Sashe 65
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ya za ayi na yi bacci, zaka yi mana sagegeduwa, ai bacci bai kama ni ba, dole na din ga bacci da ido É—aya. Uban me ka je ka cewa Alhaji?".
Kai tsaye raihan ya ce "Ce masa na yi ya taimaka ya saukeni daga muƙamin nan".
"Saboda ba ka da hankali ko? Allah ya ƙwaci abun ya baka, sai ka ce ba ka so saboda shashasha ne kai raihan?"
Bin mami kawai yake yi da kallo, ta haƙiƙance ta din ga yi masa faɗa, shi dai yayi shiru bai ce mata komai ba, babban abun da ya bashi mamaki, irin huɗubar tsiyar da ta din ga yi masa, har ta yi ta gama bai ce mata komai ba, ya tashi ya tafi, yana mamakin halin mami da tunanin yaushe zata sauya.
Ta kafa wa Hajiya ƙahon zuƙa, gashi dai hajiya ta tarar a gidan, amma tun tasowarsu mami ta kanainaye komai, gashi kishi take da hajiya kamar abokiyar gabarta, ta haɗe kai da yaranta mata duk sun saka Hajiya a gaba, dan ma duk an yi musu aure saura Nihal da ke karatu a ABU zariya, ba ta fiye zama a gidan ba, shikaɗai ne a ƴan ɗakinsu suke shiri da hajiya, dan shi har ga Allah bai ga aibun matar ba.
Ummi kuwa daga ita sai noor suka san da kayan nan, ummi ta ɓoye su a cikin kayanta, tuni ta yi wanka ta fara shafawa, sai dai fa kayan kwalliyar ne ba sa gabanta, ita turarukan da mayukan sun fi ɗaukar hankalinta.
Tayi ta kiran Raihan, daga baya tana ta shiga amma baya É—agawa, tayi wankanta ta shafa mayukanta da turare, tana sake kiran wayarsa farida ta shigo É—akin.
Gabanta ne ya ɗan faɗi, ummin na zaune a kan katifa, babu hijjabin nata na gado, ta saka skirt kawai da vest ga hijjabin a gefe, fatarta tana ta ƙyallin man da ta shafa, ga ƙamshi da ɗakin yake yi, ta saki gashin kanta ta sunkuyar da kai tana danna waya.
"Ke!" Ta daka mata tsawa, ummi ta É—ago da sauri, ta ja hijjabi ta saka.
"Dalla ki tashi ki wuce ki ɗora mana abincin dare" kallonta ummi take da mamaki, ɗazu taje tayi girkin ta koreta ta ce ba ta buƙata, yanzu kuma ta ce wai sai ta taso ta yi.
Da "To" ta amsa, ta tashi ta tafi kitchen.
Ga alamar an yi girki, amma duk an jibgeshi an ƙi ci, ta duba tukunya wata jallof aka yi ta shinkafa ta yi jagab kamar da shinkafar tuwo aka yi ta, ta kai bakinta ta ɗanɗana, da sauri ta fuzar an zabga uban gishiri da attaruhu, ga mai male-male a kai.
Hakan ba aikin kowa bane sai kausar, dan farida ta ce ummi ba zata sake shigar mata kitchen ba, ta ƙuduri aniyar ƙuntata mata, kausar ta yi girki ya ƙi ciyuwa.
A daren ta tuƙa tuwon semovita, ta sallami kowa sannan ta koma ɗaki.
Missed calls É—in raihan ta tarar, da message "Call me when you are available"
Ba ɓata lokaci ta kira shi, ya ɗaga da sallama, ta amsa masa sannan ta ce "Ka kyauta raihan".
"Da na yi me?"
"Ka fi kowa sanin me ka yi mini ai, sannan ka kashe wayarka, daga baya ka ƙi ɗaga wayata, mun yi da kai muje mu yi sayayya, in saya maka abu sai ka sai abun da ya fi ƙarfin kuɗina, kuma ka dawo mini da kuɗina har da ƙari, kafi ƙarfin abun hannuna ko?"
