Sashe 6
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta kuwa hau sababi "Balarabe kana tsaye take neman yin kisan kai, shikenan an taɓa ƴar gwal sai tayi yinƙurin cire masa ido. Duk ɗawainiyar da ubansa yake yi a gidan nan? Wace irin ɗawainiya ce ba yayi da ku, wasu lokutan ba har ciyar da kai yake ba da iyalin naka, da baka ganin kowa da mutunci sai su, saboda zuciyarka ta riga ta mutu, baka da amfani ka kashe zuciyarka ka auri mai ƙashin tsiya, baka da komai sai sokonci da son mace, wadda maganarta ta fi tawa, tun da tana baka abun da bana baka, to kayi ƙoƙari ta kashe masa ɗa, wallahi duk matakin da ya ɗauka a kanku, babu ruwana ko da kuwa wurin hukuma zai kai ku"
Cikin takaici mariya ta ce "Wato iya saboda baban Alhassan yana da kuÉ—i shi ne É—a, da idan aka É—aukar masa mataki ba zaki hana ba, ummi ce da aka ketawa haddi ba Æ´a ba? Iya Allah fa" cikin hanzari balarabe ya girgiza mata kai. Cikin É—acin zuciya ta koma É—akinta.
"Ai da ka bar ta ta cigaba da gaya mini magana, ta tabbatar mini da bata da tarbiyya, kai ban da ina tsoron Allah da wallahi tuni na saka ka saketa, ko Allah ya sa ƙofar arzkin ka ta buɗe, idan ya so ka auro falla-fallan mata, mu samu ta haifa mana masu kyau, kadara irin arziki"
Bai cewa iya komai ba, ya shiga ɗaki, ya tarar mariya ta rungume ummi, tana aikin kuka. Zai yi magana ta ɗaga masa hannu, ta yi masa alamar ya rabu da ita, haka ya ƙyaleta ya fice.
Har ya tafi kasuwa tunani yake yi? Ko haya zai nema ya tashi ya bar gidan, ya san ba iya ce kaɗai ke da hakki a kan sa ba, iyalansa ma na da hakki a kan sa, kuma suna buƙatar walwala, amma iya ta takura su da yawa, kuma ya san ba zai iya biyan haya ba, kuma duniya zata zage shi, ya kasa zama da matarsa ya fifita iyalansa a kanta, haka yayi ta tunani, ba tare da samun mafita ba.
Mariya ma wuni tayi tunani da zancen zuci, ita kanta ta san bata isa ta tafi gida ba, ta ce tayi yaji saboda takurar uwar miji ba, ba babanta ba yayyenta maza kawai sun ishe ta, babu mai goya mata baya, dan ko hirar take musu, idan ta je ganin gida, sai ace uwa ce a wurinta idan da kara da tarbiyya.
Gidansu irin iyayen nan ne masu kashe Æ´aÆ´ansu su raya na wani a gidan aure, saboda dattaku dan gidansu gidan malamai ne.
Kuma ko kusa ba zata iya gaya musu cewar an yi wa ummi fyaÉ—e ba, saboda ita kanta da take ta hayagagar rashin bi wa ummi hakkinta, tana yi ne saboda abun yana damunta, mussaman nuna wa da ake yi Æ´ar kamar ba ta da amfani, saboda babanta ba shi da kuÉ—i.
"In sha Allah ummi sai ahalin nan sun kwanta a kafaÉ—arki, Allah ya nesanta ki da talauci, ya baki ikon cin jarrabawar nan da ni da ke baki É—aya. Allah shi ya san dalilin da ya sanya yayi ki a haka, kuma ya jarrabeki Allah ya baki mai kula da ke, ko bana raye" haka ta wuni cikin kuka da damuwa.
***"
Rayuwa ta cigaba da tafiya, umma ta cika shekaru shida a duniya, sai dai bata sauya zani ba, domin kuwa gorin yau daban na gobe daban, haka iya ke yi, a kan cewa balarabe ba ya iya tsinana komai, a gidan komai shi ne koma baya.
