Sashe 104
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Gaskiya dai, ki din ga biyana ina yi miki wankan, na shafa miki kayan shafe-shafen naki, kuma in yi miki wanka, ki din ga biyana, idan ina yi miki sai kin fi fita"
Ummi ta ce "Hmm kalli agogo, sai makara ka ke yi, kuma sai na kira Alhaji na gaya masa wasa ka ke yi da aiki, ba ka fita da wuri"
Yayi dariya ya ce "Sai in ce masa ke ki hana ni fita, ki ka tsare ni da soyayya, na kasa fitowa" miƙewa tayi ta ce "Kai ba ka jin kunya fa ko?"
Kamar ba za su rabu ba, haka ya shirya suka fita falo, ta raka shi har gaban motarsa ya tafi.
Ta koma ciki tayi ta fama da aiki, dan kaf É—akunan gidan nan, kullum sai ta shiga kowanne ta gyara.
Wajen ƙarfe sha biyu ta kammala aikinta, ba ta karya ba sai a lokacin ta yi farfesun kifi da dankali, ta koma falo ta zauna tana karyawa, ga ƙamshin turaren wuta yana tashi, ga Tv tana yi.
Ta ƙarewa falon kallo, ta kalli kwanon hannunta, ta yi murmushi ta ce "Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabatta gareka, tsarkakken sarkin da babu wani kafinsa kuma babu a bayinsa, Sarkin da ni'imarsa da yalwarsa ba su da iyaka" ta furta hawaye na taruwa a idonta, ba ta taɓa tunanin irin wannan rayuwar ta ƴanci ba.
Ta É—aga wayarta ta kira maiduguri, sun daÉ—e suna gaisawa, bayan sun gama ta kira raihan.
Sun daÉ—e suna waya, suna hira sai da ya ce mata zai shiga meeting sannan ta katse wayar.
Kasancewar kifin da ta É—iba tayi farfesu da yawa raihan ya kawo, dan haka ta tsiri yin girki da kifin, a cewarta a kai wa dr. Wani wani kuma a kai gidan su raihan. Dan raihan ya riga ya bata damar duk lokacin da take son yin alkhairi, ya baga dama ba sai ta tambaye shi ba.
Tun la'asar da raihan ya dawo gida ya ci abinci, take lallaɓa shi ya kai abincin nan, amma sai yawo yake yi mata da hankali.
"Dan Allah MD ka kai abincin nan kar yayi sanyi"
Ya ce "Zan kai, yauwwa tafiyarmu fa sai next week in Allah ya kaimu"
Jiki a sanyaye ummi ta ce "Ka gaya wa mamin zancen tafiyar ne?"
"Meyasa ki ka damu ne? Zan gaya mata in sha Allah, kar ki damu ba wata matsala in sha Allah, zan kai abinci da daddare yanzu so nake na kasance da ke, wuni muka yi fa ba ma tare"
Ta yi shiru ba ta ce komai ba, ya fuskanci ta na tsoron abun da ka iya biyo baya idan ya sanarwa da mami zai tafi da ita china, dan ita a so samunta kawai ya ƙyaleta shi yayi tafiyar sa.
A booth É—in mota ya tafi da abincin sallar magariba, bayan ya idar ya fara zuwa gidan su ummi, sannan ya tafi gidansu.
Bai san Alhaji ya gaya wa mami zancen tafiyar ba, ya fara shiga sashen hajiya, suka gaisa ya ajiye mata abincin, dan ya san idan ya kai wa mami, ba burgeta zai yi ba ƙarshe ta ci zarafin Abincin ma.
Bayan sun gama gaisawa, ya shiga sashen mami, sai dai yanayin fuskarta ya nuna masa akwai matsala.
"Ina wuni mami?"
"Nemi wuri ka zauna" tayi maganar ba tare da ta amsa masa ba.
Ya zauna yana satar kallonta.
"Ni na haifeka ko waccan mummunar yarinyar?"
"Wace irin tambaya ce haka mami, me kuma tayi?"
"Yanzu raihan ka yi riƙar da zaka tsallake maganata ka ce zaka ɗauketa ka tafi china, tawa maganar ka banzantar da ita ko?"
Raihan ya ce "Wallahi mami Alhaji ne ya shirya tafiyar, ba laif....
"Rufe mini baki ina magana kana magana, na kusa kawo ƙarshen auren nan, na fuskanci ba haka suka ƙyaleka ba, tun da ka fara bijire mini, kama aure kai da Safiyya babu fashi, umarni nake baka ba shawara ba, na soke tafiyar nan" yayi mata shiru, ta ci masa mutunci daga shi har ummi, tare da aibata ummi yadda take so, tayi ta gama bai tanka mata ba, ya tashi ya bar falon.
Bayan fitarsa Nihal ta fito ta ce "Mami, dan Allah ki din ga sassauta adawa da auren nan, kina gani fa kin gama banbamin ki, ko amsa bai baki ba ya tafi"
Mami ta ce "Shi ya isa, ban haifi É—an da zai bijire mini ba a kan mace wallahi"
Nihal ta kalli mami ta ce "Idan kuma safiyyan ma yayi mata haka fa, ya so ta kamar yadda yake yi wa wannan? Tun da kin ga yanayin halinsa É—aya da Alhaji"
Mami ta ce "Gara safiyya wannan ai tawa ce, ba wani abu"
Nihal ta numfasa ta ce "Mhmm to mu kuma fa? Wasu fa zamu aura, mu ma ayi mana yadda ki ke yi mata kenan?"
Cikin mamaki ta ce "Au goyon bayan sa ki ka fara kenan ya wulaƙanta ni?"
