Sashe 105
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwanciyar hankalin ummi ya tsayewa farida a rai, tare da jin cewar kausar ce yakamata ace a cikin wannan kwanciyar hankalin, inteesar dai ga ta a cikin daular, amma mijinta ba ya ɓanɓaruwa, gashi ya juya mata baya. Ashe tun kan aure ya kai ta aka yi mata allurar family planning, wai yafi son su gama cin amarci kan su tara yara, babu wanda ta gaya wa daga baya kuma abun ya bata matsala ciki yaƙi zama, wadda ya auro kuma ta samu ciki sai wulaƙanci take fuskanta iri-iri. Ga kausar ba makaranta ba mijin aure duk da ga kyau ga kwalliya.
Abdul kuma babu ƙwaƙƙwaran aikin yi.
Saura kwana uku tafiyar, Ummi da raihan suka je maiduguri ma, Mariya kamar ta haÉ—iye ummi, suma sun yi farinciki ganin ummi, raihan yayi musu alkhairi sosai da sosai.
Suke gaya mata har a lokacin bayan bikinta, dr. Yana zuwa ya kawo musu sha tara ta arziki, tare da duba lafiyar Mariya.
Hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa ummi ba, karamcin kawu yahaya ya sanya ba ta taɓa mantawa da shi a cikin Adduo'inta, kuma a duk lokacin da ta samu abun alkhairi take kai masa da iyalinsa.
Jin mami ta matsa a kan maganar auren raihan, ya sanya jikin ummi yin sanyi, a baya tana ganin babu wani abu idan raihan ya ce zai ƙara aure, amma a yanzu fargaba ta shige ta da tsoro.
Dan a gabanta mami ke kiransa ta jaddada masa maganar auren, ko ma safiyyan ta kira shi wai zata gaishe shi, tana iya kokarinta wajen kar ta nuna masa wani abu na ɓacin rai, dan tana ganin idan ta yi masa haka ba ta yi masa adalci ba. Ta ji gaba ɗaya tafiyar ma ta fita daga ranta ba ta so.
Sai dai suna barin ƙasar, ta ɗan samu nutsuwa, mussman da kullum tana tare da raihan tana shan soyayya da kulawa kala-kala a wurin matashin mijinta.
Sun samu zuwa wurare masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali, ƙarƙashin jagorancin ɗaya daga manyan manajojin su raihan, da suke kasuwanci tare. Shi yake kula da komai nasu kama daga masauki zuwa abincin su da sauran buƙatu.
Ummi ba ta taɓa tunanin ganinta a ko da airport ba, sai gashi ta keta hazo, ta bar ƙasa Nigeria.
Babban abun da ya bawa ummi mamaki, bai wuce yadda ba ta ga mutanen ƙasar na muzanta halittarta ba, sai ma bayan shirya musu wani cin abinci da managern yayi, da iyalansa da wasu daga abokan kasuwancin su, suke cewa ba su taɓa ganin baƙar fata mai kyan ummi ba.
Da aka fassara mata da turanci abun da suka ce, saboda galibi ba su iya turanci ba, mamaki abun ya bata, wai idonta mai kyau da fatarta, har ta fara tunanin ko ba'a suke yi mata, suka din ga layin hotuna da ummi.
A duk lokacin da suka fita shaƙatawa, sai mutane su yi ta kallonta, har wasu su nemi su ɗauki hoto da ita, suna yi musu tambayoyi mussaman idan ta yi shigar hausawa, duk da ta fi saka rigunan abaya a kan kayan hausawa.
Duk da ummi na ƙoƙarin kare mutuncin aurenta, da matan su kawai take gaisawa tayi hotuna, sai da kishin raihan ya kasa ɓuya.
Sun fita baki wani ruwa da daddare shan iska, take tambayar raihan "MD dan Allah mutanen nan da gaske suke, ko zagina suke yi da suka ce ina da kyau?"
Ya ja hancinta ya ce "Idan na faÉ—a ai ba kya yarda, you are beautiful baby"
Ta saka hannu ta shafi fuskarta ta ce "An ce fararen fata suna ƙyamar baƙaƙe, amma ni har ƴan uwana baƙaƙen ƙyamata suke yi"
Ya kwantar da muryarsa ya ce "Mutanen china suna da ƙarancin nuna wariyar launin fata, su kuma mutanenmu son zuciya ne kawai, da rashin bawa abun da muke da shi muhimmanci".
Ta sake jan numfashi ta ce "Ni fa bayan baba da mama, kai ne kawai ka ke cewa ina da kyau, sai noor gani nake duk Nigeria na fi kowa muni"
Ya ɓata fuska ya ce "Ban hanaki faɗar irin wannan maganar ba? Me ki ke nema a yanzu da Allah bai yi miki ba? Ubangijin da ya yi ki yana sonki, mama na sonki nima ina sonki to me ki ke nema kuma?"
