← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 134

Sashe 126

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi ma zaune har da ciki, kayan jikinta ya isa ya saye nasu gaba É—aya har da canji.

Sai gashi ya risuna yana gaida ummi.

Abdul ya ce "Malam Idris, na turo kuÉ—i aka ce ba ka gani ba"

Cikin kame-kame ya ce "Eh wallahi, ba su shigo ba"

Abdul ya ce "Kawo wayar ta ka in duba balance" ga waya a hannunsa babu damar yin ƙarya, ya miƙawa Abdul.

Yana duba messages, ya ga alerts, yadda Idris ya din ga cire kuÉ—i, ga tsohuwa a kwance a asibiti ciwo zai kashe ta!!!

Ayshercool
08081012143

Masu neman daga farko, dan Allah ku yi haƙuri ku duba a watpad, ko ku tambaya a groups whats app ɗina ne yayi expire, bani da shi a what's app 🙏

Masu son a tallata musu hajar su a what's app channel É—ina, should contact me, ina godiya sosai da jimirin bibiyata.

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

CUTARWA!

AYSHERCOOL

(BRIGHT PENS)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

48

Cikin tsananin takaici, Abdul yake kallon Idris da yake ta rarraba ido, kamar an kwashe wa karya Æ´aÆ´a.

"Amma ga alert É—in da banki suka yi maka, na kuÉ—in, kuma sannan ga wanda suka yo maka kana ta cirar kuÉ—i, ga sunana da komai da sunan bankina".

Nan Æ´an É—akin suka hau salati da salallami, iya ta É—ago idanunta da suka yi ja, saboda azabar ciwo da wahala, ta kalli Idris kawai ta sunkuyar da kai.

Wata ƙanwar iya ta fara masifa ta ce "Amma Idris an yi mutumin banza, kana kallon yadda matar nan take kwana tana wayyo ciwo, an rasa kuɗin yi mata abun da yakamata, saboda kai azzalumi ne ka cinye kuɗi ka ce ba a turo maka ba, yanzu duk soyayyar da iya take nuna maka wannan ne sakamakon abun da zaka yi mata?"

Yaya magaji ne yayi sallama, suka amsa masa, ya kalli yadda suka yi jugun-jugun ga dai iya a zaune, balle ya ce mutuwa ta yi suka jimami.

Suka gaisa da kowa, suka gaisa da ummi cikin girmamawa, sai dai bai ko kalli in da Idris yake ba, dan tuni ya daina yi masa magana ba ya shiga harkarsa.

"Wai lafiya na ga kowa ya yi shiru?"

Kawu Ilyasu ya ce "Ɗan uwanka ne ya cinye kuɗin da aka turo masa ayi wa Iya magani, yayi magana ma ya ƙi yayi shiru"

Hashim ya ɗan kwaɓe baki ko a jikinsa, dan gaba ɗaya yana danasanin kasancewarsa a tsatson iya.  Da ƙyar matarsa take tursasa shi ya zo dubata.

Ya ce "To Allah ya kyauta, ai da sauƙi tun da shi ya ci ba wani ba, balle a tsine masa na hannun daman ta ne"

Kawu sagir ha haÉ—e fuska ya ce "Wane irin iskanci ne wannan? Uwarmu na kwance ba lafiya kuna faÉ—ar abun da ku ka ga dama"

Ummi ta ce "A'a kawu, Allah ne ya kawo wa iya lokacin shan dauɗar gora, dan duk wanda zai sha barinta ne, ita da take yawan faɗa, kuma da sauƙi tun da shi ya ci ba wani ba, sai ta fi jin daɗin shanyewa"

Abdul ya kalli ummi yana girgiza mata kai, amma tayi burus da shi, dan lokaci yayi da yakamata ta amayar da damuwarta, ayi mata fyaÉ—e amma iya ta ce a rufa dauÉ—ar gora ciki ka sha ta. Duk wani abu in dai a kan Idris ne ko son zuciyarta, sai ta ce dauÉ—ar gora ciki ka sha ta. Ita ma gashi Allah ya kawo nata lokacin.

Kowa ya din ga tofa albarkacin bakinsa a kan Idris, yayi shiru ya kasa magana.

Wata maƙwabciyar su idris, mai suna ɗahara ta zo duba iya, sai dai matar kamar ba ta da saiti, kamar wadda ta taɓa hauka, saboda yadda take magana take sakinta yadda ta ga dama.

Cikin tsantsar ƙauyanci da rashin iya magana ta ce "Kai Innalillahi wa... me ye ma ƙarashen na manta, Iya haka ki ka koma? Wannan naɗai da aka yi miki a ka, kamar shugabar bokayen gagarawa? Rayuwa kenan, ai baban Nana, gidanka da na higa kan na taho, na ce wa Shindatu ta zo ta rakoni na duba gyatumar nan Iya, amma ta ce mini wallahi ba za ta zo duba tsohuwar banza da ba ƙaunarta take yi ba.
Nana ta ce Allah ya sa daga Asibitin nan ba za a maidota gida ba, na ce ke Shindu ki ji tsoron Allah, da gyatumar ki ce a ba kya ce haka ba". Ta yi maganar tana dariya, kamar abun da ta faÉ—a É—in ba wani abu bane a wurinta.

