← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 134

Sashe 10

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da iya ta ga ummi, sannan ta tuna ta ce da yamma a dawo da ita.

Iya ta ce "Ke daga ina?"

"A ƙofar ɗakinsu na ganta, wai mamanta take jira, a wannan sanyin, maimakon ta shigo nan ta jira ta".

Iya ta ce "Ka ji munafuka, an tsotso a nono, amma a gaban idonki ai uwar taki ta tafi barki ko?".

Hashim ya ce "Kamar yaya ina ta tafi?"

Iya ta ce "Mhmm, ai mariya daga ita har ƴan uwanta ba su da mutunci, zuwa suka yi za su tafi da ita, shi ne zasu haɗa da ummi, na ce ba zai yiwu ba, in rasa ɗa na sannan ita ma su tafi da ita ba, na ƙwace ta"

Yayi shiru yana kallon iya ya ce "Amma iya meyasa? Kin san bata shaƙu da kowa ba sai babarta, ga mahaifinta Allah ya karɓe shi".

"Ba ka san rayuwa ba magajin malam, mariya sam ba ta da tarbiyya, ba zan rasa ɗa na kuma ta tafi da ƴar sa ba, ta koya mata mugun hali. Tashi ki miƙo mini kwanon can, ki zo in zuba miki tuwo".

Ummi ta kawo kwano, iya ta zuba nata tuwon masara miyar karkashi, sai dai ummi ba ta son miyar karkashi. Ta jagwalgwala tuwon, ta cinye samansa, ta bar guntun cikin tsoro ta ce "Na ƙoshi".

Iya ta kalleta ta, ta kalli kwanon tuwon ta ce "Ni zan cinye miki sauran da ki ka bari?" Ummi ta girgiza kai.

"To maza cinye shi" duk ƙoƙarin da ummi tayi, ta kasa cin abincin nan.

Iya ta din ga zaginta, ta ce ta rufe ta ajiye, zata yi maganin wannan sangartar da aka yi mata.

Mariya Æ´an uwa na ta tausaya mata abun da ya faru, da alhinin rashin mijinta ga muguntar uwar miji, da kuma rabata da Æ´ar ta.
Dan sai da mahaifinsu ya so yayi faɗa, yayanta yayi masa bayanin abubuwan da suka faru, da ƙyar ya fahimta, duk da haka dan mariya tana cikin yaran da yake matuƙar so ne, tana da matuƙar haƙuri da biyayya.

Ya ce in dai ƴa ce, tun da sun ƙwace ta, su ƙarata suma ba zasu sake bibiyar a basu ba, idan sun ga dama su din ga kawota, idan ba su ga dama ba su je su ƙarata, dan babban abun da ya baƙanta masa rai, bai wuce yadda aka ce Iya tayi iƙirarin mariya ce ta kashe mata ɗa ba, karo na farko a kan mariya, aka goyi bayan mace ko dan ba ƙara ta kawo ba, zahiri suka gani, dan maryam ta labarta musu komai, har da yadda ake muzanta ummi, da cewar da iya tayi, wataƙila ɗan ta ma baya haihuwa, saboda su kaf danginsu babu kalar ƴar, daga baya kuma ta ce ita zata riƙe ta.

"Ai ban san mutanen kawai bane na basu ƴa ta, dattakun yaron da nutsuwarsa ce ta sanya haka, ina da yaƙinin zuriyata babu lalatacce, kar wanda ya kuma bi ta kan yarinyar, ku ƙyale su da ita, ke kuma idan kin gama takaba, Allah ya kawo miki miji nagari".

A ɓangaren mariya ba ta ji daɗin wannan goyon baya da aka yi mata ba, mussaman yadda ƴan uwa suka goya masa baya, a kan yanke alƙarsu da in da ummi take, ita a ganinta hakan ba masalaha ba ce, ita da ummi meye nasu a ciki.

