← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 134

Sashe 25

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mafaka gidan ƙamshi, na da kyakywan albishir ga amare uwar gida, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

P11

Haka a ka kai ummi, mata suka gama surutansu, wasu daga cikin maƙwabta da suka san irin rayuwar da ummi take yi, suka din ga tsinewa iya, mussaman ganin ɗakin da aka kai budurwa, da tsohuwar katifa, ko zanin gado babu.

Aka din ga ƙananun maganganu, sai dai babu wanda ya isa ya iya tunkarar iyan, ya gaya mata hakan, saboda iya bala'inta da tashin hankali, haka kowa yayi maganganun sa ƙasa-ƙasa.

A hankali kowa ya watse aka bar ummi, Æ´an matasan yaran da aka bar ta da su, suka gaji da zama, ango bai shigo ba, suka watse suka bar ummi ko fitila babu.

Wani irin tsoro ya mamaye ta, da ta ji motsi kaÉ—an sai ta razana, shiru-shiru babu idiris babu dalilinsa.

Ji ta din ga yi a ranta, kamar ta tashi ta koma gida, dan wani irin tsoro take ji, kamar ace kyat ta zura da gudu, saboda duhun da ya mamaye ilahirin gidan.

Dare ya cigaba da yi, duhu ya sake mamaye ko ina da ko ina, ta yadda ko tafin hannunta ba ta iya gani, tun tana jin motsin mutane sama-sama, har gari ya koma yayi tsit, sai kukan ƙanan ƙwari. Cigaba da kuka ta yi cikin firgici, ta tashi a hankali ta leƙa tsakar gida, ta hango ƙofar gidan a buɗe, tsakar gidan kuma sai ta yi ta ganin abubuwa na yi mata gizo, saboda a tsorace take, kuma ga duhu.

Da sauri ta koma can ƙuryar ɗakin ta takure, bacci take ji sosai da sosai ga gajiyar aiki, ga ta biki, ga tashin hankali ga kuma dukan da ta ci jiya da daddare a wurin Iya.

Babu tsammani ta ji rugugin hadari, da walƙiyya ko ta ko ina, fashewa tayi da kuka, tana son tashi ta fita da gudu ta koma gida, amma tsoro ya hanata.
Tana nan zaune ruwa ya kece ya din ga zuba kamar da bakin ƙwarya, ta tashi da nufin ta rufe ƙofar ɗakin, amma ƙarfin zubar ruwan, da kuma tsawar da ake yi, ya sanya ta koma ta zauna tana cigaba da kuka.

Ruwa ya din ga feshi cikin É—akin, wani irin sanyi ya mamaye garin.

Ruwa ya shigo ɗakin sosai ya jiƙe, sai dai bai kai kan katifarta ba.

Kasancewar bacci ɓarawo ne, ya kwashe ummi a nan zaune ba tare da ta shirya hakan ba.
sai da gari ya waye ya fara haske, sannan ta tashi a razane.

Ruwan da aka yi duk ƙasa ta shanye, ta zama taɓo, wani kofi ta gani a tsakar gida, ya cika da ruwan da aka yi, tayi alwala da shi, ta koma ɗakin tayi sallar asuba.

Tana nan zaune cikin zullumi da fargaba, aka yi sallama, wasu daga cikin Æ´an biki ne suka zo, hakan ya sanya ta ji daÉ—i.

Suka din ga rafsa guÉ—a, ummi dai da ido kawai take bin su.

Suka kawo mata abun karyawa, ake tambayarta ina angon? Tayi shiru ba ta ce komai ba, dan kuwa ba ta san me za ta ce É—in ba.

Suka ƙara yi mata ƴan gyare-gyaren da zasu yi mata, suna ta hira suna yi mata nasiha, da azahar suka ce za su tafi.

Ummi ta É—au hijjabinta ta ce za ta bi su.

"Ki bi mu ina? Ai ko ƙofar gida ki ka fita babu iznin mijinki, Allah zai ƙona ki a wuta, ki koma ki zauna, shima yana ango amma safiyar fari ya fice, har azahar bai dawo ba?" Cewar wata dattijuwa.

Ƙanwar Iya ta ce "Bar mara mutunci, ai da alama ba son auren nan yake yi ba, haɗin Iya ne kawai, kodayeke ai ma ya furta, tun da hama ta yi masa Allah ya sanya alkhairi, ya ce ba amin ba, ba ya so"

"Too ikon Allah, ai dama idiris ba mutunci ya cika ba, har ta bani tausayi, sannu kin ji ummi, Allah ya baku zaman lafiya ya baki juriya" suka gama salallaminsu suka tafi.

Ta dawo tsakar gida, ta haɗa takalmanta ta zauna, ta zubawa hanyar ƙofar gida ido, in da Allah ya taimaketa, baƙin da suka zo, sun saka yara su je gida, sun ɗaukko bokiti, an cika mata shi da ruwa, da haka ta samu na alwala.

Da la'asar aka turo ƙanin idris ya kawo wa ummi, abinci ta karɓa ta ce masa dan Allah ya tayata zama kar ya tafi, tsoro take ji.

Cikin ikon Allah bai tafin ba, ya tayata zama, har suka ci abinci tare, sai magariba ya tafi ya bar ta ita ɗaya ƙwal kamar mayya.

