Sashe 68
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Raihan, shine ka bawa Yaya Abdul wannan kayan ya kawo mini, idan aka tuhume ni a ina na samu me zance? Kar ka janyo mini matsala fa"
"Kar ki ji komai ki ce ni na saya miki, saboda na fuskanci kina so, budurwa ce ke ba tsohuwa ba, dan haka mace sai da kwalliya, ni ina da yayye da ƙanne mata, duk in da mace take tana buƙatar kulawa, a kan buƙatunta na yau da kullum, kar ki ji komai yayata, ki yi kwalliyarki dai-dai da addinin musulunci, Allah ya kawo mana abokin rayuwa na gari" maganar sa ta ƙarshe, da yayi addu'ar sai ya ji wani abu mara daɗi a ƙasan zuciyarsa.
Ya kashe wayarsa, ummi ta bi kayan da kallo, ina ma zata iya amfani da kayan nan, ta tashi ta kulle ƙofar ɗakin, ta ɗauki kayan tana gwadawa ɗaya bayan ɗaya, karo na farko da ta ɗauki jambakin da yasa mata wancan karon, ta ƙara tisa shi a kan jajayen laɓɓanta, ta saka kwalli a idonta.
Ta ƙurawa kanta ido a gaban mudubin, ta din ga juyi a tsakiyar ɗakin, wai yau ita ce ta saka wannan kayan masu tsada, ta kalli takalmin ƙafarta mai tsini, ta din ga kaiwa tana komowa a ɗakin.
"Allah ya ƙaro maka arziki mara yankewa, ya yalwata maka duniya da lahira" hakanan ta ji ina ma ya ga kayan a jikinta, har da janbaki ta saka yau, abun da yake so ya mayar da ita ƴar gayu.
***
Gaba ɗaya farida ta kasa sukuni, tun da mijin inteesar ya ce zai ƙara aure, suke yawon neman asiri, amma babu abun da ya sauya, ga azabar takura daga dangin miji, da gori na cewa ita juya ce.
Da ya ce kan ya ƙara auren zai canza mata gida da furnitures, amma babarsa ta ce bata yadda ba, da wanne zai ji, kuɗin da zai kashe yayi wani auren, ko kuma wanda zai kashewa juya, da ma tana haihuwa ne da sauƙi.
Gefe ga kausar dr. Ya ƙara hura mata wuta, a kan lallai ko tayi karatu, ko sai ta fitar da miji.
Farida kuma ta yi alwashin, sai ummi ta koma ƙauye ta bar mata gida, ko kuma ta fitar da miji itama, dan ba zai yiwu ya takura wa ƴar ta ita kaɗai ba.
Ga noor wani irin rashin ji take yi, ba ta shakkar farida ko kaɗan, tsagera ce ta gaske, ummi ce kawai sai dr. Suke iya tanƙwarata, dan ko Abdul sai ta ga dama take jin maganar sa, dan ta ce faridan ba ta sonta, su inteesar kawai take so, ita kanta ummi tsagerancin da noor take yi da ƙanan shekarun nan, yana bata tsoro, amma babu yadda ta iya, tana yi mata addu'a, tare da yi mata fatan shiriya.
Gashi farida ta É—ora laifin hakan a kan ummi, wai ita take zigata, take hurewa Æ´ar ta kunne.
Kamar a baya da duk abun da za ayi ummin ba magana take yi ba, haka yanzun ma, ba wani abun take cewa ba, duk abun da za ayi sai dai tayi shiru.
Babban abun da ya É—aga mata hankali, bai wuce kawu Yahaya da ya je gagarawa, ya dawo da katin bikin Yaya magaji ba, kuma ya tabbatar mata da ita za su je bikin nan, kuma a yadda yayi maganar umarni ne kawai ba wai neman yardarta ba.
Ta amsa masa da to, amma ƙasan zuciyarta wani irin lugude take yi da fargaba, da fatan Allah yasa ba da sun je za a baro ta a can ba, dan kuwa farida ta ƙara matsa lamba sosai da sosai, ta addabi ummi da gorin rashin aure da kuma ƙara tabattar mata da barin gidan.
Gefe guda kuma, abokin shawarar ta ta, ya zama very busy, wataran sai su wuni ma basu yi waya ba, ga tafiye-tafiye da suka sako shi a gaba, saboda importing na kayansu, nan da nan kuwa ya fara rama, duk ranar da zai dawo gari, sai ya yi wa ummi waya tayi masa abinci, ya aika a karɓo masa ba zai ci na gida ba.
Alhaji Tahir ya sha suka da caccaka, a kan yadda ya ɗauki ragamar babban kasuwanci kamar wannan, ya danƙawa raiha, a matsayinsa na ƙaramin yaro, Alhaji Tahir ya toshe kunnensa, dan kuwa bai ji zai canza ra'ayi ba.
Abunka da mata da miji, mami tayi ta lallaɓa Alhaji, har ya amince da maganarta a kan raihan yayi aure, amma ya ce ba ruwansa da zaɓa wa raihan ɗin matar aure, balle auren yaƙi daɗi ace laifinsa ne.
Shima Alhajin yayi iya ƙoƙarin sa wurin fahimtar da raihan muhimmancin ace yana da iyali yanzu, tun da ya samu matsayi.
Raihan ya ce "Wai Alhaji da wanne zan ji?, tsufa zan yi da wuri, ka manta nauyin da ka É—ora mini?"
Alhaji ya ce "Ni meyasa ban tsufa da wurin ba?akwai riba a cikin yin aure da wurin babban mutum, aure ba takura bane ba, kwanciyar hankali ne da nutsuwar zuciya ka yi tunani a kai".
Raihan ya ce "To Alhaji zan yi, zan yi shawara da hajiya"
Alhaji ya ce "Ba maminka ba?".