Babu bakin magana, haka tayi shiru sai bin su da ido, ta ƙare ta shige uwar ɗaka, ta durƙushe a kan gwiwoyinta, ta din ga rusa kuka, ita ma meya rage mata na bashir da za ta kalla ta ji daɗi ban da ummin? Ta din ga kuka, zuciyarta na wani irin zafi, ji take kamar duniya babu wani abu da ya tage mata da zai sanyata farinciki, mahaifiyarsu ta rasu, yayyenta duk sun yi aure, sai ƙananan ƙannenta da matar babansu, dan ma mutuniyar kirki ce.

Washegari da asuba, iya ta idar da sallar asuba, ummi na ƙasa a duƙunƙune a cikin hijjabinta a ƙasa, ko zani ba a shimfiɗa mata ba, ba wanda ya kai ta tayi fitsrai, ta saba sai mariya ta kai ta tayi fitsari, kan ta kwanta, dan haka ta yi wa iya fitsarin kwance.

Kamar zata daki sa'anta, haka iya ta taƙarƙare ta ɗalawa ummi duka, a gigice ta tashi tana sosa wurin, saboda zafi.

"Dan ubanki fitsarin kwance ki ka yi mini saboda sangarta?" Dubawa ummi tayi ta ga fitsarin tayi, ta yi shiru ta kasa magana, sai hawaye.

"Au kuka ma ki ke yi mini, saboda sangarta da iskanci, zan yi maganinki, fita ki É—ebo ruwa a randa ki zo ki zuba"

Da sauran duhun asuba, dan haka ummi tsoro take ji, ta fito waje ta tsaya tana kuka.

"Ba zaki wuce ba, sai na zo" ta jiyo muryar iya. Cikin sauri ta je ta ɗebo ruwa, garin sauri ta koma ɗakin, ta faɗi sassanyar ruwan randar nan ya sheƙe mata a jiki.

A gigice ta yi wata irin ajiyar zuciya, tana kyarma. Ta tashi da guntun ruwan a moÉ—a, ta shiga ta zuba a wurin, kamar yadda iya tayi mata umarni, ta dawo É—akin ta tsaya.

Iya ta kalleta ta ce "Munafuka, shi ne ki ka zuba ruwan a jikinki, sai ki cire kayan ki saka wasu, ga tsummokaranki can".

Cikin rashin wayo, ta kwance kayan, ta saka uniform É—in ta, dan ta san ranar monday ce, ta tattara kayan fitsarin, ta haÉ—a su a cikin masu kyan ta É—aure, dan kuwa mama ta hanata zubar da kaya ko ina.

Ta juya ta kalli gabas tayi salla, ba tare da tayi alwala ba, dan da ruwan É—umi take alwala da mama tana nan, dan haka ta zata idan ba ruwan É—umi, ba sai ka yi alwala ba.

Gari yayi haske, ta je gaban murhu, ta saka hannunta ta dangwalo toka, ta cuccuÉ—a bakinta, ta kuskure ta koma É—akin iya, tana jiran iya ta bata abinci.

Aka kawo wa Iyan kunu mai zafi, amma ta kalli ummi, ya ce ta É—auki tuwon jiya ya cinye, dan ba za a zubar ba.

Miyar karkashin ce ba ta so, dan haka ta sake jagwalgwalawa, ta ajiye ta fito tsakar gida, tayi ta kallon ƙofar ɗakin su, ta ƙarasa ƙofar ɗakin tana ƙwanƙwasawa, wai ko mama zata buɗe, sai da ta gaji, kawai ta fita, ta kama hanyar makaranta, lokacin kusan tara da kwata, tana tafe iska na kaɗata, ga azabar sanyi jikinta babu rigar sanyi, sannan babu mai a jikinta, dan haka tayi busu-busu da ita.

"Ke daga ina?" Malamar da take ajin su ta tambaye ta.

"Gida" ta faɗa a taƙaice.

"Yanzu ne lokacin zuwa makaranta?"

Tuni hawaye ya cika wa ummi ido, saboda tana tsoron duka ta ce "Mama ce bata nan, ba ta dawo ba"

"To kuma gidanku babu wanda zai ce ki taho makaranta da wuri? Kalli jikinki fa ko mai baki shafa ba, kamar wadda zata aikatau ba makaranta ba" Æ´an ajin suka kwashe da dariya.

