare shi a gefe sannan ta nannaÉ—e gashin kanta ta tufke shi.
Ta sanya doguwar rigar shadda brown, ta kawo dogon hijjabi milk ta saka, ta ɗauki niƙabinta ta sanya.