← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 134

Sashe 54

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya sauka daga kan gadon sa, ya shiga banÉ—aki ya yi wanka yayi brush, ya sanya kayansa ya fita.

Sashin mami ya nufa, duk ba su tashi ba, ya duba kan dining an ajiye masa kayan breakfast da masu aiki suka girka.

Ya buɗe foodflask, ya tarar da doya ce da ƙwai, sai kayan tea, doyar ta ja mai sosai da sosai.
Yayi guntun tsaki, ya fice ya nufi sashin Hajiya, sai dai kai tsaye ɓangaren mahaifinsu ya wuce.

Yana zaune yana shan tea, gefen sa ƙaton tray ne, ɗauke da kayan marmari yana kallon labarai.

Ya É—aga kai ya kalli raihan ya ce "Dama kana gidan nan?"

Raihan ya ƙarasa kusa da shi ya risuna ya ce "Barka da safiya"

"Yauuwa barka babban mutum, ka tashi lafiya?"

Alhamdilillah, ya amsa yana zama a kusa da Alhajin.

Ya ce "Alhajin Allah kana sararawa, ka bar mu a nan ka je ka huta ka dawo, ka ƙara fresh sosai"

Sanin halin raihan, na zolaya ya sanya shi yin murmushi ya ce "Ina wani hutu Raihan? Ina can ma aiki nake yi, haryanzu ban huta ba, zuwa yanzu yakamata ace ku kuke kula da komai, amma sai dai nayi da kaina, yayyenka sun fi mayar da hankali a kan shashashanci".

Cikin kulawa raihan ya ce "Ka yi haƙuri, ka daina damun kanka, kai ka ce ƙuruciya ce take damunsu, za su daina".

"Zuwa yaushe kenan? Idan ƙuruciya ce kai meyasa ba ka yi?"

Raihan ya ce "Haka ne, amma dai kayi haƙuri ka kwantar da hankalinka, abun da su Yaya Salim suke yi, ka ɗauka jarabta ce daga Allah.
Kalli shekarunka sun ja, ba hawan jini, ba ciwon suga, ga mu Allah ya baka, ga tarin dukiya da al'umma suke amfana ga Hajiya ga mami dukkan mu naka ne, idan ka duba wannan ni'imomin sai ka ga abun da suke yi bakomai bane ba, dan Allah kar ka saka damuwa a ranka wani ciwon ya kama mana kai".

Kallon Raihan yake yi, cikin tsananin soyayya da kulawa, ya tsiyayo tea cup, ya bawa raihan sannan ya ce "Madalla da yaron kirki, nasiharka na ratsa mini zuciya, in sha Allah zan cigaba da yi musu Addu'a"

Raihan ya ce "Yauwwa father like no other, we are proud of you, ka cigaba da yi musu addu'a in sha Allah zai zama labari"

Alhaji Tahir ya ce "Mahaifiyarka na ganin kamar laifin Hajiya ne ya sanya su lalacewa, amma kamar hajiya na iya ƙoƙarin ta a kan tarbiyya".

"Haba Alhaji, kar ka É—orawa kowa laifi, Hajiya ba ta da sakaci ko kaÉ—an".

"Haka ne, ina son na roƙeka wata alfarma ne".

Raihan ya gyara zamansa ya ce "To Alhaji, Allah ya bani ikon yi".

Ya ce "Yauwwa, lissafin da muke yi na shekara shekara da manager, da kai nake so ku yi, a fitar da zakka, a fitar da wanda za a biyawa umara, harajinmu na nan gida da sauran ƙasashe, da duk wasu gyare-gyare da zamu yi, idan ku ka gama sai ka kawo mini na duba"

Raihan ya É—an yi shiru yana nazari, "Ya dai na ji ka yi shiru?"

Raihan ya É—ago ya ce "Babu damuwa in sha Allah za ayi, zan je na same shi".

Alhaji Tahir yayi murmushi ya ce Yauwwa "Babban mutum, ka ga atleast na sake na huta sosai da sosai"

Raihan yayi murmushi yana cigaba da zuƙar shayi, nauyi ne mai girman gaske Alhajin ya haɗa shi da shi, dan aiki ne ba ƙarami ba.

