Sashe 11
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da suka koma gida, aka din ga yi mata faÉ—a, saboda ya zama dole a sanar da dangin su bashir maganar juna biyun nan.
Watanni huɗu da barin ummi a hannun iya, Ummi ta gane shayi ruwa ne, dan duk da ba girma ne da ita ba, amma tafi samun sauƙi da sassauci, a lokacin da mariya tana nan.
Gashi son makaranta ya shiga ranta sosai da sosai, idan ta yi wa iya laifi, sai iya ta hanata abinci, da ƙyar take iya zuwa makaranta, sai dai da ka ganta a cikin uniform ɗin nan, ka san babu kulawa, da babu wanda ya kai ummi tsafta a makarantar, amma wataran idan ka ganta, kamar ta shekara babu wanka, a wannan shekarun, ita take wanka da kanta, idan gari babu sanyi sosai tayi wanka da ruwan buta, idan da sanyi taƙi yi, dan wataran ruwan kawai take zubawa a jikinta.
Man shafawa sai iya ta ga dama zata bata ta shafa, shi ma ba iya shafawar tayi ba, iya ta daina bata, wai tana yi mata ɓarnar mai.
Wanki kuwa, sai idan na'ima za ta yi nata, sannan ya ta haÉ—a da na ummin, tayi ta goge mata, idan ba haka ba kuwa, sai dai tayi ta yawo cikin dauÉ—a.
A wata ukun nan, ummi ta koma kamar rainon mahaukaciya, wannan uban gashin babu mai kula mata da shi, ga cin zali da yara suka cigaba da yi mata, tun ummi na saka ran dawowar mama, har ta haƙura.
Saboda sabo, da sassafe idan ta tashi, sai ta ɗauki tsintsiya ta share sashin, ko da kuwa ba zai fita ba, saboda haka mama take yi, ta wanke bakinta da gawayi, ta jiƙa jikinta da ruwa buta ɗaya.
Idan ba makaranta ta tafi ba, mutanen gidan wannan ya ja ya aika, wancan ya ja ya aika, kamar baiwa, masu aiken nata, wani lokacin idan sun yi abinci su bata, domin kuwa bata ƙoshi da wanda iya take bata.
Duk ranar da tayi kuskuren yi wa iya fitsarin kwance kuwa, ko wani laifin, sai ta kira idris, ta bashi bulala, ta tuɓe ummi, ta ce ya zane mata ita.
Ga shi ya cigaba da kawo mata farmaki, gashi ta yi girman da ba zai yiwu ya É—auke ta ba, sai ya tsiro da salon aike, ya ce idan ta sayo ta kai masa É—akin su.
Yau idris ya kasa jurewa, ya aiketa sayen omo, ta dawo ta tsaya tana raɓe-raɓe, cikin ikon Allah sai ga naima, suka yi kiciɓis da ummi a soro ta ce "Ummi, tun ɗazu nake jiranki, ina kallon yadda malam babba ya zane ki, saboda makara, amma shi ne baki taho ba".
"Yaya idris ne ya aike ni sayen omo, ya ce na kai masa É—akin su".
"Ɗakin su kuma? Ina laifin ya ce ki kai wa babarsa, kuma ina sauran yaran gidan? To wallahi ko da wasa, kar ki kuskura wani a mazan gidan nan, ya aike ki ya ce ki kai masa ɗakinsa, ko wani wuri da mutane ko da kuwa zasu dake ki" ta waiwaya ta ga awwalu zai shiga sashin mazan ta karɓi omon ta ce "Kai auwwalu, ka kai wa idiris aiken da ya yi wa ummi, wuce muje ke kuma"
Suka tafi makaranta, ta saya wa ummi awara a hanya, da suka je ta zaunar da ita a makaranta ta bata ta ci.
Suna tafe a hanya naima na sake jaddadawa ummi, kar ta kuskura wani ya aiketa, ya ce ta kai masa É—akinsa a samarin gidan.
Ta raka ummi har cikin gidan, tana shirin tafiya, Idris ya shigo yana yi wa naima bala'i.
"Wacece ke a wurinta, da har zan aiketa ki hana ta kai mini aike?"
Naima ta ce "kamar yaya, makaranta zamu tafi mun makara"
"Dole tare zaku tafi makarantar? Har in aike ta ki hanata kawo mini saƙona?"
"Amma dai da alama baka da gaskiya, ba dai an kai maka aiken ba, ya zaka din ga aiken yarinya ka ce ta kai maka É—akin ka" nan da nan bala'i ya kaure abunka da gidan gandu, nan da nan aka taru, ya din ga kurarin zai yi mata dukan tsiya.
Iya ta hau naima da masifa, har da cewa kar ta sake shigowa, tun da sharri za ta yi wa idris.
Ita duk wannan abun ba shi ne damuwar ta ba, tausayin ummi take ji, ta kalli yadda ummin ta rakuɓe tana kuka.
Naima ta ce "Ba abun da zai sake shigo da ni in sha Allah, amma dai wallahi idris ka canza hali, mutumin banza kawai" iya ce ta hana shi, da cewa yayi sai ya zane naima.
Iya ta ce kowa ya watse, har ya nufi hanyar fita, ya dawo ya shaƙo ummi tare da luƙa mata wata irin ashar. Ƙara tayi tana kakari.
"Dan ubanki, daga yau idan na sake aikenki, ki ka biya wani wurin, ko kuma na sake ganinki da wannan yarinyar, sai na kashe ki" ya jefar da ita a wurin, ta riƙe wuya tana tari, wani irin yawu mai kauri na wahala, na zubowa daga bakinta, ta cire hijjabin makarantar ta tana gogewa, gashin kanta kuwa, kalba biyu ce tafi wata, ita ma naima ce tayi mata.