Ta sake cewa "To dai jin abun da suka faÉ—a, ya sa jikina yin sanyi na taho, to Allah dai ya bata lafiya, ni dai idan ta warke to, idan ba ta warke ba dai dan Allah ina bin ta jaka É—aya da muttala biyu kuÉ—in surfe na, gara a fara sauke mata nauyi tun tana raye".

Hashim ya saka hannu a aljihunsa, ya É—aukko É—ari biyar ya bata ya sallameta.

"Amma dai ka kyauta, wallahi gara ku bincika, Iya akwai shegen cin bashi, kuma ba ta biya, sai dai wani ka yi mata Allah ya isa ka ga hakan kuma ai bai yi ba"

Kawu Ilyasu ya ce "Ke dan Allah ki tafi ki bawa mutane wuri, mahaukaciya kawai"

Ta soke É—ari biyar É—in ta, ta fita tana dariya.

Babansu ya kalli Idris ya ce "Ka ga illar bujirewa iyaye ko? Matar da aka aura maka, ka wulaƙanta ta bayan ka yi abun kunya, ga wadda ka ke so ɗin abun da take faɗa a kan kakarka, mun gode amma in Allah ya yarda zaka gani, kuɗin nan da ka cinye sai sun hanaka kwanciyar hankali " aka din ga bashi haƙuri, a kan kar ya yi wa Idris baki.

Ummi ta ƙara tsorata da lamarin rayuwa, da yadda take tsoron Iya da Idris, abun ba a cewa komai, amma kallesu yanzu abun tausayi, da gari banza ne da iya tana nan tana ta zagin jikokinta tana tsine musu da sun motsa, ga tsinuwar nan tana ta tasiri a tsakanin su yanzu.

Ummi ta tashi ta fita tana amsa wayar raihan, a ƙalla ta kai mintuna arba'in, sai ga ta dawo da receipts a hannunta.

Ta miƙawa ƙanwar iya ta ce "Gasu nan, na biya duk abun da yakamata ayi mata, za su yi mata".

Ta waiwaya ta kalli Idris ta ce "Kai kuma, daga nan zan je in kai ƙararka wurin ƴan sanda, duk in da kuɗin nan suke ka dawo da su, dan ba wanda za a ƙara tursasawa shan wata dauɗar gora, da ake shanye ta wasu a ƙi shan ta wasu, shi ma auwwalun duk in da yake sai an nemo shi"

Kamar su shige cikin ummi, suka din ga zambaɗa mata godiya, Iya kuwa ta ƙure ummi da ido.

Ummi ta zauna a kusa da ita, ta ciro kuɗi, ta saka mata a cikin hannunta ta ce "Na san da magana a bakinki iya, amma ki sani ban yi miki wannan abun, dan na burgeki ba, ko ki so ni, bana fatan ko da ƙiftawar ido na yi abun da zai saka ki so ni ko na burgeki, tun da wanda na yi a baya ma babu riba.
Na yi miki ne kawai saboda zatin Allah, kuma saboda kin haifi mahafina, mutumin da ki ka azabtar kamar ba ke ki ka haife shi ba, saboda abun duniya, saboda waÉ—an nan" tayi maganar tana nunawa Iya kuÉ—in hannunta.

"Yanzu dai ba ya duniyar, mummunar ƴar sa da baki tabattar ko daga tsatsonki take ba, cikin hukuncin Allah ya rufa mata asiri. In sha Allah ba zan bari ki yi wulaƙantcciyar jinya ba, saboda babana bai wulaƙanta mini uwa ba, ke ma ba zan wulaƙanta ki ba, amma ki sani hakkin zuriyarki da ki ka raba kansu da kanki ne, ki ka gama tsine musu yake bibiyar ki.
Allah ya baki lafiya, duk abun da Allah ya yassare mini, zan din ga turawa yaya magaji"

Kamar munafukai haka duk suka duƙar da kai, ta gama maganganun ta, ta tashi ta ce wa su Abdul su tafi.

Idiris hankalinsa ya tashi da ya ji ta ce Æ´an sanda, dan ya tsorata da lamarin ummi, tun da ta saye gidansu na gado.

Abdul suna tafe a hanya, suna tattaunawa a kan yadda familynsu yake ƙara rushewa, saboda jahilci da rashin background mai kyau.

Can uganda dr. Ya cigba da karatunsa, idan baya nan yaran abokinsa suna shiga su taya mariya zama. Duniyarsa kawai yake ci da tsinke, yana samun duk abun da yake so daga gareta, ba tare da fargabar tashin hankali ko abun da za a buƙata daga gare shi ba.

Sai dai ƙasan zuciyarsa babu daɗi, yadda kausar da inteesar suka haɗe kai da babarsu, suka daina shiga sabgarsa, ko gaishe shi da suke yi a waya suka daina, daga noor sai Abdul sune suke ta tasa, sai kuma ummi.

Dan ƙarewa ma farida blocking ɗin sa ta yi a what's app.

Tun abun yana damunsa har ya watsar, ya cigaba da addu'a tare da rungumar amaryarsa hannu bibbiyu, ya ji hakam kamar samun salama ne daga rashin mutuncin farida.

Ga mariya da tsantsar ladabi, dan haryanzu wasu lokutan abubuwan ta irin na da take yin su.

Bayan tafiyar ummi, a ka yi wa Iya hoton ƙwaƙwalwa, cikin kanta lafiya ƙalau, sai dai tsananin damuwar abubuwan suke faruwa ya sanya jininta yin mummunan hawa.
Chapter 126 · 0% Book details