Hashim ya rasa in da zai sanya ransa, damuwa ta din ga sassaƙar zuciyarsa, gashi tun da aka ɗaura aure, bai saka idiris a idonsa ba, yana son zuwa gidan ummi, amma yana tsoron yaje ya tarar da abun da ba shikenan ba, da zai ɗaga masa hankali.

Baban su Idris ya samu Iya yake tambayarta, ya za ayi da dangin mahaifiyar Ummi, yakamata a sanar musu.

Iya ta ce "Rabu da su, gayyar tsiya ko an gaya musu uwar mai za su tsinana, talakawan banza, ba su ajiye komai ba sai buzu da tawwada sai allo, ai a haka aka tsaface mini ɗa, aka shanye shi ba ya moruwa sai abun da take so, yanzu idan suka sani tsaf za su yi wata ƙulla-ƙullar, a bari sai komai ya lafa, an kwana biyu sai a aika musu da goro da alewa ace na aurar da jikata, shikenan"

Saminu ya ce "Amma Iya za su ga kamar ba a kyauta musu ba fa"

"Ita abubuwan da tayi mini kyautawar ta yi? Can su ƙarata yarinya ce dai na aurar da ita"

Saminu ya jinjina kai, amma dai ya san abun da aka yi ba a kyauta ba, ko ba komai suna da hakki a kan ummi, tun da Æ´ar su ce ta haifeta.

Ummi haka ta sake kwana a gidan nan, ita kaÉ—ai babu idris babu alamarsa, haka ta sake yin kwanan tsoro da tashin hankali.

Sai dai wayewar garin Allah, babu wanda ya tuna da ita balle ya aiko mata da abinci.

Babar idiris ta fara ƙorafin, tun da aka kai ummi, Idiris bai zo ya ko gaishe su ba, har maganar ta je kunnen iya, ita ma tayi maganar a ranta, amma kasancewar sai a ranar baƙi suka gama watsewa, abun ya dawo kanta.

Rai a ɓace ta aika Alhassan, ta ce ya je gidan ummi, ya ce Idris ya zo tana nemansa.

A hanyar ƙofar fita, ya tarar da ita a zaune, tana kallon masu wucewa.

"Ke ummi, kina amarya kina zama a hanyar ƙofar gida kina leƙe?"

Duk da ba shiri suke yi ba, ummi ta ce "Tsoro nake ji, nikaÉ—ai ce a gidan"

Ya ce "Taɓ, ina yaya idiris, Iya ta ce yaje tana nemansa"

Ummi ta ce "To ai bai taɓa zuwa gidan nan ba, ni tun da aka kawo ni ban ganshi ba"

Ya waro ido ya ce "Ke da gaske!? Ke kaÉ—ai ki ke kwana a gidan nan?"

Ta É—aga masa kai alamar eh.

Ya ce "Sannu da ƙoƙari, kuma ki ka zauna? Kodayeke idan ma ki ka ƙi zama kin san sauran, bari na je na gaya wa Iyan"

Hankalin iya ba ƙaramin tashi yayi ba, da jin cewar wai tun da aka kai ummi bai taɓa kwana a gida ba.

Ta É—au mayafi ta tafi gidan ummi, a nan tsakar gida suka tarar da ita a zaune.

"Ke ummi, ashe tun da aka kawo ki, Idiris bai kwana a gidan nan ba?"

Ummi ta É—aga mata kai alamar eh.

"Kuma dan ubanki ki ka ja baki ki ka yi shiru baki faÉ—a ba? Har sai da na aiko, ke da na nemeki na rasa haka na yi miki, ba yawon nemanki na tafi ba? Wato baki damu da shi ba ko?" Ummi dai ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Iya ta yi ta mata masifa, sannan ta fita, daga gidan, ta saka aka tafi kasuwa aka kirawo babansa, da sagir aka ce musu, ba a ga idiris ba.

Iya ba ta damu da tsawon kwanakin nan, ya ummi take ba, ta ci abinci ko ba ta ci ba, bata bi ta kan hakan ba.

Aka din ga yawon nemansa, wurin abokansa da sauransu, da ƙyar aka gano shi, can wurin wani abokinsa ya koma, a can yake kwana.

Iya ta same shi ta din ga zaginsa, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, mahaifinsu ma kamar zai kai masa duka, saboda takaici da ɓacin rai.

Hashim kallon su Iya yake yi, yana tausaya musu ranar da hakkin ummi zai kama su baki ɗayan su, babban abun da yake ƙara bashi mamaki, irin yadda ba wanda yake iya yi wa musu a kan duk wani son zuciyarta.

Ummi ba ta san me yake faruwa ba, sai ma tunanin Allah ya sa Idris yana lafiya, tun da an ce tun ranar É—aurin aure ba a sake ganinsa ba.

Da ƙyar tayi sallar la'asar, saboda yunwar da take ji, cikinta sai ƙugi yake yi, har wani jiri take ji idan ta tashi, ban da ruwa ba abun da ta sha, tana son fita nemawa kanta mafita, amma an ce idan ta fita ba da izinin Idris ba, Allah zai ƙonata, gashi kuma tana son komawa makaranta, amma ba ta ganshi ba balle ta tambaye shi.

Sallamar yaro ta ji, tayi sauri ta fito daga ɗakin, wani yaro ta gani da kwano, ya ce mata "Gashi in ji mamanmu" saboda ƙuruciya da yarinta, ummi ba ta tambayi daga ina ba, ta karɓa ta ce ta gode.
Chapter 25 · 0% Book details