← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 134

Sashe 51

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita dai tayi shiru ba ta ce masa komai ba.

Ya bata wayarsa ya ce "Saka mini lambar ki, sai na turawa maryam, ku dinga gaisawa, zumunci abu ne mai kyau".

Wayar ta sa zuƙeƙiya mai kyan gaske, ta saka masa lambar ta miƙa masa.

Ya ce "Masha Allah, to nima za a din ga zumuncin da ni? Tun da ƙaninki ne ni?"

Ummi ta yi murmushi ta ce "To"

"To yaya ummi na gode sosai, sunana Muhammad Raihan"

Ta ce "Ai na sani"

"Ai tuna miki na sake yi, ranar da muka haÉ—u mun kusa yin faÉ—a, ashe kin sanni nine ban gane ki ba"

Tayi murmushi tana sake gyara zaman facemask É—in ta.

"Ki rage saka niƙabin nan da facemask, idan ba haka tayaya mutum zai gane ki, you are lucky ina da saurin gane mutane ma, da mask ɗin na gane ki"

Ummi dai ba baki, dan dama can ba mai hayaniya ba ce, sai murmushi da take yi.

A bakin titi ta ce masa zata sauka.

Ganin ya takura mata, ya sanya ya ƙyaleta, ta buɗe motar ta waiwayo ta kalle shi ta ce "Na gode sosai"

"Nima na gode ki gaida gida" yana kallonta cikin dabara ta ajiye masa ruwa da lemon da ya bata ta fice.

Raihan ya taimaketa da ya É—aukkota, ba dan haka ba, sai ta ci uwa tafiya, kafin ta hau mota, dan kuÉ—in motarta ba yawa a jakar.

Har ta shiga gida, jikinta ƙamshin turaren raihan yake yi, kasancewar gaba ɗaya motar ma ƙamshin turaren take yi.

Yana zaune a motar ya kira lambar ummi, tana sauri zata shiga gida, wayarta ta fara ringing, ta ciro wayar ta É—aga tana hello.

Kashewa yayi jin muryarta ce, yayi saving number da brown eyes.

Ummi ta shiga gida tana fatan Allah ya sa ba wanda ya ganta ta sauka daga motar raihan.

Bayan sallar isha'i maryam ta kira ummi a waya, tare da yi mata ciwon bakin bata nemanta.

Sosai suka fara hira da ummi, sai dai hirar ta daina yi wa ummi daɗi, lokacin da maryam ta fara yi mata zancen ita yaushe za ta yi aure? Ummi ta ƙarƙare hirar suka yi sallama.

***
GAGARAWA

Masifa da bala'i a gidan idris, kamar karnuka tun maƙwabta na shiga cikin lamarin, ana ƙoƙarin sasant al'amura, abu ya gagar a gaban yaran suke faɗa, suyi ta zage-zage da ashar kamar maguzawa.
Yarinyar sa ga fari kuwa, tun da aka je da ita family house, aka yi mata gori, Hindu ta wanke ƙafa taje har gidan tayi musu tijara da rashin mutunci.
Babu wanda hindu take saurarawa a dangin Idris, tun daga kan Iya har sauran mutanen gidan.
Dan haka Idris ya fara tunanin ƙara wani auren, ko ya samu sassaka daga masifa da bala'in hindu, gashi kamar tayi masa asiri, duk tijara da bala'in da zata yi masa ba zai iya sakinta ba.

Hashim kuwa ya kasa samun nutsuwar samun matar aure, saboda gaba É—aya hankalinsa a kan ummi yake, sai dai iya tayi masa kandagarki, dan ta riga ta ce ba ta lamunce ba, dan haka ya san ko giyar wake ya sha, tun da iya ta furta ba ta so, babu mai goya masa baya.

***
Ƙarfe kusan goma na dare, Ummi ta yi wanka tana shirin kwanciya bacci, dan washegari asabar ce, za ta je islamiyya da safe ta koyar da yara, dan haka da wuri take son kwanciya dan ta kammala aikinta da wuri ta tafi da safe.
Kallon baƙuwar lambar take yi, sannan ta ɗaga tayi sallama.

Ba ta ɗau muryarsa ba da farko, dan haka gabanta ya faɗi, ko bisa tsautsayin wrong number, wani namiji bai taɓa kiranta ba.

Sai da ya ce "Yaya ummi" sannan ta É—au muryar.

Ta ce "Au babban mutum, yanzu na É—au muryarka ai".

"Ke, Alhajinmu ne fa kawai yake faÉ—ar sunan da ki ka faÉ—a, sai Hajiya, waye ya gaya miki wannan sunan?".

Ummi ta yi murmushi ta ce "A bakin maryam na ji, kuma ai sunanka babbane, ba a faÉ—arsa anyhow"

"To sai ki ce Raihan ai"

"To shikenan, ya mami da su Hajiya?".

"Suna lafiya, ta kira ki kuwa?"

"Eh mun yi waya da ita, ka kyauta ai".