"A'a Hajiya"
"ÆŠan gidan Hajiya, ni ba zan bayar da shawara ba sai Hajiya kenan? Ai shikenan babban mutum".
Gidansu ummi kuwa yau gaba ɗaya jikinta babu daɗi, ta gaji sosai da sosai, dan farida baƙi tayi, kan ummi sai ciwo yake yi, kamar za ta yi zazzaɓi da ƙyar ta lallaɓa ta yi aikace-aikace.
Sai da ta jera kwana biyu ba ta zuwa aiki, ta sanarwa manager ba ta da lafiya ne, haka islamiyya ma, kwana biyu zazzaɓi ya sakata a gaba da matsanancin ciwon kai da na ciki.
Dama Ummi ba ta saka ran wani ya bata kulawa ba, ita da noor kawai suke jinyar, noor ta yi wanke-wanke da abun da zata iya, a daddafe ummi take aikin gidan, farida ta lura da hakan, amma ko a jikinta dama da dr. Yana nan ne ya fuskanta zai kaita asibiti.
Raihan kuma ba sa iya waya, sai ta what's app, dan kuwa baya ƙasar gaba ɗaya, dan haka bai san halin da take ciki ba.
Tun ƙarfe shida ummi ta ga farida sun ɗauki mota da ita da kausar sun fice, Abdul kuwa aiki yaƙi samuwa, dan haka a wani kamfanin sarrafa taki, dr. Ya samar masa aiki, shima farida ta din ga kushewa, da nuna ɗanta ya fi ƙarfin wannan, amma Abdul ya ce yana so zai yi.
Ganin da noor tayi ummi babu lafiya sosai, ya sanya ta karya da buredi ta tafi tahfeez, ummi ta din ga burgima a É—akin ta, ga amai kuma cikin ta babu komai.
Wayarta tayi vibrating ya fi sau shida, da ƙyar ta ɗaga ta yi sallama.
"Baccin safe ki ke yau kenan, ko islamiyyar baki je ba? Na shigo gari jiya da daddare, abincinki nake son ci, kuma in ganki".
Cikin ƙarfin hali ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, bana jin daɗi amma zuwa yamma in sha Allah idan na gama zan kira ka".
Bai san lokacin da ya tashi tsaye ba ya ce "Ummi kamar fa haki ki ke yi, kina Asibiti ne?".
"A'a ina gida ne, zan warware in sha Allah" tayi maganar da ƙyar kanta na sarawa.
"Bani 20minutes gani nan" kan ta sake magana ya kaste kiran, ya fita da sauri.
Ummi ba ta sake sanin in da kanta yake ba ma, sai da ta ji ana buga ƙofar ɗakinta.
A hankali ta ce "Waye?".
"Mai gadi ne, kin yi baƙo ne, yana sallama"
Ummi ta ce "To" maimakon ta tashi, sai ta cigaba da bacci na rashin lafiya, a ƙalla maigadin ya zo sau uku, kan ta iya fitowa.
Hankalin raihan ba ƙaramin tashi yayi ba, da ya ga ummi, idanuwanta duk sun yi waje.
Tana ƙarasawa ta nemi wuri zata zauna a ƙasa, ya hanata hakan ya saka ta shiga motar.
Tun da ya ja motar yake faɗa a kan wasa da lafiyarta, oho ba ta ma san takamaiman zahiri ne ko mafarki ba saboda zafin zazzaɓi.
Ba a samo kan ummi ba, sai bayan ta sha ruwa roba biyu, sai dai a halin da take ciki, hankalinta yana gida, kar wani ya dawo a tarar ba ta yi girkin rana ba.
Likita ya din ga yi mata tambayoyi cikin harshen Ingilishi, dan ba ya jin hausa, da ƙyar take iya amsawa saboda ciwo, kuma hankalinta yayi gida.
Ya ce "Akwai ciki ne?" Sai da ummi ta kalli likitan, amma ta kasa magana.
Raihan ya ce "Babu".
"Ka tabattar? When last ta yi period?"
Maimakon raihan ya ce ba ta da aure, sai ya kalleta ya ce "Yana tambayar ki".
Likitan ya ce "Kai baka sani ba ne? Are you not couples? Na ji ka ce babu ciki"
Raihan ya wani gyara tsayuwa ya ce "Ai da yake bana gari, shiyasa ban riƙe ba, ummi ki gaya masa" ta sunkuyar da kai ta yi shiru, kamar ta buɗe ido ta ga ta ɓace, raihan ya gama da ita gaba ɗaya.
Raihan ya ce "She can't recall, but she's not pregnant"
Aka yi wa ummi teses, malaria da typhoid sun yi mata mummunan kamu.
Likita ya ce a bari ta kwana É—aya a asibitin, ummi ta ce ba ta san zance ba, ta sha faÉ—a a wurin raihan kan rashin kula da lafiyar ta, tare da yi mata kashedin saura ta je gidan a sakata aiki tayi. Ji yake tamkar ya samu wani kauwamammen wuri, ya ajiye ummi ya din ga kula da ita, kulawa ta musamman.
Ta so ace zata iya abun da raihan ya ce, taƙi yin aikin gidan, dan a galabaice take, amma da cin mutuncin da za ayi mata, gara aikin gidan.
Tayi ta yi wa Allah godiya, har suka dawo bayan azahar su farida ba su dawo ba, dama noor sai la'asar zata dawo.
Haka ta lallaɓa take aikin, lokaci-lokaci sai raihan ya kira ummi, ya tambaye ta ya take ji a jikinta, gaba ɗaya ya kasa nutsuwa hankalinsa ya ƙi kwanciya, dan babban fatansa ace a kwance take ko ruwa za ta sha, a ɗaukko a bata.