Ya shanye shayin, ya miƙe tsaye ya ce "Bari na ƙarasa wurin Hajiya mu gaisa"

"To shikenan babu laifi"

A sanyaye Raihan ya tashi ya nufi sashin hajiya, ba zai iya cewa mahaifinsu a'a ba ne ba, amma wannan aikin kamar yayi masa yawa, ba zai iya jajircewa ya yi shi, kamar yadda shi Alhajin zai yi ba.

"Babban mutum ya dai, na ga kana tafiya a hankali, ko yunwa ka ke ji ne?"

Ya zauna yana faÉ—in "Eh, ina É—an jin yunwa ma, me ku ka yi?".

"Ka san halinsu, kowa dafe-dafensa yayi, ni kuma tuwo na saka a É—umama mini na sha da tea"

"To ni ma zan ci tuwon"

Ta ce "To bari a kawo, har da man shanu kuwa da yajin daddawa, mai É—an karen daÉ—i"

Yayi murmushi ya ce "Hajiya kenan, ina su Yaya Sagir?"

Ta É—an rausayar da kai ta ce "Ba su tashi ba".

Ya jinjina kai sannan ya ce "Yauwwa Hajiya, kin tuna yarinyar nan ummi? Ƙawar maryam?"

Ta ce "Eh, ya aka yi?".

"Yauwwa Alhamdilillah, dan Allah me ki ka sani a kanta?"

Hajiya ta É—an yi shiru tana nazarin sa, sannan ta ce "Meyafaru da ita? Me ka ke son sani a kanta?".

"Ba wani abu bane ba, mami ta fara faÉ—a mini abubuwa a kan ta, so ina son sanin if their is way, we can help her, like she's not socially ok"

"To ai kaga ƙawar maryam ce, ni kuma ba wani son shiga harkata suke yi ba, amma dai ina ganinsu tare da maryam, yarinya ce mai matuƙar haƙuri da biyayya, kamar babanta ne ko babarta ce ɗaya daga ciki ya rasu, yayan babanta yake riƙonta, matarsa take maltreating ɗin ta, gaskiya i don't know much about her. Na so ace a cikin yaran nan akwai nutsatstse, ai da na haɗa su aure, tarbiyyar ta na burge ni sosai da sosai"

"Kin san meya ja hankalina, har na tambayeki?"

"A'a sai ka faÉ—a".

"Yadda maryam take yawan bani labarinta, da irin abubuwan da suka din ga yi mata na wulaƙanci suna makaranta, gidansu an yi maltreating ɗin ta, makaranta yara sun yi maltreating ɗin ta, wai wasu lokutan har da malamai, abun bai yi mini daɗi ba wallahi Hajiya"

Hajiya ta ce "Shiyasa nake yinka babban mutum, akwai hangen nesa da zurfafa tunani".

Cikin damuwa ya ce "Hajiya, kowace halitta da Allah yayi, tana da muhimmanci da kuma amfani, sosai nake jin zafi idan na tuna abun da maryam ke faɗa a kan ta, gaba ɗaya yanayin ta kamar a tsorace take da mutane ma, kuma ni banga muninta ba, baƙa ce kawai, meye abun aibata mutum a kan abun da baka da ikon yin sa?"

"Babu kam"

"Amma Hajiya kina ganin zan iya taimaka mata?"

"Me zai hana? Idan har da ɓangaren da zaka iya supporting ɗin ta, go ahead nima zan yi farinciki da hakan"

Raihan ya sake gyara zaman sa ya ce "Wallahi na so maganarki ta farko ta tabbata, ina ma akwai nutsatstse a cikin su yaya salim, da É—aya daga cikin su, ko shi ko yaya sagir da wani ya aureta"

Cikin damuwa ta ce "To ya zan yi, sun ƙi karatu, sun ƙi kasuwa sai shirme, sai addu'a kawai"

"Kar ki damu Hajiyarmu, lokaci ne, zasu daina ne in sha Allah, ayi tayi mana Addu'a"

Hajiya ta É—ora hannunta kan na Raihan ta ce "Addu'a kullum cikin yi muku ita ake ai, ubangiji Allah ya tsare mana ku"

Ya amsa da Amin.