Ya ce "To Allah ya haÉ—amu a ladan baki É—aya"

Ta amsa da "Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum"

"Ya aikin?"

"Aiki Alhamdilillah"

Ya ce "Masha Allah, kiranki nayi na kwashi gaisuwa kawai, tun da mun yarda mu yi zumunci, tun da maryam ba ta nan, sai mu mu din ga yin zumuncin. Dama bani da abokai na yi ƙawa, ƙawar yayata ta zama ƙawata".

Ummi ta girgiza kai ta ce "Mace da namiji ba sa ƙawance ai, ƙanina ne kai".

Yana daga kwance ya tashi zaune ya ce "To shikenan, muje a haka yaya ummi"

Tayi murmushi ta ce "Sai da safe".

Ya ce "Allah ya tashemu lafiya yaya, sweet dreams".

Ummi ta ajiye wayar tana cigaba da murmushi. Ta bi wayar da kallo, ƙanne suna da daɗi, ta so ta rungumi su intee kamar ƙanneta, amma suka nuna mata ba haka ba, shima Abdul alaƙarsu farida ta saka musu ido, da ta gansu tare sai zagi da cin mutunci.

Ɓangaren Raihan ma, wayarsa ya bi da kallo, yana kallon lambar ummi da ya sakawa brown eyes, sanyin halinta ya burgeshi, abun da mami ta gaya masa game da ita, ya sanya masa tausayinta, dan haka yake jin ko na ƙanƙanin lokaci ne, zai shiga rayuwarta ya fahimci ta ina zai taimaketa, kuma zai yi mata addu'ar samun miji nagari mai ƙaunarta.

A rayuwarsa ummi ce mace ta farko da ya ji yana son shiga rayuwarta, idan ba iyayensa ba sai Æ´an uwansa mata, ba ruwansa da shiga harkar kowacce yarinya, duk da suna yi masa shishshigi, saboda Raihan kyakykyawa ne kamar maryam, kamar sa É—aya da mahaifinsu.

Washegari tana makarantar islamiyya, tana fama da ɗalibai, kusan ƙarfe goma da rabi, ta sake ganin kiran Raihan.

"Ina kwana yaya"

"Lafiya ƙalau, ka tashi lafiya?"

"Lafiya ƙalau, ya nake jin hayaniya kina ina ne?".

"Na je islamiyya, ne ina tare da É—alibai" .

Ya ce "Ok, ashe sayyada ce, mu yi waya idan kun tashi, dama kira na yi idan kina lafiya"

Ta ce "To godiya nake, Allah yayi albarka"

Yayi murmushi ya ce "Dan Allah ki saki muryarki ki daina iyayi"

Dariya ce ta kamata, ta ce "Ka cuci iyayi kuwa"

"Am serious, na yi recording wayar nan, zan tura miki ta what's app ki ji yadda ki ke magana, sai anjima take care" yayi maganar a hankali.

Ayshercool
08081012143
    *CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P23

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books É—ina, da free pages duk akwai a kan watpad account É—ina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

23

Murmushi ummi ta yi ta sauke wayar, tana sake gazgata maryam da take yawan faÉ—ar Raihan rigiamamme ne.

A ɓangaren sa shima ajiye wayar yayi yana murmushi. 

Ya sauka daga kan gadon sa, ya shiga banÉ—aki ya yi wanka yayi brush, ya sanya kayansa ya fita.

Sashin mami ya nufa, duk ba su tashi ba, ya duba kan dining an ajiye masa kayan breakfast da masu aiki suka girka.

Ya buɗe foodflask, ya tarar da doya ce da ƙwai, sai kayan tea, doyar ta ja mai sosai da sosai.
Yayi guntun tsaki, ya fice ya nufi sashin Hajiya, sai dai kai tsaye ɓangaren mahaifinsu ya wuce.

Yana zaune yana shan tea, gefen sa ƙaton tray ne, ɗauke da kayan marmari yana kallon labarai.

Ya É—aga kai ya kalli raihan ya ce "Dama kana gidan nan?"

Raihan ya ƙarasa kusa da shi ya risuna ya ce "Barka da safiya"

"Yauuwa barka babban mutum, ka tashi lafiya?"

Alhamdilillah, ya amsa yana zama a kusa da Alhajin.

Ya ce "Alhajin Allah kana sararawa, ka bar mu a nan ka je ka huta ka dawo, ka ƙara fresh sosai"

Sanin halin raihan, na zolaya ya sanya shi yin murmushi ya ce "Ina wani hutu Raihan? Ina can ma aiki nake yi, haryanzu ban huta ba, zuwa yanzu yakamata ace ku kuke kula da komai, amma sai dai nayi da kaina, yayyenka sun fi mayar da hankali a kan shashashanci".

Cikin kulawa raihan ya ce "Ka yi haƙuri, ka daina damun kanka, kai ka ce ƙuruciya ce take damunsu, za su daina".

"Zuwa yaushe kenan? Idan ƙuruciya ce kai meyasa ba ka yi?"
Chapter 51 · 0% Book details