Mariya kuwa sallar magariba ake yi, kawai suka ga ta fito daga ɗaki, tana ƙoƙarin fita, mama wadda take matar babansu, ta riƙe ta, ta ce "Mariya lafiya ina zaki?"
"Mama kukan ummi nake ji, kamar tana ƙofar gida fa"
"Mariya ummi na jigawa, kina Maiduguri ta ina ki ka ji kukan nata?"
"Iya wai ba kya ji ne? Ni kukan ummi nake ji"
Mama ta ce "Iya kuma, nice fa mariya"
Mariya ta yi ƙuri da ido, tana kallon mama, sai yanzu ma ta dawo hayyacinta, gaba ɗaya ta kasa gane menene yake faruwa, bacci take ko idonta biyu, ita dai kamar kukan ummi kunnunwata suke jiye mata.
Ayshercool
08081012143
              *CUTARWA*
       BRIGHT PENS
      (FREE BATCH)
Shiru mariya ta yi, tana bin mama da kallo, jiki a sanyaye ta ce "Ki yi haƙuri, na zata gaske ne, magungunan da na sha ne, bacci ya ɗauke ni na ga ummi"
Mama ta ce "Mariya ki sassauta wa kanki a kan yarinyar nan, kar ki je ki haukace a banza fa"
Mariya ta amsa da "To"
"Ki din ga yi mata addu'a, Allah zai tsare miki ita" gyaÉ—a mata kai kawai ta yi, ta koma É—aki.
Ummi kuwa ta ci kuka kamar babu gobe, saboda zafin shaƙar da ta sha.
Iya ta ritsuta a É—aki tana tambayarta, ko wani abun take gayawa na'ima, ummi cikin kuka ta din ga girgiza mata kai, tana tsoron kar ta dake ta.
Har gari ya waye, tana jin wuyanta babu daÉ—i, ta yi wanka, ta sanya cukurkuÉ—aÉ—É—un uniform É—in ta, dan ma an yi sa'a a wanke suke, dama na'ima da yamma ta ce zata yi musu guga, aka yi uwar watsi.
Iya bata kulata ba, dan haka ta yi sharar tsakar gida, ta É—au kofinta, ta je sashin sa'adatu, da niyyar a bata kunu, sai dai ta tarar ta gama rabawa yaranta, suna sha zasu tafi makaranta.
Ta juyo da kofin a hannunta, tayi karo da magaji.
"Baki tafi makarantar ba ne?" Ta jinjina masa kai.
Ya kalli kofin hannunta, babu komai a ciki.
"Kunun ma baki samu ba? Iya bata baki ba?" Ta jinjina masa kai.
Ya karɓi kofin, ya shiga sashin su na maza, ya fito ya miƙa mata kunun cikin kofi.
Har ƙasa ta tsuguna ta karɓa, ta zauna a kan wani kututture, ta kafa kai ta din ga sha, saboda uwar yunwar da take ji.
Ta shanye ya karɓi kofin, ya bata naira ashirin, ta karɓa ta ce "An gode"
"Kiyi sauri ki tafi makaranta, kar su dake ki" ta ce "To"
Ta kamar hanya ta tafi, jin ta a ƙoshe da kunu ya sanya ta tafiya cikin nishaɗi.
Sai dai yau ma ta makara, a bakin gate discipline mistress ta fara zane ta, tare da ci mata mutunci saboda ƙazanta, jikinta bususu fuskarta duk busasshshen koko, ga sauran kwantsa a idonta.
Ta tafi aji tana kuka, saboda zafin bulala.
Ta je ta tarar ana yi musu darasi, ta buɗe jakarta da yanzu a baƙar leda take zuba su, duk sun zama shara da tarkace, fensirinta kuwa dama tsintar sa tayi, ya zama ɗan mitsitsi da ƙyar take iya riƙe shi ta yi rubutu.
Head master ya shigo ajin, duk suka tashi suka gaishe shi, yayi musu umarnin su zauna.
Ya dubi malamarsu ya ce "Malama, yara biyar zaki zaɓo mini masu ƙoƙari, zamu tafi da su gidan talabijin, za ayi wani shiri da su, a haska su"
Malamar ta ce "Ok sir, yanzu kuwa"
Ta tashi ta kira yara uku, ta huÉ—u ta kira sunan Salma Muhammad Bashir.
Wani irin farinciki ya kama ummi, saboda malamarsu ta zaɓeta a cikin wanda za a tafi da su gidan talabijin na jigawa, tana ta murna za ta ganta a talabijin, dan duk da rashin kulawar nan, ummi tana da matuƙar ƙoƙari, in dai aka yi darasi a gabanta, to ta ɗauke.
"Ke!ke tsaya" headmaster ya dakatar da ita a tsakiyar aji.
"Wannan kuma ina zata?"
Malama ta ce "Sir, yarinyar na da ƙoƙari fa, ita ce take first position"
"A hakan, wannan yarinyar da ya take karatun,? Ba ita ake kora ba ba ta biyan kuÉ—in PTA, da yaya take iya karatun"
Ta ce "A haka, ita take ta É—aya?"
"Kai canza wata dan Allah, haba wannan tayi muni da yawa, wannan ko an saka mata camera ai ba za a ganeta ba, baƙi ƙirin da ita haka, ji uniform ɗin ta fa, tubarkallah ni wannan tayi baƙi samo wata mai ɗan kyan gani, ke koma ki zauna ba za a tafi da ke ba, ji kayan jikinta kamar ƴar ci rani"
Tuntsirewa da dariya da yaran suka yi,hakan ya bawa hawayen idonta ƙwarin gwiwar zubowa, ta tafi lungun aji ta zauna, tana share hawayen.