"A'a ba haka bane ba, dan Allah kar ki yi mini wata fassara daban".
"Haka ne mana, ni bani da abun da zan baka ko? To ka zo ka karɓi kuɗin nan and am serious"
Ya gyara kwanciyarsa ya ce "Ni fa a cikin damuwa nake, kaina har ciwo yake yi, zaki ƙara mini damuwa"
Sai kuma ta nutsu "Wace irin damuwa kuma?"
"Ba maganar waya bace ummi, zan zo in sameki"
Ummi ta ce "Amma dai komai lafiya ko? Kar ka sa hankalina ya tashi fa, ka fara gaya mini"
"A'a ba abun tashin hankali bane ba, ki kwantar da hankalinki gobe in sha Allah zan zo"
"To Allah ya kawo ka lafiya, ko menene ka fawwala wa Allah ka ji?".
"In sha Allah, sai da safe" suka yi sallama, ta gyara shimfiɗarta, ta kwanta tana jin ta kamar wata ta daban, ƙamshin da yake tashi a jikinta sai nishaɗi take yi.
***
"Anty Rakiya, ai in gaya miki da ƙyar na yi barci daren jiya, tun da Alhaji ya faɗi wannan sanarwar da ƙyar na yi barci saboda murna, shi ɗan naki da yake ba kan gado ya cika ba, ya je ya samu uban wai ba ya so"
Rakiya ta ce "Kin ga raihan da rigima, Allah ya kawo dama yayi fatali da ita, kar ki kuskura ki yarda, ai ke lalacewar Æ´aÆ´an can gaba ta kai ki Bilki".
Mami ta ce "Can gaba ma, kuma ƙoƙari zan yi duk mai yiwuwa in saka masa ido, dan tun a jiyan na kirawo shi na ƙare masa ta tas, yanzu abun da ya rage zan yi, dole in jajirce kar ruɗin kuɗi ya sanya shima ya fara biye-biye in yi biyu babu, shima ya lalace aure zan yi masa yaya, ai zai iya riƙewa"
Yaya rakiya ta ce "Ke bilki"
"Wallahi yaya rakiya, kar in je ya lalace mini in shiga uku, idan na yi masa aure, sai ma yafi mayar da hankali a kan kasuwancin uban, ya san yana da nauyi a kansa, duk da ba ma'abocin kula mata bane ba, amma kin san kuÉ—i, yadda ya samu wannan babban matsayin yakamata ace yana da cikar kamala ta aure kuma"
"Wannan gaskiya ne, to da mai zai hana ki haÉ—a shi da Safiyya, ayi Æ´ar gida kawai"
Mami ta ce "Wallahi kuwa, tuwona naina sai dai kin san shi, ba a iya masa, zan tuntuɓe shi da zancen idan har ya amince bani da matsala, amma dolensa yayi aure, hakan zai ƙara sanya ma'aikatan su girmama shi"
Suka cigaba da hira, Anty rakiya na ƙara ziga mami, da yadda za ta ɓullowa lamarin hajiya, ta kankane komai, da kuma muhimmancin aurar da raihan, mussman idan suka haɗa shi da Safiyya, dan ƙarafafa zumunci.
***
Ƙurii raihan ya yi wa ummi da ido, yadda take ta yi masa dariya.
"Ni ko? Ni zan gaya miki damuwata ki saka ni a gaba kina dariya, wasu abubuwan duk shawararki na bi, ƙarshe na rufta kuma kin zo kina dariya"
"To ai kai É—in ne, yadda duk ka tashi hankalinka dole ka bawa mutum dariya. Ni da na zata wani abun da ba a so ne, da farko dai congratulations mai girma MD" hararta yayi yana kallon wayarsa.
"Attention" tayi maganar tana kallon sa.