Haka zalika balarabe, ya fara tunanin miƙewa ya nemi kuɗi, ko dan samawa iyalin sa farinciki da kwanciyar hankali, mussaman ƴar ƙaramar yarinyar nan, da aka mayar da ita tamkar wata halitta daban.
Yau suna kwance da daddare tare da mariya ya ce "Maman Ummi kin san wani abu?"
Ta ce "A'a"
"Ina ga Æ´an kuÉ—aÉ—ena da nake tarawa, zan je birni in ga abun da zan iya yi, ko Allah ya sa na samo arziki"
Mariya ta kalle shi ta ce "Baban ummi baka yadda da yadda Allah ya ajiye mu ba? Na san babu daɗi abun da iya take yi maka, amma dai ka yi haƙuri da barin garin nan, ka tafi yawon neman kuɗi, raba bawa da arziki sai mutuwa, dan Allah kayi haƙuri"
Ya gyara kwanciyarsa ya ce "Maman ummi, tun da abun nan ya faru da ummi, ji nake tamkar ina kan wuta, gidan galibi duk maza ne tana cikin haɗari, sannan ki duba ki ga yadda ake yi mata a gidan nan, ɗazu fa suna tafe da yarinyar nan da take ɗaukarta ta tafi da ita islamiyya, yara suna tsokanarta baƙar tukunya mai ƙyalli, ba ki ji zuciyata ba, wallahi yanzu haka bani da burin da ya wuce tashi na bar gidan nan.
Da nayi tunanin ko kano zan je wurin yaya hashimu idan da wata hanya da zai É—ora ni a kan kasuwanci, to kuma bana son na je na É—ora masa É—awainiya, kuma kin ga shi É—an boko ne, iya ta ce sai na bi su Rabiu kudu neman kuÉ—i, bana son yin nesa da ku, amma na fuskanci idan na cigaba da zama a haka, wahala zamu cigaba da sha".
Mariya ta nisa ta ce "To, ni dai dan ta ni, wallahi baban ummi zan cigaba da haƙuri, komai lokaci ne, amma duk abun da ya shafi umarnin iya, babu ruwana a ciki, Allah ya taimaka ya bayar da sa'a, ummi kam za ta yi gwagwarmaya wadda sai dai mu bata gudunmawa ba zamu iya tare mata ba.
"In sha Allah komai zai zo da sauƙi, kuma zai wuce umminmu zata rayu cikin farinciki"
"Allah ya sa"
Ya amsa mata da "Amin"
Abu kamar wasa, Iya ta din ga yi wa balarabe kwarmato, a kan lallai ta yi magana da Rabi'u maƙwabcin su, lallai ya nemo kuɗi, ya bi shi lagos, ya ɗora shi a kan hanyar neman arziki.
Bashir ba shi da kuÉ—in da aka ce ya tanada, dan kuwa rabi'u cewa yayi ya tanadi dubu É—ari, harkar fawa yake a lagos, ya je ya koya masa.
Ya ce wa iya ba shi da halin kuɗin nan ta ce "Ai dama ba zaka yi su ba, Allazi babu wanda ya karɓo jakadancin talauci zuwa duniya, ka je ka tambayi ilyasu, ko sagir, ga saminu, ko Yahaya, tun da su masu zuciyar nema ne, kuma ba a rasa nono a riga, su baka aro.
Bashir baya son dalilin da zai sanya ya keta billensa ya nemi alfarmar Æ´an uwansa, saboda yadda ba sa yi da shi.
Amma bisa ga umarnin iya, ya tambayi sagir aron kuɗi, amma ya kada baki ya ce "In ara maka kuɗi, ka biyani da me? Gaskiya ba zan iya ba, kuɗin nan masu wahalar samuwa, na baka in yi sadakar dole da ba niyya, kayi haƙuri kawai". Ya ji ciwon abun da yayi masa, amma ya dake ya gayawa maman ummi.