Ummi ta girgiza kai ta ce "hmm MD kenan, idan aka ce ina da kyau wallahi sai in ji kamar zagina ake yi, saboda na fi sabawa da jin kalmar cin mutunci "
"Ni kuma wallahi a duniya, a yanzu dai ban sani ba ko a gaba, amma wallahi ba ki ga yadda ki ke yi mini kyau ba Salma, komai naki son shi nake, wallahi duk macen da na gani, sai in ga ba ta kai ki ba. Ina kaucewa auren Safiyya ne saboda a yanzu dai na ƙara aure ba zan iya adalci ba son da nake yi miki daban ne, a ƙasan zuciyata nake jin ki, bana son wani abu na rashin daɗi ya raɓe ki, ban san ya zan misalta miki ba ki gane ummi, kawai ni dai ki yadd ki saka a zuciyarki ina sonki, kuma wallahi ban taɓa ganin muninki ba ko sau ɗaya. Kawai ji nake duk matar da zan aura ba zan samu biyayya da kulawar da nake samu a wurinki ba, mutane kawai suna ganinmu ne, amma ba za su gane tarin baiwa da Allah ya yi miki kala-kala ba, su muninki suke gani, ni kuma abubuwan da nake gani game da ke ba zasu lissafu ba. Ina sonki kariun nisa'i"
Sanyin iskar wurin, da daɗin kalaman raihan, ya sanya wani irin shauƙi ya kama ummi, tare da jin ta a sama, kalaman na raihan suka sanya ta ji kamar a duniya babu wadda ta fita sa'ar miji. Abu kamar a mafarki ita da ake cewa ba zata auru ba, sai dai a taimaka a aureta saboda muninta, amma yau gashi Allah ya gwangwaje ta da miji na kere wa sa'a, kalaman na raihan ko ƙarya yake yi mata sun yi mata daɗi.
Ta rungume shi sosai ta ce "Allah ya barmu tare har aljanna Zaujul janna, kana cikin mutane masu muhimmancin da suka haska fitila a rayuwata mai cike da ƙalubale kala-kala, dan Allah kar ka daina sona, ko zaka yi aure a gaba ko ka so wata, dan Allah kar ka daina so na, ko da ka daina sona ka ɓoye mini dan Allah, kulawarka tayi tasiri a rayuwata idan na rasa soyayyarka da kulawarka komai nawa zai koma farko, kai kaɗai ne hope ɗina yanzu, an ce wataran ana gajiya da juna dan Allah kar ka gaji da ni" ta ƙarasa maganar kamar mai magiya.
Ya saka hannayensa biyu yana shafa bayanta, yana jin yadda take kuka.
"Soyayyar da aka gina da tubalin toka ita ke gushewa, tamu kuma da tubalin dutse muka gina ta, ni da ke har aljanna babyna" ya ƙarasa maganar yana ɗago fuskarta yana share mata hawaye.
Tausayin ummi ya cigaba da mamaye masa zuciya, tare da jin zai jure kowane ƙalubale ummi ta samu farinciki.
Kwanakin su ummi takwas a ƙasar, ɗaya daga cikin waɗanda suka ci abinci tare da su ummi, ta nemi iznin ummi a kan tana son ɗora videonsu da suka yi ita da ummi, a YouTube, babu tunanin komai ummi ta ce mata to, saboda yadda ta san da shigarta ta mutunci a jikinta a ka yi videon.
Sai dai kwana ɗaya take nunawa ummi adadin views ɗin da videon ya samu, ya tafi viral da yadda mutanen ƙasar har ma da wasu suke sharhi a kan ummi.
Communication da mutanen yana bawa ummi wahala, dan su ba su iya turanci ba, ita kuma ba ta jin yarensu.
Amma duk da haka mutane ne masu tambaya, wasu lokutan har live videos suke yi da ummi, suna yi mata tambayoyi a kan mutanen Afrika, a gaya mata tambayar da turanci, ta basu amsa da turanci a fassara musu.
Raihan sai dai ya kalle su yayi dariya, ya san suna takura ummi, dan ba son mutane take yi ba, gashi kuma kamar tsoronsu ma take ji.
Sai dai ya ƙyalesu ne, saboda wataƙila a dalilin haka ummi ta samu wani cigaba a rayuwarta, da zai tabattarwa da duniya musamman masu nuna cewa ita mummuna ce, ba za ta yi acheiving wasu abubuwa a rayuwa ba saboda kalarta.
Har tambayarta suke yi a kan ƙabilar hausawa, da Nigeria baki ɗaya, duk da akwai masu tambaya cike da izgili ga ƙasar sai dai cikin hikima da dabara ta aiki ummi take basu amsa.
Sai da ummi ta fara damuwa da yadda adadin masu zuwa ganinta da hotuna da ita ke ƙara yawa kamar wata halitta ta daban, ga kuma kyaututtuka da ake ba ta.
A daddafe suka yi wata ɗaya, fatarta ta ƙara kyau, duk da daga ita har raihan abinci ba kowane iri suke iya sakin jiki su ci ba.
Ummi ta tara kyaututtuka sosai, ranar da zasu tafi ƙawarta da suke video ta ba ta kyaututtuka, ɗan zaman da suka yi sun saba da ita, suka yi ta tambayarsu yaushe za su dawo, raihan ya ce musu sai wani lokacin.
A jirgi ya din ga yi wa ummi mitar daga zuwa ƙasar mutane ta zama cele, shi fa haushi yake ji yadda ake sakata a social media.
Cikin damuwa ta ce "Meyasa baka gaya mini ba ka so ba? Ka bari muke yi, ni bana son su ga kamar na yi musu wulaƙanci ne"
Yayi murmushi ya ce "Sweetheart, komai yana da sila, tsakani da Allah zuciyata kamar ta fashe, ana talla da matata, amma sai na tuna ke Æ´ar jarida ce tun ainihinki ma, kuma ban san alkhairin da zaki iya samu a sanadin hakan ba, ina fatan ko iya haka a ranki zaki ji cewa ke ta mussman ce, kalli dubban mutanen da ke bibiyar live É—in da ku ke yi, ba kuma wai dan kina wani abu na musamman ba, kalarki da irin halittarki da mutanenmu suke kushewa, su ita ta ja hankalinsu"
Tayi shiru ba ta ce komai ba, ta cigaba da wasa da yatsun raihan da ke hannunta.