Ya juyo yana kallonta shi ma "Ka saurareni, mu ajiye wasa da komai a gefe, zan yi magana a matsayina na yayarka ne" ya haÉ—a hannyensa biyu ya yi tagumi ya zuba mata ido.
Ummi ta ce "Ba bakina zaka kalla ba, ka saurareni da kyau, a matsyinka na mutum mai muhimmanci da ba zan manta da shi ba, ina fatan Allah ya haÉ—a ni da kai a aljanna a majalisar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, kuma duk mai son ya tashi da annabi Sallallahu alaihi Wasallam sai ya kiyaye cin hakkin mutane.
Kai mutumin kirki ne raihan, kar ka bari kuɗi da shugabanci su yi wasa da imaninka, ka ji tsoron Allah, ka ji tsoron Allah ka riƙe gaskiya da amana, kar ka cuci kowa kar ka ƙasƙantar da kowa, yayyenka ƙannenka ma'aikatanka da duk wani na ƙarƙshinka, ka kula da su bisa amana, kar ka yi son zuciya, kuma kar ka saka a ranka lallai sai kowa ya soka, kawai ka yi dan Allah.
Abu na gaba, dole ka rage wannan jin kaɗe-kaɗen, ka mayar da hankali a kan azkar, da addu'a Ubangiji ya dafa maka yayi maka jagora, ya rabaka da dukkanin abun ƙi.
Sannan idan Allah ya sa ka tashi yin aure, a yanzu ko a gaba, ka samo mace ta gari, wadda abun da ka ke da shi, ba zai rufe mata ido, ta ja ka ga hallaka ba, danmu mata mutane ne masu kanmu da yawa, tsaf sai wata ta yi yinƙurin mallakarka da dukiyarka ta rabaka da kowa, kar ka auri mace dan kai kana sonta kawai, ka duba makomar zuriyarka da ahalinka, kai mutumin kirki ne zaka iya babban mutum, ka yawaita saurara tarihin salihan bayi da yadda suka gudanar da rayuwarsu mussaman ta fuskar shugabanci, hakan zai ƙara sanya maka tsoron Allah, Allah ya tayaka riƙo Muhammad Raihan"
Jikinsa gaba É—aya yayi sanyi, kalaman ummi maimakon su kwantar masa da hankali, tayar masa da hankali suka sake yi, tare da jin tamkar ta sake É—aure shi da jijiyoyin jikinsa.
"Ummi wallahi an scared, ba zan iya ba, jagoranci abu ne mai wahala"
"Haba madubina, kai kake ƙoƙarin koya mini jajircewa, kai kuma in ga gazawarka? A'a kar ka watsawa Alhaji ƙasa a ido, zaka iya ka ji"
Yayi shiru bai ce komai ba.
Ta ce "Ka ce to mana"
"Ba zaki gane a yanayin da nake ba ne".
Ummi ta ce "Eh ba zan gane ba kam, karɓi kuɗinka" tayi maganar tana ajiye masa envelope ɗin da ya saka mata kuɗi a kan tebur.
"ÆŠauke tun kan ki fusata ni, na yi miki rashin mutunci a gaban mutane"
Da mamaki ta kalleshi ta ce "Amma raihan idan ka yi mini haka ba ka kyauta mini ba, kuma ba zan ji daÉ—i ba" tayi maganar muryarta na rawa, dan tuno shi tayi ranar da suka je office É—in su, da ya burkice sai da ya bata tsoro.
Ya tashi tsaye ya ce "Bari na ƙarasa office, idan na samu kaina zan zo mu tafi gida, idan kuma aiki yayi mini yawa zamu yi waya" ko amsarta bai jira ba, yayi waje ya barta da kuɗin.
Sai da ya fita manager ya ce "Ummi, me aka yi wa mutumin ne na ga yana cika yana batsewa?"
Ummi ta ce "Rigima kawai yake ji"
"Ai nima na ga alama, shiyasa ban kula shi ba".