← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 134

Sashe 46

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kalmar gorilla! Ta daki ƙirjin ummi, hakan ya haifar mata da wata irin mutuwar jiki, munin nata har ya kai a kira ta da gorilla?

Zuciyarta ta din ga bugawa da sauri-sauri, tamkar zata kifa ƙasa ta shiga ajinsu tana wani irin kuka, wane irin abu ne wannan?.

Ishaq ya kalli abokinsa ya ce "Kai Nura kamar fa ta ji ka"

"Ahha haba dai?"

"Tana kusa fa ka faÉ—a"

Nura yayi tsaki ya ce "To sai me?".

Ishaq ya ce "A'a nura, zuciya ba ta da ƙashi, cin fuska ba shi da daɗi, tuntuni na gaya maka ka daina kamanta ta da dabba, yarinyar so silent ba ruwanta da kowa bai kamata ba wallahi"

"Ka ga kar ka isheni, jokes ne"

"Ai gaskiya ce, ba wani jokes wallahi, ko kusa yarinyar nan ba ta yi kama da abun da ka ke misalta ta ba, hidden beauty ne da ita, baƙinta da rashin gayu ke hana kyanta fitowa, amma ba ta yi kama da abun da ka ke faɗa ba".

Suka tafi aji, yana ta yi masa faɗa, suna shiga aji kuwa, kan ummi a ƙasa da alama kuka take yi.

Gaba É—aya jikin Ishaq yayi sanyi ya ce "Ka gani ko? Kuka take wallahi".

Shigowar malamin ya sa kowa ya nemi wuri ya zauna, ya fara gabatar da abun da ya kawo shi.

Sai dai yana lectures yana ganin yadda ummi ke sharɓar hawaye.

"Ke are you ok? Meyake damunki ne?"

Ta kasa magana ta tashi tsaye tsam, ta É—auki jakarta cikin kuka ta ce "Sir dan Allah ka bani iznin tafiya gida"

Duk da zafin malamin da rashin son wargi, amma kukan da ummi take yi, yana nuna akwai tsantsar damuwa a zuciyarta.

Kamar yadda ake son malami ya kasance cikin kulawa ya ce "Babu damuwa, amma zaki iya tafiya? Ko ki na da ƙawa ta raka ki gidan?" Ta girgiza masa kai ta ce "Zan iya tafiya"

"Kin tabbata?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

Ya ce "To shikenan, ki tafi a hankali ki yi ta Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ta jinjina masa kai ta risuna masa ta yi masa godiya sannan ta fice ta tafi gida.

Ta daÉ—e ba ta yi kuka mai yawan na yau ba, tun noor tana rarrashinta, har ita ma ta fara kukan.

Ta rarrashi noor, ta aiketa kitchen, ta mayar da ƙofar ɗakin ta rufe, ranar ba irin bugun da farida ba ta yi ba, a kan ummi ta buɗe ta zo ta yi mata aiki, amma mursisi taƙi buɗewa abun za ba ta taɓa yi ba kenan. Ta san ƙarshen abun dai, zagi ne za ta sha shi da cin mutunci a wurin farida.

Tayi shiru tana tunani kala-kala a zuciyarta "Ko zan ji daÉ—i a rayuwata? Ko zan huta, ko kuma a haka zan cigaba da rayuwa, sanin gaibu sai Allah.
Idan ina da rabon hutawa da jin daɗi, Allah ka kawo mini su da wuri, ba dan na gajiya da karɓar jarrabawar ka ba, ni'imominka gareni sun ninka jarrabawar, Allah ka shiga lamarina" tayi maganar a bayyane cikin kuka

Sai da ta jera kwana biyu ba ta je makarantar nan ba, ranar da ta je, malamin da a period É—in sa ta tafi gida, ya kirata ofishin HOD, suka din ga tambayar ta meyake damunta, dan malamai da yawa sun fuskanci kamar tana da social fear.

Kukan da ta kasa riƙewa a gaban su, ya tabbattar musu da tana da damuwa sosai da sosai.