Ita kanta mariya abun yayi mata ciwo, abun da iya take musu ya sanya ta tsane ta, duk da ita ta haifi mijinta, tattara samirun ta, har da zobenta da aka saya mata lokacin aure ta sayar, sai ganinta yayi da kuɗi, dan ita kanta wulaƙancin da ake yi masa yana bata haushi.
Ya din ga yi mata faÉ—a a kan sayar da kayanta da tayi.
Ta ce "Idan har tafiyarka zai sanya iya farinciki, a daina wulaƙanta mu, ka tafi kawai Allah ya tsare"
Ya riƙe hannunta ya ce "Na gode mariya, Ubangiji Allah ya saka miki da alkahirin sa, ya ƙara miki haƙuri, kada Allah ya sa na ci amanarki, ko a yanzu ko a gaba, Ubangiji Allah ya kula mini da ku" haka ya din ga zuba mata addu'a kamar ta yaye masa gaba ɗaya matsalolin sa.
Saura kwana É—aya ya tafi, da ya shiga ya fita, sai yayi musu addu'a, ya sanya musu albarka da ita ummi.
Da daddare mariya ta shirya masa kayansa a wata jaka, tana ta yi masa addu'a. Ya zura mata ido yana kallon ta.
"Wai wannan kallon fa?"
"Da za ace in nuna matar aljanna a duniya, zan nuna maman ummi"
Tayi murmushi ta ce "Zaka fara ko?"
"Allah ba wasa nake ba amaryata" ta kwashe da dariya ta ce "Ko ba amarya ba, da wannan Æ´ar tamu nake amaryar, in zo in fara tara kayan É—akin auren ummi, wai wa ya ganni maman amarya ranar auren ummi ba zama".
Yayi dariya ya ce "Kema É—in yaushe aka yi naki auren ki ke hango auren ummina, in sha Allah sai ta yi karatu mai zurfi, Allah ya sa kan na tafi É—in nan akwai rabo a cikin nan, ummi ta samu É—an uwa"
"Amin ya Allah, ni kaina ina son jariri wallahi"
"To Allah ya bamu mai amfani, ya bani kuÉ—i na halal na wadata ku, mu rayu cikin farinciki"
"Amin, amma yanzun ma Alhamdilillah, ai kuÉ—i ba su ne farinciki ba" sosai suka din ga hira, tana ce masa ban da kallon matan yarabawa idan ya tafi lagos, ya din ga yi mata dariya.
Har ta yi barci, amma shi ya kasa bacci, ya tashi daga kan gadon, ya koma shimfiÉ—ar ummi, da ta yi nisa a baccinta sosai.
Ya kunna fitila yana kallonta, sam bai ga munin Æ´ar sa ba da mutane suke faÉ—a suna zuzutawa.
Ya din ga shafa gashin ummi, yana kallonta.
Mariya ta yi juyi ta hango shi, ta ce "Baban ummi, ko saka maka ita zan yi a jakar ka ku tafi, wannan ƙauna haka?"
Yayi murmushi ya ce "Ko yara nawa zan haifa ummi ta daban ce a zuciyata, ina ƙaunar yarinyar nan"
Mariya ta ce "To kar dai ummi ta mamaye ko ina a zuciyar, a rage mini wuri"
Yayi murmushi yana cigaba da kallonta.
Juyi ummi ta yi taga hasken fitila, ɗan razana ta yi, saboda haryanzu ba ta manta yadda aka yi mata fyaɗe ba, dan daren da aka yi mata fyaɗe ta tuna, da ƙarfe ta ce "Baba"
Ya ce "Na'am ummina"
"Kai ne" tayi maganar tana shafa fuskarsa.
"Eh Ummina"
Ta ce "To" ta cigaba da lumshe ido zata koma bacci.