"Silent" malamar ta tsawatar tana kallon ƙafar ummi, da kamar an ciro ta daga haƙa rami, ummi kuwa gwanar kuka, ta kama ƙasan farin hijjabinta, tana goge hawaye.

"Wuce ki je ki zauna"

Ta nufi wurin zamanta, can wuri ɗaya, ta cigaba da sheshsheƙar kuka, tana jin muryar wani yaro, cikin murya ƙasa² yana cewa "Baƙar tukunya, yau an shafeta da toka"

Iya sam bata san makaranta ummi ta tafi ba, kawai sai nemanta ta yi ta rasa, hankalinta ya tashi, ta fito tana zagawa tana nemanta.

Ummi kuwa da ƙyar ta koma gida, saboda azabar yunwa, har wani jiri take yi, tana ta Addu'a Allah ya sa tana zuwa ga mama, sai dai kash, tsakar gidan nan fayau, ko shara bai gani ba, ta kalli wurin murhu da maman ke ɗora girki, shi ma babu komai a wurin, ta kalli ƙofar ɗakin su, ɗakin dai a rufe.

ÆŠakin iya ta shiga, ta nemi wuri ta kwanta, ta fara kuka tana share hawaye, tana kiran sunan mama da baba.

Bacci ya É—auke ta, sai dai hayaniyar iya ta tashe ta, "Dan ubanki ina ki ka je, ki ka tayar mini da hankali, nake ta yawon nemanki, lungu-lungu kamar akuya.

"Makaranta na je"

"Uwar makarantar, kin gaya mini zaki je?" Ummi ta girgiza kai.

"Kawai dan ki tayar mini da hankali, to ubanki ma bai É—aga mini hankali ba, balle ke" ummi dai tayi shiru ba ta ce komai ba.

Iya ta gama zaginta tsaf, sannan ta bata abincin rana, sai dai ba dan zai isheta ba, haka ta ci.

Da yamma yarinyar da take tafiya da ita makarantar allo, na'ima, ta zo tafiya da ita, Naima ƴar ɗakin mariya ce, dan tana son ummi sosai, ita take tafiya da ita makarantar allo, kuma ta ji labarin mariya ta tafi, iya ta ƙwace ummi. Ta tarar da ummi a zaune tayi shiru, idonta duk hawaye.

"Iya na zo tafiya da ummi makaranta"

"Gata nan, sai kun dawo" iya tayi maganar tana nuna ummi a wulaƙance.

Naima ta tambayi iya kayan ummi, ta gaya mata in da suke, ta ga jiƙaƙƙun kaya a ciki.

Ta ce "Ummi, na ji kayan ki a jiƙe?"

"Fitsarin kwance na yi ban sani ba"

"To ki daina haÉ—a su da kayanki masu kyau, idan mun dawo daga makaranta, zan wanke musu"

Ummi ta saka mata kuka ta ce "Yaushe mama zata dawo?"

"Ki yi haƙuri, nima ban sani ba, amma za ta dawo" ta shirya ummi ta sakata a gaba suka tafi makaranta, tausayin ummi ya kama ta.

Kwana ɗaya kawai, mariya ji take yi tamkar ta taka da ƙafa, ta koma gagarawa, ta ɗaukko ƴar ta, duk sallar da tayi, bata iya addu'ar komai, sai roƙon Allah ya kula mata da ummi, Allah ya dawo mata da umminta.

A kwana a tashi mariya ta gama takaba, sai da tun bai fi watanni biyu da daowarta gida ba, ta fuskanci tana É—auke da juna biyu, kuma ta ja bakinta ta yi shiru, ta din ga rashin lafiya, ba cin abinci, duk ta rame ta fita daga hayyacinta, maryam ta rakata asibiti, sai a lokacin da likita yake yi mata tambayoyi ta tabbatar musu da tana da ciki.
Chapter 10 · 0% Book details