Duk yadda suka matsa ta, ba ta gaya musu abubuwan da suke damunta ba, duk da tana da abubuwa da dama a ranta, da take son tattauna shi da wani, amma ta kasa samun wanda zuciyarta za ta nutsu da shi, su tattauna sosai, ko ba ayi mata maganin damuwar ba, atleast ta furta abun da yake damunta.

Suka nemi zasu zauna da mahaifinta, amma ta din ga yi musu magiya, a kan kar su yi hakan, dan a ganinta idan aka yi hakan tamkar ƙure babanta kawu yahaya ne, domin kuwa yana iya ƙoƙarin sa a kanta.

Nasiha suka din ga yi wa ummi, tare da bata ƙwarin gwiwa, a kan muhimmancin mayar da hankali a kan karatunta, da shanye ƙalubale, wanda ba ƙaramin jin daɗin nasihar ta su yi ba.

A ƙarshe HOD ya cigaba da tsokanar ta, da cewar ba ta da visa baƙar balarabiya ce ta shigo musu ƙasa.

ÆŠaya malamin yake ce mata, tun da Æ´ar jarida ce ita, kuma an san su da neman suna, idan ta mutu yana son idonta zai saya da tsada, ta shiga kundin tarihi.

HOD ya ce "Allah ya kiyaye, wannan idon na larabawa ne a Nigeria Masha Allah, in dai wannan tarihin ne mun yafe, ko Salma"
Ummi ta sunkuyar da kai tana murmushi.

Ummi ta ji daÉ—in mutuntawar da malaman da take wa kallon iyaye suka yi mata, da nuna damuwarta kamar ta su, nasihohin su, sun shige ta sosai da sosai.

HOD yaje ajin su ummi, ya yi musu jirwaye mai kamar wanka, ta hanyar gugar zana a kan wulaƙanta ɗan Adam, da muhimmancin girmama ɗan Adam.

Ta samu sassauci daga jin wani abu mai nauyi da yake damun zuciyar ta.

Sai dai ta kasa manta kalmar gorilla, noor da Abdul suna falo suna kallon film É—in king Kong, ummi har ta wuce ta dawo, ta ce "Yaya Abdul"

Ya É—aga kai ya ce "Na'am yaya ummi"

"Dan Allah wai ina kama da gorilla?"

Wani irin banzan kallo yayi mata ya ce "Wace irin magana ce wannan?"

Cikin son ɓoye abun da ya faru ta ce "Amm, dama kawai na tambaya ne, dan na ji ana cewa ni mummuna ce"

"Kuma sai ki haɗa kanki da biri, haba ummi, ke tsakani da Allah idan aka ce ke mummuna ce sai ki yarda? Ki ƙarewa kanki kallo, a kan me zaki yadda ke mummuna ce? A halittar Allah babu mummuna, duk wanda ya ce miki mummuna ki ce ubansa ya sassaƙo kamar ki"

Noor ta ce "Maama kenan za a gayawa, itama tana cewa yaya ummi mummuna, kuma fa yaya ummi gashinta har nan, tafi fa maama gashi"

"Tashi ki bar nan wurin kan na tatsileki, baba suda" yayi maganar yana kallon noor.

Ummi kuma ta ce "To shikenan yaya Abdul, na gode sosai "

"Dan Allah kar ki kuma faÉ—ar haka "

"Ba zan sake ba in sha Allah" sai dai a ranta tana jin har ta mutu ba zata manta da Nura ba, ya shiga cikin jerin mutanen da take yi wa wani irin kallo a zuciyarta.

Ƴan ajinsu ummi ba su tashi mamaki ba, sai da result ya fito na first semester, ummi ta ja magana, GPA ɗin ta 4, wanda kaf ajin babu mai wannan grade ɗin.

Kasancewar ɗabi'a ce ta ɗan adam, mu'amala domin cikar muradi, ya sanya suka fara lallaɓowa, domin shiga jikin ummi, amma fafur taƙi ta cigaba da rayuwar kaɗaici.