Sai da ya ci ya cika cikinsa, sannan ya tashi ya fita.

Har ummi ta koma gida, Raihan bai sake nemanta ba, tayi ta duba wayar amma bai kira ba.

Dr. Yan gari, yana ta ƙoƙari a kan kausar ta samu admission ita ma, domin kuwa a wannan karon, Farida ta ce ba zata sake aurar da ƴa ba, sai ta fara makaranta, saboda kar a sake kwata irin yadda aka yi a kan inteesar.

Suna falo suna kallo, dr. Ya ce lallai ummi ta fito falon ita ma, dan baya son duk suna tare a falo, amma ta din ga ware kanta ita kaÉ—ai a É—aki.

Ummi dai ta zo gefen kujeru ta zauna a ƙasa, tana kallon, wanda a son ranta tafi son zaman kaɗaicin a ɗakinta.

Noor ta hana su yin kallon, sai tsalle take a tsakar falon, tana karanta ayar Allahu nooro samawati wal ardi.

Abdul ya ce "Noor, dan girman Allah ki zauna wuri É—aya ki yi karatun nan a nutse".

Sai ta koma hawa kan kujera tana dirowa.

"Ke dan ubanki ki nutsu" Kausar tayi mata tsawa.

Noor ta ce "Babanmu É—aya"

Dr. Ya ce "Lafiya ce wannan tsalle-tsallen da take yi.

Farida ta ce "Duk ta bi ta ishi mutane da karaÉ—in tsiya".

Noor ta koma kusa da dr. Ta zauna ta ce "Dr."

Ya ce "Na'am shalelena, yau kuma a dr. Na nake"

"Ka san me? Wata a ajinmu, babansu ya auro kishiya, yanzu mamanta biyu kenan".

Yayi dariya ya ce "Masha Allah, to Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya".

Ta gyara zama ta ce "To Abba ni bani da wata maman sai maama, ita kuma ba ta so na"

"Tana sonki mana".

"Abba dan Allah muma ka auro mana kishiya, nima mamana ta zama guda biyu"

Ashar ɗin da farida ta yi mata sai da duk suka razana, ta zaburo zata make noor, amma noor ta tashi da gudu, tana murguɗa kwankwasonta tana dariya, ta tsaya daga can ƙarshen falon ta ce "Wallahi Maama idan ki ka kuma dukana, sai na ce Allah ya sa Abba ya auro kishiya"

Farida ta dafe kai ta ce "Na shiga uku da wannan yarinyar, anya nikaɗai aka yi wa tiyata a ɗakin nan ba ayi mini musanye ba, anya yarinyar nan tawa ce? Gaba ɗaya ƴa ba ta da mutunci sai iskanci da rashin mutunci. Kodayake ba laifinta bane ba, tun da aka saka mata sunan bare da babu dangin iya babu na baba, kuma ana koya mata yadda zata wulaƙanta ni".

Tsam ummi ta miƙe, dan ta san ƙarshe faɗan kanta zai dawo.

Ta tarar da noor a É—akinta, ta haye wa ummi kan katifa, ta yaye mata zanin da ta shimfiÉ—a.

"Mama" ta kirata kamar yadda take kiranta.

Noor ta É—ago ta kalleta.

"Meyasa ba kya jin magana ne?"

"Me nayi?" Tayi maganar cikin tura baki.

"Ban hanaki yi wa maama rashin kunya ba?"

Noor ta ce "Ba kya nan jiya ta dakeni, tayi ta zagina".

Ummi ta ce "To ai ke É—in ce ba kya ji mama"

"Ina ji mana, ai in dai ta dake ni, cewa zan din ga yi Allah ya sa Abba ya auro kishiya"
Chapter 54 · 0% Book details