Nihal ta yi murmushi ta ce "Ahh haba dai, kawai dai wani hasashe nake yi ne, Allah ya kyauta"
Ummi kuwa ta sha kwalliyar dare, tana jiran dawowar raihan, amma yanayin yadda ya shigo ya tabattar mata da akwai matsala, ko kallon in da take bai yi ba, ya wuce wani bedroom É—in.
Jikin ummi yayi sanyi sosai, ta shiga tunanin ko ta yi wa raihan wani laifin, amma ta ga lafiya ƙalau suka rabu, hakan ya tabattar mata da ba ita ta yi laifin ba.
Bayan mintuna talatin, ta je ta leƙa ɗakin da ya shiga, ya kwanta yayi ruf da ciki, ta na son shiga amma idan yayi irin wannan burkicewar tsoronsa take ji, dan haka ta ƙyale shi.
Da safe ma ko karyawa bai yi ba, dan tana kitchen ya tayar da motarsa ya fice, sai ta ji gaba É—aya duniyar ta yi mata zafi, kamar ta É—ora hannu a ka tayi ihu.
Raihan kuwa ga damuwar abun da mami tayi masa, ga tausayin ummi yake ji, har cikin ransa yake jin idan ya auri Safiyya ba zai yi mata adalci ba, dan jin ummi yake yi a kowanne sashi na zuciyarsa, haka zalika ma yaushe ya auri ummi, da har za ace ya kawo wata?.
Ya ji ba zai iya cewa ummi ya janye tafiyar su ba, hakan kamar zubar da kimarsa ne tare da kimar ita kanta mamin da ta kasa gane hakan, dan haka ya ji bai zai iya cewa ya fasa tafiyar nan ba da ummi, ya san duk abu Alhaji zai tsaya masa.
Sai ƙarfe huɗu na yamma ya dawo gida, ya kwaso gajiya sosai da sosai, sai dai kamar mai aljanu ya koma normal har yana ce mata gajiyar da ya yi kamar yayi gudun kwana biyar.
Ta biye masa ya gama cin abinci, ya koma falo zai yi kallo, amma ta bar falon ta koma bedroom.
Ya bita É—akin ya tarar da ita ta fito da kayan wardrobe tana gyarawa.
A ɗan shagwaɓe ya ce "Yanzu fisabilillahi ba ki yi aikin bana nan ba, sai yanzu da na dawo, sonake ki zauna a kusa da ni mu yi hira" ta ɗago da idanunta ta kalleshi, ta kawar da kanta tana tura baki ta cigaba da aikinta.
Ya ƙarasa gabanta yana cewa "Wai madam ya ne? Me na yi miki ne?"
Cikin rauni ta ce "Kai zan tambaya me na yi maka? Kawai ka share ni, har da canza ɗaki kuma ni ban san me na yi maka ba, sai yanzu zaka din ga yi mini wasa ba zan yi hirar ba" tayi maganar har muryarta na rawa saboda shagwaɓa.
"Ohhh sorry kairun nisa'i, ba ki yi mini laifi ba, ba na son laifin da ba naki ba ya shafe ki ba ne, kin san idan ina fushi sai a hankali yanzu ba gashi na saukko da kaina ba, ai idan ke ki ka yi mini laifi ke zan yi wa, bana son in ɓata miki rai ne alhalin ba ke ki ka yi laifin ba".
"Ni ba ruwana da kai, har da wani canza É—aki, to ka tafi kenan kwaso maka kayanka zan yi na mayar maka É—akin da ka kwana, nima na huta"
Ya kwashe da dariya ya rungumota jikinsa ya ce "Ke idan wani ya gaya miki wannan tatsuniyar zaki yarda? Raba ɗaki da ke, ke ko a baki ya yi miki ma'ana? Iya wuya muna tare sai dai ki yi ta haƙuri. For now dai a yafe mini laifina"
Ta É—aga kai ta kalleshi ta ce "Bribe me tukuna"
"Da me?"
Cikin nutsuwa ta ce "Ka fasa tafiya da ni, saboda hankalin mami ya kwanta bana son ta yi mini fushi da kai"
Yayi saroro yana kallonta, ya maze ya ce "Ba na ce miki zan kula da komai ba? ba zata ƙi ba ai"
Tayi murmushi ta ce "Na san a kan maganar ne ka yi fushi jiya, idan damuwarka ta wurin aiki ce ina ganewa, haka idan da mami ne dan Allah ka yi haƙuri, wallahi ba wani abu ka je ka dawo".
Raihan ya ce "Ba yadda ki ke tunani ba ne, za ta amince fa, honeymoon zamu je"
Ta waro ido ta ce "Wane honeymoon kuma? Me ya rage kuma wani honeymoon zamu je, ai ka gama honeymoon É—inka a nan"
"A'a fa, ga aiki ga stress, gara muje mu samu cikakken lokacin cin soyayyarmu ba hayaniya" yayi maganar yana sumbatar bakinta.
***
An kai ruwa rana sosai da mami a kan tafiyar nan, Alhaji ne ya tsaya tsayin daka a kan tafiyar, ya ce idan raihan ya dawo ayi zancen auren safiyya.
Duk da farida ta san sirikar ummi ba ta sonta, amma ba ta zaci ummi za ta samu kwanciyar hankali da nutsuwa haka ba, Ummi ta je ta yi musu sallama a kan tafiyar su china. Duk wanda ya san ummi a baya ya ganta yanzu ya san a cikin ni'ima take, iya kyan da fatarta tayi ka san tana samun kulawa.
Noor ta din ga murna, jin ummi za ta je china har da cewa ta gaisar mata da su bursuli.