***

Gidan Idris kuwa, kamar masu zaman bariki, saboda faɗa zagi yana zagin hindu tana ramawa, tana kiran sunan uwarsa da ubansa tana zagi, idan yayi gangancin dukanta kuwa, ta dinga wawurar abubuwa tana kwaɗa masa kenan, dambe da zage-zage har ƙofar gida kamar dabbobi, maƙwabta suna raba su.
Sulhu kuwa an yi musu shi babu adadi, amma abu ya ci tura.
Sam ba ta ganinsa da mutunci, shi ma kuma haka, taje gidansu ta gaida Iyayensa kuwa ba ta wannan, saboda ta ce ba zata je gaida tsohuwar banza ba, ta ji labarin zaman da yayi da matarsa Æ´ar uwassa, ita ba zata lamunci cin zarafi ba.

Ya gaji da iskancinta, ya kamata yayi mata tulus da duka, ashe tana da juna biyu, ta yanke jiki ta faɗi, ƙarshe dai sai da iyayenta suka rufe Idris a police station, aka wulaƙanta shi aka kai ruwa rana kafin a sake shi, banda kuɗin magani da aka saka ya biya.

Kwana biyu da dawowar sa daga hannun ƴan sanda, ya je ya samu hashim a kan ya bashi shawara, so yake a lallaɓa kawu yahaya da ummi, a dawo da auren su.

Hashim ya ce "Haba Idris, lokacin da na din ga ankarar da kai ai kasa ganewa kayi, ummi tafi ƙarfin ka yanzu, wace irin azaba ce ba ka yi mata ba, tun tana ƙaramar yarinya. Yanzu ta sauke Alqur'ani har sau biyu, ta shiga jami'a tana karatu, ka ce ta dawo, to tayi maka me? Kai da ko kwalin sakandare baka da shi".

Idris ya waro ido ya ce "Ummin ce a jami'a, kai waye ya gaya maka?".

Hashim ya ce "Muna waya da ita, bautar ƙasa nake son na gama, idan Allah ya sa na samu aiki, zan nemi auren ummi".

Idiris yayi masa wani mugun kallo ya ce "Amma dai ka ci kai, matar da na saki zaka aura? Bazawara ce fa kai kuma baka taɓa aure ba. Haryanzu bana son ummi, ban taɓa jin ƙaunarta a raina ba, amma ina da muradi a kanta, idan har ba ta dawo mini ba, idan ina raye baka isa ka aureta ba".

Hashim ya yi murmushi ya ce "Zamu gani ai" Idris ya tashi fuuuu ya tafi.

Idris yayi shiru yana tunani, tun da mahaifinsu ya takura masa da maganar aure, ya gaya masa ga ƙudurinsa, Iya ta ce bai isa ba, ba zai auri bazawar da ƙaninsa ya saki ba, kuma ta riga ta cire ummi daga jikokinta tun da ta ƙi yarda a rufawa Idiris asiri!.

Babansa kuma ya ce Idan ya sake ɗaga maganar nan, zai yi masa abun da bai taɓa tsammani ba.

Duk son ummi da islamiyya, haka ta haƙura, saboda yanayin makaranta, ta samu wata makarantar, a nan unguwarsu, take zuwa asabar da lahadi ɗaukar karatu.

Sai dai ganin ummi tana da ilimin addini dai-dai gwargwado, idan aka yi mata ƙarin nata karatun, sai a haɗata da aji tayi musu ƙarin Alqur'ani da wasu litatafan.

Duk da ayyuka sun ƙara yi mata yawa, hakan yayi mata, saboda tana zama busy sosai, tana hana zuciyarta tunane-tunane da sukan jefata cikin damuwa.

Ga bikin Intee ya matso kusa, sai gori take sha a gidan nan, wai ta zama guzuma, babu mashinshini a haka za ta dauwwama wanke-wanke da shara.
Chapter 46 · 0% Book details